👑 *GIDAN SARAUTA*👑
Written by *Zeeneert💕*
*Zeeneert* @wappad
*Page Three*
ASALINSU
Sarki Sulaiman babban sarki ne acikin Nigeria da babu yankin dazakaje ba asan dashiba tsabar tashen da mulkinsa yayi dama kuma adalcinshi ga talakawanshi,asalin iyayenshi nomads ne(Wanda akafi sani da fulanin daji) tun kakanni wanda basu da takaitaccen gurin zama suna yawo ne depending on the weather tayanda zasu samu su ciyar da dabobbbinsu dama su kansu ahakan ne har Allah yasauke su acikin garin Zaria wanda tun alokacin ba abakin komai take ba don mutane tsirarru ne kawai agarin. Tunda sukazo garin Zaria suka ji dadin zama agarin se suka kasa yin gaba suka kafa gida da kasuwancin su wanda ahakan ya bunkasa har suka saba da mutanen gari akazama daya. with time population na karuwa ah garin har garin Zaria yafara zama babban guri alokacin da Allah yadauki ran Sarkin garin bashi da magajin daza abama sarauta don haka akanemi wanda yacancanta aka bama wanda shine mahaifin sarki Sulaiman shima bayan shekaru tsufa tazo se mulki yadawo hannun Sarki Sulaimanu wanda alokacinshi bakaramin taka rawar gani yayiba don ganin yayi wani abun alfahari a yankin Zaria hakadai rayuwa tacigaba, Sarki Sulaiman yazama abun soyuwa ga kowa bama a Zaria kadai ba a kasar Nigeria bakidayan ta. Matar shi daya kwallin kwall wanda tunda ya aureta basu samu haihuwa ba har na tsawon shekaru takwas hakan kuma besa yakara aureba dukdama irin takuramasa da jama'a sukeyi da irin hakurinshi dama kuma addu'a dasukeyi gakuma subjects dinsu dakeyi musu. Bayan wani lokaci Allah yabama Zuwaira ciki kaman da wasa, ba karamin farin ciki sukayiba lokacin har yar kwarya kwaryar Walima seda akayi. Haka aka raini cikinnan kamar kwai harzuwa lokacinda Sarauniya Zuwaira tasauka inda ta santalo danta namiji kyakyawa dashi son kowa kin wanda ya rasa. Murna a masarautar da mutanen gari baki daya kamar suyi yaya. Ranar suna aka rada ma yaro suna Almustapha wanda mutanen gari ke kiranshi da Yareema tun haihuwarshi,ma'ana mai jira ya gadi Ubansa. Zuwaira da Mai martaba suka dauki son duniya suka daura ma yaron komai yace yanaso za ayimishi har tasowanshi, Almustapha yazamanto me kiriniya da son yawace yawace da freedom,tun yana shekara biyar akeson fara koya mishi swordfighting,hawan doki dayanda ake tafiyar da al'amuran Fada amma kwata kwata bayaso sabida baida passion for sarauta sam! wannan abun baidamu su Sarki ba se suka barshi a tunaninsu yarinta ne with time zefara dakanshi, Yareema Almustapha nada shekara bakwai Allah yasake bama Zuwaira ciki wannan karan anyi murna sosai don harta fidda rai ga haihuwa sede murnar batakai na lokacin haihuwar Almustapha ba
haka akayi suna lafiya akasama yaro Abdulrahman. tunda aka haifi Abdulrahman yazama abun so acikin masarautar sabida yaron akwai shiga rai. Shima kanshi Almustaphan yadauki son duniya yadaurama tilon kaninshi komai yasamu na Abdulrahman haka Abdulrahman dinma yataso yanason dan uwanshi komai tare sukeyi hakanan Almustapha bayason laifin kaninshi komai yana shigan masa sede abunda ya banbantasu Abdulrahman na matukar son sarauta tun yana shekara biyar yake koyon fada dason hawan doki daduk wani activities na sarauta,gashi da kwazo da kaifin basira gakuma son manyance. alokacin ne kuma akafara matsama Almustapha yadinga koyon abubuwa sede ranshi bayaso ko anfara koya mishi seya gudu. akwai ranar da Sarki Sulaiman yakirashi yayi mashi fada sosai wanda hakan betaba faruwa ba yayi kuka sosai sannan yadau alwashin fara yin abunda mahaifinshi keso don bayason bacin ran iyayensa kwata kwata don haka yafara participating dukda kuwa ranshi bayaso,bakaramin dadi Mai martaba yajiba ga canzawan First child dinnashi kuma hair to the throne! sekuma yawanci karfin koyon yakoma kan Almustapha aka daina bama Abdulrahman din attention sosai wanda hakan bakaramin sosa mai rai yayiba sede be nuna ba saboda shi yarone dabai cika tada hayaniya ba bekuma cika nuna damuwarshi a fili ba sede yakebe gefe yayi kukansa me isansa yashare hawayensa, Abdulrahman yakasance yaro meson rubuce rubuce barinma akan abunda yafaru dashi dakuma abunda yakeso tunda yafara wayau yakan zauna yazana kanshi a zaune akan kujerar sarauta kokuma yana tsaye rikeda sword jikinshi da kayan alfarma shiyasa koda yalura bazai samu sarautar ba anfison abaman Yayanshi seya rubuta cikin diary dinsa how he felt and the rest.
YOU ARE READING
GIDAN SARAUTA
FantasyA story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......