👑 *GIDAN SARAUTA*👑
Written by *Zeeneert💕*
*Zeeneert* @wappad
*Page Four*
Yajima zaune gurin yana saka da warwara kafin daga karshe yabude idanunshi daga lumshesun dayayi yashiga duba time a wristwatch dinshi. Ganin lokacin shan maganin Umminsu haryanaso ya gota yasa yatashi dasauri yanufi hanyar fita a makarantar don zuwa gida. Duk inda yawuce yanaji ana kuskus kokuma a tsaya ana kallonsa ana nuna shi anma ko a kwalarsa! Inda sabo yariga yasaba yakuma zame mai jiki! Shi abunma mamaki yakebashi yanda mutane basu wanke nasu kashin ba suke bin diddigin na wani! abu dayane yasani cikin su babu mai kusantar shi da maganan koyace zaikawo mai wargi so far as he's in his right senses ! Iyakacinsu zagi da maganar fatan baki! The only state dasu ke ci mishi mutunci shine when he's drunk.
Ayanzu ma dayake tafiyar wasu Yan Mata yahadu da agabanshi suna tahowa. Tunda suka dososhi ya lura dayanda dayar keta kallonshi kamar zata cinye shi inda dayar kuma data lura da hakan setayi saurin janyo hannun Kawartata suka canza hanya tanayi mata kuskus.
"Muyi sauri Aisha mudauko kayan kada tailor dinnan yagudu"
Wabce hannunta Aisha tayi sannan tace "Toh miye nawani canza mana hanya? Wai bakiga hadadden gayen dana gani bane inakokarin inyi shooting shot dina?" Aisha takarashe maganar tana kokarin sake komawa direction dinda Almustapha ketahowa,damkota
Muniba tasakeyi cikin sauri tana fadin "Don ubanki naga abunda kika gani din nima and I'm doing nothing but to save you! inkuma so kike kitashi a aiki daga yau a idon duniya sekije ki ai" Aisha da is literally confused taceda Muniba "Bangane me kike nufi ba?" Kasa kasa ganin Almustapha yakusa isosu Muniban ke fadin "Yareema Almustapha ne fa Aisha!" Aitake jikin Aisha yafara bari batakuma yi wata wata ba tabi direction dinda Muniba tafara bidasu dazu,Muniba tabi bayanta dasauri tanacewa ta jirata anma Aisha se kara sauri take kamar zata tashi sama,cewa take"Yau na shiga uku na lalace Muniba cewa fa akayi inmutum ya yarda yahada ido dashi toseyayi anfani dashi! nashigesu na Allah yasa bamu hada idanuba" Aisha takarashe maganar kaman zatayi kuka tana tatttaba fuskarta da gumi keta yankowa. Yar dariya Muniba tasaki ayayinda takamo ta suna tafiya tare tace "Keba uwar jaraban son maza ba! Kowa kika gani kinaso! Wataran sekin debo ma kanki jangwamgwam ai!" Aisha tace "Wallahi nadaina dagayau. Kawai yamin kyau ne dama. danasan shine Almustapha koma nasan zamu hada hanya aiko makarantar ku bazan zo ba,nikam wace irin kaddarace takawoni cikn SAMARU yau" me Muniba zatayi inba dariya ba,harda su rike ciki ganin yanda Aisha ke exxagerating abun kuma. Tace "Aaaa kekuma banda Exxaa mana Aisha...."
Aisha dahar lokacin hankalinta yake atashe tace "Babu wani Exxa wallahi! Inaga baki taba jin abunda ake fada akanshi baneba shiyasa and it happens I swear because har hukuntashi mahaifinsa yakeyi" Muniba tace "Bantaba jiba shine nake kokarin protecting dinki daga gareshi?" Aisha tace "Hakane kuma! Ammadai yayi asara yakuma bata ruwansa da tsalle! Ga kudi,ga mulki,ga kyau,ga iya gayu amma yarasa wani irin rayuwa zaiyi sai wannan?" Muniba dako hirar Almustaphan bason entertaining take ba tsabaryanda taki jininsa tasaki tsaki tace "Kede kibar zancennan kawai! Rayuwarsa ce yaje yayi yanda yaga dama can ta matse musu. Muyi indauko kayan mukoma gurin macucin tailor dinkin nan" adole Aisha tahakura suka canza babin hirar tasu zuwa wani.
Almustapha kuwa tuni yayi wucewarsa gida yabarsu da kwasan zunubi. Koda ya isa samun su Amira yayi suna cin abinci,sannu dazuwa sukayi mishi sannan Amiran tazubo mishi abinci bedamu da kanshi ba matsawa yayi kusada Ummin sannan yajingina mata pillow ya kwantar da'ita ajikinshi sannan yayima Amiran alama data miko mishi plate din abincin inda yashiga bama Ummin abinci tanaci ahankali harseda tanuna takoshi sannan yadauko drugs din yabata tasha.
Kallon fuskarta yayi sannan yace ahankali kaman wanda bayason magana
"How are you feeling Mother?".
Lumshe idanunta tayi alamun dasauki,bekuma cewa komai ba sema cigaba da kwanciya datayi a jikinsa yanajin su Afiya suna hira abunsu jefi jefi inda shikuma yakebinsu da kallon tausayi tareda tunanin koyaushe komai zai wuce?
YOU ARE READING
GIDAN SARAUTA
FantasyA story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......