BABI NA BIYU

714 18 0
                                        

Mimi da bata karasa shiga kichin ba dariya abin ya ba ta,ganin ba su ma lura da ba ta ida shiga kichin din ba suke soye war su.

Tana mai jin dadin ganin a kodayaushe yadda dadyn ke matukar  koƙari wajen kula da su tare da nuna tsantsar soyayyar sa ga momyn ta ko a ina ne.

Kichin din ta shige bayan ta dauki ledar kayan marmarin da dady ya taho da su(fruits) don shi ma'abocin shan su ne sosai musamman ma kankana(water melon) saboda yana kara lafia sosai a jikin dan Adam.

Wadansu hadaddun kuloli guda uku na abinci ta dauko,ko da ta dawo falon har su Momyn sun haura sama ta shiga jera su a kan teburin cin abinci(dining table)domin ta sa a ranta daga yanxu in dai har tana gida,ta hutar da momyn ta yin girki,ita zata rin ka yin abincin.

Bayan ta dawo kichin ne, ta hango Iya mai taya su 'yan aikace2 ta shigo,cikin girmamawa a matsayin ta na wanda ta girme mata ne sa ba kusa basuka shiga gaisawa a mutunce.

"Ina wuni Iya,ashe kin shigo?"

"lafiya lau Maman Alhaji dama haka take kiran ta ai ban ma wani dade da shigowa ba"Iya ta bata amsa

Cikin ranta tana kara yaba halayyar Mimin wacce ke bata girma a ko yaushe duk da tana a matsayin ta na mai musu aiki

Shiya sa take ganin girman ahalin gidan domin masu kudi ne da suka san daraja da mutumcin dan adam wadanda basu dau duniya da zafi ba,ba kaman wani masu hannun da shunin ba da suke ganin talaka ba a bakin komai ba fa ce makaskanci kuma marar galihu.

Bayan sun gama gaisawa,sai kowa ya kama aikin da ya shigo da shi,Smoothie na water melon ta shiga hadawa dady domin yafi son sa haka akan a yayyakan masa.

Kai tsaye kankanan ta dauko ta shiga yankawa,kafin ta wanke shi a tsaftace sannan ta ciccire 'ya 'yan da ke ciki,bayan ta gama ne ta dauke injin markade(blender)ta yayyanka su kanana ta saka a ciki,sauran su kankanan,lemo,ayaba da abarba daya rage sai ta yayyanka ta sa a plates,sauran ta maida cikin leda saboda lalacewa ta sa fridge,markade kakanan tayi,kafin ta juyo a glass jug mai kyau da daukar ido ta fasa kankara a ciki don yayi sanyi,sannan ta kara maida shi fridge.

Bayan ta kammala sai ta fara gyaran wajen data bata duk da Iya tayi tayi da ita akan ta barshi zata yi amma sam ta ƙi,tunda ita ta ɓata wurin ,ita ya kamata ta gyara.

Bayan ta gama da kitchen,falo ta dawo ta kara gyara ko ina duk da ba wani datti yayi ba tunda Iyan ta gyare ko ina,sai ta jona burner ta saka turaren wuta mai balain kamshi wanda lokaci daya  gaba daya falon ya dau kamshi,sai da ta tabbatar ko ina ya kama kamshi sai ta kashe burner din
ta wuce zuwa dakin ta dake a sama shima sabida gabatar sallah asr da ke kira a lokacin.

Woow shine kawai abinda ya fito daga baki na bayan tayi sallamar da tayi ta ƙutsa cikin dakin ni ko ina biye da ita don ganin gulma ni hafsatu😅

Ɗakin ya matukar ƙayatuwa,sak irin dakunan princesses din nan da ake nuna wa a tv na fina finan turawa,ko ina a tsaftace ga wani kamshi mai dadi dake tashi a dakin

Ga uban teddies a jere kan gadon da suka cika kusa rabin gadon,komai na dakin kalar pink ne da touch of purple wadanda suka kasance best colours din ta,tun daga paint din har gadon,labule,kafet da sauran tarkacen dake dakin duka da kalolin akayi amfani.

Towel din ta dake jikin hanger kalar purple ta dauko,a natse ta fara cire kayan jikin ta,sannan ta fada ban daki,wanda ya kasance kalar pink ne zallah,bata dauki wasu lokuta ba ta gama wankan,tare da dauro alwala ta fito

Darduman dake shinfide a gefe ta hau tare da saka jilbab hijab din ta sai ta warware towel din dake jikin ta ta tada sallah

Bayn ta idar aduoi ta shiga yi wa iyayen ta da ita kanta da tare da fatan samun cikar burin ta a rayuwa kafin ta shafe jikin ta ta tashi

ƘADDARA TA Where stories live. Discover now