A'INDO Tantagariyar Yar Aiki

1.2K 48 6
                                    

https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
            *A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨


                     *NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋


*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚


*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*
 
                👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
     _and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*



_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_


       *Page -49-50*

Kallon Hajiya yayi yaga wai ita tayi maganar ko kuwa?

   Yace"haba Hajiya wacen yarinyar da take bakauya ya za'a hadata da wanan nutsatsar."🙄

  "Hum yaro man kaza ,ai sai kayi,ni zan shiga na kwanta,ka tashi kaima ka koma b'angaren ka."
  Hajiya na gama fadar haka ta koma sama,tabar Alhassan cik'e da mamaki ,da kuma tambayoyi a Zuciyar sa.

      Fitowa A'indo tayi da cup a hanun ta ,tana tafe tana shan tea ,tana danna wayar ta,dan chatting suke da Bashir,table ta zauna na cin abinci,taci gaba da da chatting dinta tana dariya,inda gaba-daya hankalin Alhassan ya karkata a kanta ,sam bata ma san yana nan ba,sanin da tayi cewar Hajiya ta koma b'angaren su.

   Wayar ta ce tayi kara ma'ana Kira ya shigo,dagawa tayi tana dariya,fararan hakoran ta,mai d'auke da wushirya a tsakiya,wace ta kara ma  hakoranta kyau suka bayyana,tace"hahhh Kalbi ya dai dagaske nake maka fa,Allah na yarda da zaran an gama auren Husseina kaima ka turo,tunda su hajiya ma sun yarda."

  Duk wanan hirar da take a kunuwan Al'Hassan ,ransa yayi bala'in baci,yayin da hankalin sa ya tashi Jin tana cema wani ya turo ,har zai tashi ya nufe ta ,kuma sai ya fasa,zaune yake anma ji yake kamar ana zuba masa garwashi a zuciya,duk da bai yarda cewar A'indo bace,ya ma za'a ce itace,bayan wacan Yar kauye ce,jahila,marar aji kuma mumuna,ya za'a hadata da wanan,daga gani tanada aji,ga ilimi,ga kuma kyau,gata tamkar ba'indiya,Kai ina Hajiya zolayar sa kawai take.
  Ji yayi gaban sa ya fadi Jin tana cema wani wai ya turo waye wanan kuma.

   Gama shan coffeen ta tayi ta tashi,sai yanzu hankalin ta yakai kansa,ko shekara nawa zatayi bazata taba manta wanan bakin mugun ba,jin tayi gaban ta yayi muguwar faduwa.kenan dai yazo,hum Alhamdulillah tunda dai yanzu ba matar sa nake ba,bai isa ya takurani ba,kuma ma ina ruwana dashi."

     Sakin ajiyar zuciya tayi sanan ta daidaita kanta,tazo ta gaban sa ta huce,wanda kamshi turaren ta ya dawo dashi daga duniyar shaukin ta,har takai gurin caji ta zage wayar salma,zata fita taji yace"ke bakisan ki gaisar da mutane  ne ba,kina ganin mutane anma bazaki gaida su ba."

   Cak A'indo ta tsaya,gaban ta na faduwa,dakewa tayi ta kirkiro murmushin tura haushi na gefen baki,ta juyo,ta zuba masa ido cik'in ido,wanda ya yasa  faduwar gabansa dum,ba shaka wanan yarinyar ce,ko gizo ne,kai hakan bazai taba yiwu ba,ta ya ma za'ace itace ina sam bai yarda ba.
     "Humm ashe akoi mutum a gun Sorry ban lura bane,ina wuni,anzo lafiya to Masha Allah."

    Tana gama fadar haka ta juya tayi ficewar ta,yayyin da Zuciyar ta ke mata tafarfasa.

    Wajen su idrissa ta nufa dan  fada musu sakon Hajiya,anma ta iske har sun tashi basa nan,hakan na nufin sun gama tadin,tab yau wace rana hum.
  .ta fada tayi gaba abunta,barin Alhassan tayi cik'e da baki,shi fa bai gane ba,da sauri ya tatara computer da wayoyin sa yabar b'angaren,ya nufi b'angaren idrissa iske sa yayi ya fito daga wanka.
  "a'a bros kaine nayi tunanin ma kayi barci saboda gajiya, murmushi Alhassan yayi sanan ya fido wayar sa da ya d'auki A'indo lokacin da ta fito daga kitchen tana Shan tea bata sani ba,yace"kanina dan Allah wacece wanan,ya nuna ma Idrisa photon ,Idrissa ya  duba ,yace Yaya yaushe ka d'auki wanan pic din.

INA SON SHIWhere stories live. Discover now