47 Tsakaninsu

2.8K 339 54
                                    

A cikin wannan halin da suke sai ga Indo ma ta mike zaune. Sai rarraba ido take tana kallon sarautar Allah. Ba ta san abin da yake faruwa ba, sai dai ta ga yan mata biyu rungume da junansu.

Rabonta da Gimbiya Saadiyya tun tana 'yar watanni uku. Ba za ta iya cewa ga ta ba, hasali ma su duka biyun ba ta san ko su waye ba.

Tana daga idonta daga can gefe ta hangi Kursiyya sai mazurai take yi. Ga hannunta ta ko'ina jini ke fita, duk ta ciccije kanta. Ga kuma Zabba'u da idanuwa suka gama kumburewa dan kuka.

Cikin sanyin murya ta ce,

"Fulani Kursiyya..."

Tana kokarin mikewa ta isa gare ta. Da sauri mai martaba ya ci gabanta. Ya ce,

"Wannan muguwar matar sam ba ta cancanci wata maganar arziki ta hada ku ba. Abu mafi kyautuwa ma sai dai idan Allah ya isa za ki yi mata, bisa ga zaluntarki da ta yi ke da diyarki."

"Ban fahimta ba." Indo ta fada kasa-kasa tana kallon mai martaba.

"Na gaza gane abin da yake faruwa.  Ni dai a sani na barci na kwanta a dakina dazu, ga shi kuma yanzu na farka na gan ni a dakin da ban san ko na waye ba. An canza shi zuwa ginin zamani tamkar ba a masarautar Bilbah din da na sani ba. Don Allah ku fitar da ni daga duhu."

Mai martaba ya ce,

"Ba barci kika yi ba Indo. Wannan makirar matar ce ta sa aka tsaface ki, yau kimanim shekaru talatin da daya ke nan, kina a tsaye kikam ke ba mutum ba ke ba gawa ba."

Indo ta zabura da karfi har tana neman faduwa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mai martaba da gaske kake ko da wasa?"

"Ba fa komai kika ji ba Indo, kadan ke nan daga sharrin Kursiyya da aminiyarta Zabba'u."

Duk sai jikin Indo ya yi lakwas, ta matsa inda Kursiyya take, cikin kuka ta ce,

"Me na miki Kursiyya? Me na yi miki da na cancanci wannan zaluncin daga gare ki? Me na tsare miki a rayuwa?"

Cikin halin ko'inkula Kursiyya ta ce,

"Babu fa abin da kika yi mini, kawai tsanarki na yi. Na ji bakin ciki ne da kika samu juna biyu, bayan jimawa da aurenku ba ki samu ciki ba. Na kuma tabbatar cewa abin da za ki haifa sosai mai martaba zai so shi. Don haka na je na asirce abin da kika haifa, ta zo da bakin jini tun tana jinjirarta. Ke kuma aka mayar da ke mutum mutumi.

Kar fa ki zaci kin min wani abu ne. Kawai dai kiyayya ce. Kuma har yanzu na tsane ki. Na tsane ki Indo ke da 'yarki."

In banda sunan Allah babu abin da Indo ke fadi. Su mai martaba kuwa tsananin mamakin Kursiyya ne ya cika su.

"To ina 'yata take?"

Ta fada bayan ta juyo ta kalli mai martaba. Da hannu ya gwada mata inda Saadiyya da Hafsa suke. Cikin murmushi ya ce "Canki 'yarki a cikinsu."

Ta matso kusa da su. Hannun Hafsa ta fara rikewa, ta ji shi da dumi sai dai ba irin sosai din nan ba. Ta saki ta kama na Halimatus-Saadiyya, a nan ta ji wani irin dumi mai matukar dadi, ta shiga wani irin yanayi da ta nemi duk wata damuwa ta Kursiyya ta rasa ta. Ta jawo ta a jikinta ta rungume, suna jin bugun zukatan junansu.

GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?)Where stories live. Discover now