Ina son shi

2.3K 26 7
                                    

[05/01 à 20:05] Maimouna Matar Abdoulahi: 💝💝💝💝💝💝
     💘💘💘💘
   *INA SON SHI*
    _(ya tsane ni)_
            🌹🌹🌹🌹🌹🌹
                  🌼🌼🌼🌼
                       ✨✨
                           ✨

                  *NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best writers Among all writers_)📚


*Page 1-2*

   ,,,,,,,,,zaune take rakube k'ofar wani katon kamfani,Wanda fadar tsaruwar sa ma bata lokaci ne,tayi tagumi,in ka ganta kace wata mahaukciya ,domin dai duk mai hankalin da yaga yanda take da kayan dake jikin ta to zaiyi tunanin sabon kamu ce,wani tsohon hijabi ne a jikin ta ,duk ya tsufa ya yayage duk da ka gansa kasan ya gaji da yagewa ana  dinke sa,duk yabi ya yayage , atamfar jikin ta dinkin riga da zani shima ya tsufa har tayi fari,   baka ce anma ba sosai ba,dan bakin ta mai kyau ne,irin na Americaine  beauty dinan,duk yanda take hakan bai hana na gano sirin dake fuskar ta ba,tanada madaidaiciyar  face  mai d'auke da fararen idanuwa masu girma kuma farare,gasu kyawawa,har walkiya suke in ta kalli mutum,,tanada karamin baki,gashin girar ta nada dan yawa, yarinyar dai tanada kyau sosai kawai rashin gata ne ya maida ta haka.

       "Ke!!!
Wani security ya buga mata tsawa wanda ya rikitar da ita ta nemi zabgawa a guje ,"ke maza ki tashi ki bace min a nan ke wai yaushe zakiyi hankali kusan kullum sai an koreki anma sai kin dawo."

    Murguda masa baki tayi tace"tab aradu saide kuyi hakuri dani dan saifa na ganshi ,idan ba haka ba zan tada zanga-zanga anan."
   Yarinyar ta fada ,juyawa security yayi ya koma ya zauna dan yasan shairin ta yanzu zata tara masa jama'a kamar yanda tayi ranar,shikam bai taba ganin naci da jaraba irin na wanan yarinyar ba,haka ta wuri a gurin bata ga muradin ran nata ba,Saida aka tashi daga kamfanin sanan ta juya ta tafi yayin da wani zazafan zazabi ya taso mata a lokaci daya,saboda rashin ganin sa,Wanda a kullum idan bata gansa ba to wanan ranar sai tayi zazabi.

         Kwance yake cik'in bargo sai rawar dari yake alamun yana jin jiki.

   Fitowa tayi cik'in shirin ta Wanda idan ka ganta zakayi tunanin yan Mata ce Wanda kuma abun ba haka bane,domin kuwa Matar aure ce sanye da siket,da riga wanda suka matse ta,ta d'aura d'ankwali,sai dan karamin mayafin da ta d'aura saman kafada,tasa takalmi mai tsini fara ce gajera,kyakaywa tana taunar shuiwingwom ta nufo wajen sa "Prince ni zan tafi boutique dan akoi kayan da za'a kawo yau zanje a kawo gabana,zan kai dare so na bar komai idan kana bukata bye."

   Tana gama fadar haka ta fara kokarin fita,kansa ya Fido yace"Zinat kina so na kuwa,shagon ki yafi lafiya ta,bazaki iya tsayawa ki kulla da mijin ki ba..........

      Kallon sa tayi shekeke ,sanan daga bisani ta gyara yanayin fuskar ta tace"kayi hakuri baby na,kasan ana jira na a boutique na,bayan haka har Salon dina kwana biyu ban leka ba bansan abinda ke wakana ba,dan haka kaga ko na zauna ba ni zan baka lfy ba,so plz Ahmed ka sarara min haba."

   Tana gama fadar haka ta fice daga gidan ."

   Share  kwalar da ta fara zubo masa a idanun sa yayi Allah na gani yana bala'in son Matar sa Zinat anma sam ita bata san yanda zata kulla dashi ba,shi namiji ne mai son kula ,tarairaya,a nuna masa So,gashi dai yanada komai bai rasa komai ba,kyau ,ilimi,gata, mutunci,kwarjini ,kudi,shine Wanda mata ke  so anma shi baya kulla su,bai taba ba yan mata fuska ba ,bare ya basu damar nuna masa son da suke masa, Zinat kadai yaba dukanin Zuciyar sa da komai nasa,anma ta watsar dashi.
  Waya ya d'auka ya kira doctor Said kuma amininsa ba'a d'auki minti ashrin ba sai gashi a gidan bayan sun gaisa ne,Saif ya duduba sa yace"ya Salam Ahmed kanada mata kake shiga wannan  halin,a gaskiya abokina wannan  zaman da kakeyi in baka d'auki mataki ba zaka iya halaka kanka, Ahmed ba yau nace maka ba Matar ka zinat bazata iya da kai ba ,ka nemi jinsin ka ka kara aure dan wanan abun da ka d'aukan ma kanka ba mai bilewa bane."
   Bata rai Ahmed yayi yace"a gaskiya Saif banajin zan iya son wata ya mace bayan matata."
" To haka zaka tsaya kwanan ka su kare tun lokacin ka baiyi ba,ka sani fa wannan sperm din da kake bari a jikin ka zai iya daskarewa ya zame maka matsala a ciki ma harda matsalar haihuwa,kaida kanka kace min rashin gamsuwa ya janyo maka wanan halin zazabin da kake ciki."

INA SON SHIWhere stories live. Discover now