maleek 16

725 51 0
                                    

 
  16

"Saukowa yakeyi ahankali daga mata kalar jirgin sama fuskarsa dauke da kyayyawan murmushi Wanda ya karama kyayyawar fuskarsa kyau, Idan ka ganshi bazaka taba cewa muhassin din da kasani bane yakara haske fatarnan sai shekin Hutu takeyi gashi yayi yar kiba da ka ganshi kasan ainihin balaraben Egypt ne,

(Nikam cewa nayi to shida maleek wa ma yafi Kyau ne Amma sai natuna Abinda addinina yace ahankali na furta _FATA BARAKALLAHU AHSANUL KHALIKIN_)

Janye yake da Dan Karamin akwatinsa yanufi Inda ake musu checking bayan an kammala ne ya dauki drop direct gida ya isa, wanka yayi ya shirya cikin kananan kaya wayarsa ya fidda wadda tin a mota take ringing, sundade suna fira da samha kafin at last sukayi sallama.

Bayan rana tayi sanyi yashirya Don zuwa ganin amininsa, maleek na zaune a daki kawai yajiyo muryar abokinsa, cikin tsananin farin ciki yabuga tsalle yana rungumeshi sosai cike da farinciki, bro wannan shine bazata yaushe a gari, kaganka kuwa kamar wani bature u have totally change kodai surgery kajene, dukansa muhassin yayi a kafada yana zolayar ta isa hakanan to yanzu ya ake ciki, Kai zantambaya kodai kasamo budurwane cos I can smell somtin fishy, dariya suka fasheda cikin murna da kuma kewar zuna, fira sosai sukayi wadda suka fi two months basuyiba.

Hajiya ce tin daga waje take rangada uwar guda cikin farin ciki, laila ce tafito tana ya mutsa fuska haba mama bacci fa nake kika tashi ni, 

Ke sokuwa jibi nan tana ware mata kudin a hannunta yau akwai shagali, tsaki taja tace inakuma kika samo wanan ko alhaji bawa yabaki,  ke kwal ubanki uban alhaji, hajiya tabani na mata wani aiki Amma gaskiya bazanyiba cinye kudin zanyi kuma ahaka zan dinga karbar kudi ahannunta ehe,

wallahi mama kiji tsoron Allah de, ke ai tsoron nashi kikeji shiyasa kike biye biyen maza koh, tafada tana maka mata harara,

Keni duk bawannan ba, kinga sonike ki kama danta Indan da yiyuwa ma ki aure sa inaga gun boka ayashe zanje yamin aiki, "tir Allah y tsare a'i da rogo wallahi ki ma bar maganar Dan bazai ma yiyuba wannan mai mugun halin", takarashe maganar tana turo baki

Amma ban taba sanin bakida hankali ba sai yau shegiya kawai kesan kudinda sukedasu ne Ina ruwanki da halinsa, fadar hajiya a harzuke

"koma duniyar garesu ai muma munadasu Banda ma kinje Kingama sallama ma boko dukiyar mu sbda wa enna yan iskan alhazan naki"

"Kika kuma furta wani abu sai na fasa miki baki shegiya fitsararriya  kashen tsiya, yar bakinciki, kin gwammace ki cigaba da bin kwararo da dakin samari ahaka zaki Kare"

"Bakomai ai ke kika koyamin"

Sanda tadauka tabita dashi tashige daki tana sa makulli.

MEENAL ce Zane tana rero karatun kurani cikin murya mai dadin sauraro saida ta kammala tashafa adduoin ta Sanna tamike tafita inda iyayenta suke zaune

Meenal mami takita ahanki kinga kicire yaronnan aranki kinga akanshi jiya akazo aka ma mahaifin ki cin mutunci dakuma wai Amana gargadi inji mahaifiyarsa wai danta ba saar yarmu bane, wai inta sake ganin danta a gunki komai zai iya faruwa, kinsanta batada mutunci komai zata iya aikawa Dan ko dan darajarmu dakuma Kare mana mutunci ki kyaleshi kinji ko,

Gabantane yafadi Don tasan rabata da maleek babban kalu balene a rayuwarta, cikin dauriya tace "mamy da abba kuyi hakuri da Abinda aka muku insha Allah baze sake faruwa ba" bakomai yar albarka kide kiyaye toh saida safe tamusu sallama tashige daki

Kuka take sosai sbda kome zaayi bataso a wulakanta mata iyaye bata ji dadin abinba sosai, tana gani maleek nakiranta tashareshi at last tamasa text wai kanta na ciwo

