maleek 24

679 53 1
                                    


   24

"Maleek tinda yashiga bedroom dinsa wanda yaci uban nasa nacan gidan kyau dakomai, ya rarumi towel yawuce bathroom saida yacika Jacuzzi da ruwan dumi yazuba turaren wanka da komai sannan yashige hankalinsa kwance ya dade kafin yafito yasaka farar shirt mai gajeran hannu da three quarter ya dau drink yawuce garden, zama yayi iska na kada masa gashi kansa yana zukar drinks dinsa wayarsa ya dauko ya dannan kiran meenal kana gani kasan hankalinsa kwance yake.

Muhassin tinda ya isa gidan nan gaban sa ke faduwa sbda harga Allah tsoronta yake ji baka Danba sbda danta ma bata raga mishiba.

Tattaro sauran courage dinsa yayi yashiga gidan, sallama yayi a palon tana zaune tana latsa waya, amsawa tayi batare da ta kalle sa ba, baku ma tadena abinda takeyi ba, sai bayan kamar 5mins tayi breaking silence din strictly fuskarta a daure babu alamun wasa tace

Ni kuke nema ku mayar abokiyar wasan kuko?

Dagowa yayi yana kallonta irin bai fahimci magarna taba dinnan

Tace were ix ur frnd?

Dan sanyi yaje aransa ganin batasan komai ba, yace mom Allah I don't know what u re even talking about, meyasami maleek din Ina yaje,

Wani mugun kallo tawatsa masa tace good, karka damu very soon I will caught u people red handed!!

Mom kiyi hakuri insha Allah zan nemo maleek duk inda yake,but nakira wayarsa ma a kashe take,

Rufemin baki munafikin banza, I can never believe ur words plss u can leave tana nuna masa hanyar da hannu but kasani inde har da hadin bakinka kasani definitely u are in hot soup!

Mikewa yayi jikinsa a sanyaye ya wuce.

Meena tin randa abin yafaru bata sake sakewaba duk batajin Dadi Dan kofitowa batayi ma, gashi biki nata matsowa.

Mom duk dubararta ta since Amma ta kudiri ko dan abinda maleek yayi saita nuna masa itace ta haife shi kuma tanada karfin iko akanshi.

MALEEK ne zaune bakin swimming pool da gajeran wando kafarsa nacikin ruwan yana wasa dashi, yana waya da masoyiyarsa

My love yaushe zakizo gidana ne I missed u fa inason ganinki sosai cewar maleek

Hmm my dear kayi hakuri bazan iya zuwa ba, mace me mutunci bata bin saurayi har gidansa ai, sede kafadi wani gun inyaso saimu hadu.

Ok to hakan yayi zuwa gobe saikizo muhadu a eatery ko,

To bade gobe ba don inada exams gobe gaskiya sede zuwa jibi

To bakomai Allah y kaimu lpia,

Yana gama wayar ya Mike yashige cikin bedroom king size bed din shi ya haye tareda Jan blanket, dama aikinsa kenan daga cin abinci sai bacci hankalinsa kwance, kana ganinsa sai ga haka a tattare dashi Don wani mugun kyau da ya kara.

Muhassin yashiga damuwa gameda Abinda mom tafada mishi, kuma yasan tazuba tsaro sosai  intagane sufato, akwai matsala sosai yasani.

Ranar dayakama satin maleek daya rabonsa da gida kuma saura sati daya bikin su da meena ranar zasu hadu da meenal

Maleek yagama shirinsa a ranarda zasu hadu da meenal, yayi kyau sosai, keys dinsa yadauka yawuce eatery dinda zasu hadu, text yamata na address din gurun.

Ba bata lokaci tashiga tsab cikin gown din tamfa tayafa mayafinta,  light makeup tayi fuskarta tayi kyau sosai tafito zuwa eatery din.

Tana isa ta tarada da maleek har ya iso, abinci sukayi ordering sukaci suka koshi, daga nan ya kaita park suka sha wasanni da soyayya sosai kamar babu Abinda ke damunsu can da yamma suka wuce mall don yimata shopping.

Mom ce takira meenah tace baby kidena damuwa kinji ko don't mind maleek, maleek naki ne kinji ko kuma yanasonki next week zaa daura muku aure kinji.

To mom haka zaayi auren baya sona, kodai yanada wacce yakeso ne

HABA baby babu wata wacce yakeso bayan ke, ki kwantarda hankalin kinji ko, Don kartasake mgna tace tashi muje kirakani mall zanyi shopping daga nan kema kiyi taki siyayyar

Mikewa tayi tashirya cikin jeans da shirt mai Dan tasawo haka tayafa gyale suka fito.

Dede zasu shiga mall din meena tahango wata kamar meenal, Amma saita share, tace kila de me kama da ita ce.

Mom kuwa idonta ne yasauka akan maleek yana kokarin shiga mota, wani murmushi tayi Wanda batasan sanda ya fito ba.

Maleek bayan sungama siyayya yaja motarsa zaifara sauke meenal gida daga nan yawuce nasa gidan.

Mom tace ma driver follow dis car, kallonta ya tsaya yi tace be fast karta bace maka, juya kan motar yayi daga shiga mall din yabi bayan su maleek.

Meena tace mom muda zamuje shopping y are we following them, keep watching shine abinda mom tace mata.

Duk Inda sukayi binsu su drivern mom keyi, saida sukayi nisa maleek ya Kula kamar Ana binsu abaya, saurin dauke hanya yashiga wata corner, binsu drivern mom yayi aguje shima, hankali tashe maleek ke tsula ubangudu, saida akazo wani lonely road Inda ba motoci duk bishiyoyine a gun mom tace sha gaban su da sauri, drivern da sauri yayi overtaking dinsu ya tsaida motar gaban su suna facing juna.

Cak meleek ya tsaida motar hankalinsa tashe don yasan yau kashinsa ya bushe musamman da yaga mom a motar.

Meenal ce ta bude motar tafito , meena da tacika tayi bam ta balle murfin motar tafito, isowa gaban meenal tayi batace mata komai ba tadauketa da Mari cikin tsananin fushi,

kankance ido tayi ta nunata da yatsa tace meenal kin cuceni, ashe ke munafuka ce bansani ba nayi Dana sanin yarda dake, babu abinda zance miki saidai nace Allah y isa tsakanina da ke.

Kwallane kawai ke zuba a idon meenal don tasan babu abinda zata ce ma meena kuma tasan ranar irin ta yau na nan zuwa dama

Itama meena kuka take sosai ta koma mota ta kifa kanta a kafarta tana kusan bakin ciki

Maleek ne  hankalinsa tashe yama rasa Ina zaisa kanshi mom ce ta karaso kusa da shi ta sauke masa tagwayen Mari masu azabar zafi, cema driver tayi saka shi a mota, kaikuma ta nuna guard din ta tace zomin da motarcan........





Mrs abvdool ce.....

Comment and vote.

"MALEEK"Where stories live. Discover now