Tinda taje skul batada kuzari sosai taga muhassin, amma ga mamakin sa bata nuna farincikin ta sosai ba, saidai kawai suka gaisa tawuce, kallo yabita dashi yana meke faruwa, jikinsa ne yayi sanyi yace kodai tayi fushine Don baka mukeba

Guri tasamu ta rakube tayi nisa tuna ni taji andafata Murmushin yake tasaki ganin meena ce, I hope all its well lpia frnd,

"Lpia Lau meenah am not just in d mood"

"I can't believe dat, u wasn't like dis before y d sudden change , nice ko maleek ne?

Bakowa fa tana daga kafada

"Oya muje musha ice cream ban son Ina ganin mutum in dis mood tarashe tana murmushi"

Binta tayi suka isa Inda ake saida wa siyama musu tayi suka zauna suna sha meenah na mata fira tana kyalkyatar dariya, har tamanta da Abinda ke damunta

Maleek  yahango su daga nesa sun balain burgeshi, jiyawa kawai yayi yabar gun karya bata musu mood.

Gurin after 5 maleek yamata text yace su hadu a wani eatery by 8pm don akwai important bayanin  dazemata kuma gashi mom tasa masa kyakkyawan tsaro, so baze iya zuwa ba,

Bayan tagama  magrib tana zaune har akayi isha sannan tayi dinner takoma daki tana karanta wani book

Shikuwa tin quarter to 8 yaisa gun yana Sanye cikin rigar sanyi Don garin da isa sosai, yana zaune a varender yaga ta Inda zata Bullo, ganin shiru har after 8 yasa yamata miss calls har ukku bata dauka ba

Saida tagama karatunta  sannan tamike tahaye gado da zumar bacci, wayar ta janyo  Don ganin time, miss calss tagani har shida na maleek daya tin 8 20 wasu kuma har to 9

Mikewa tayi tace innnalillahi nashiga ukku wallahi namanta Sharp maleek yayi zamu hadu, hijab tasaka tafito tace mamy zanje gidan su nihat zan mata karatu gobe zasuyi exams tin dazu tamin magana kuma wallahi namanta

Dawannan daren haka,

Eh wallahi tin dazu tamin mgna wallahi mantawa nayi tafada kanta a kasa,

To adawo lpia karki Dade de kinga dare tafarayi, to mAmy

Zaune yake iskar hadari tafara kadawa aka fara yayyafi gashi bezo damota ba muhassin ya rage masa hanya

Saida tadan taka sannan tasamu abin hawa, suna fara tafiya aka balle da ruwa kamar da bakin kwarya

Yana nan zaune ga masu shagon sun rufe gari yafara duhu kuma ga ba ko abinhawa me wucewa

Tana sauka tahango shi rakube ruwa yamasa duka dukyajike sai rawar sanyi yake abinka da Dan Hutu basabo

Innalillahi maleek tinyaushi kake nan meyasa ka tsaya ruwa yama duka Dan allah kayi hakuri, jin shiru yasa ta girgizasa cikin tashin hankali tana meyasameka

Meenal sanyi ze kasheni Bana son sanyi ki taimakeni, rudewa tayi taciro hijab dinta tayafa masa Amma still rawar sanyi yake,

(Niko nace waya isa maleek yajira shi ai saidai shi ajira Shi Amma gashi ruwa yamasa duka sbda manal lalle so masifane)

Anfi 30 mins Ana ruwa kuma duk kansu yakare itada maleek, itama sanyi take ji sosai, banyan ruwan ya tsagaita ne tajawo shi zuwa kan cinyarta jikin taji kamar wuta, nabani maleek zazzabi to ni yazanyi rasa mafita tayi, dubara ce tafado mata ta kira meenah

Meenah na kwance to 10 tafara bacci taji wayar ta na ringing tsaki Taja cikin bacci ta dauka, jin abinda meenal kecewa yasa tace what meyasame ki ne, plss kawai kizo yanzu I need ur help,plss help meenah, to meyasame tane i have to go a frnd indeed is a frnd inneed hijab kawai tazura taja motarta a guje

Adede Inda tamata kwatance ta nan tafaka, haska su tayi da fitilar mota taga meenal zaune tana kuka ga maleek kwance a kafarta kamar ba rai.......

MRS AVBDOOL CE..........

"MALEEK"Where stories live. Discover now