5

1.3K 36 0
                                    

*illar mazan zamani*

*Aysha A bagudo*

*Maimuna matar Abdullah*

*Yar mutan kagara*

page 21to 25

.....tsawon minti talatin tayi  kwance agurin tana murkudusun ciwon ciki , wani irin azaba take ji daga kasan mararta har zuwa ilahirin gangar jikinta wanda hkn ya haddasawa jikinta daukar kirrma..

kasan mararta ya curewa guri daya tuni gumi ya rufeta yashiga tsatsafowa mata agabadaya ilahirin jikinta banda juya kai da ciza labe babu abinda take .

cikinta da mararta ne sukayi wani irin murd'awa da karfi lokaci daya ta saki kara razananniyar tare da furta "wayyohhly Allah nah cikina bayana zan mutu mutuwa zanyi can kuma tasoma jin wani   danshi dashin ruwa me zafi daga kasanta yana diga a saman pent dinta  kmr ance ta duba , taga jini a matukar zabure ta mike tsaye jikinta na sake daukar rawa tashiga bin jikinta da kallo tabbas jini tagani wanda hkn ke  nuni da cikin jikinta ne ke yunkurin  Fita daga jikinta.

wani sanyayen ajiyar zuciya ta sauke take wani sanyin  dadi  ya rufeta lokaci daya km ta fashe da wani marayan kuka tasoma daga kafafunta da kyar tana cillasu har takaraso  bakin titi  inda zata samu adaidai zuwa unguwarsu .

tsayuwar minti goma tayi abakin titi batare da tasamu abun hawa ba sakamakon yanayin unguwar hkn yasa tasoma takawa ahankali tana jan kafa.

a matukar jigace takaraso gidansu wanda xuwa lokacin  nishi ma da kyar take iyawa, dan  tasoma jigata matuka.

tana karasa shigowa d'an tsukukun dakinsu ta zube kasa warwarss tana janyo numfashi da kyar tana fitarwa ahankali hannuta dafe da mararta tana murkususu .

malika da imtisan  sukayo kanta a matukar tsorace hankalinsu a tashe suke tmbyrta inada taje.

" yaya hafsat ina kike je?

" tun da'zu muke zaman jiranki ?

imtisan ta kara dacewa  "  innarmu har fitsari tayi akwance ,da kyar nida malika muka canza mata kaya , jin har lokacin tayi shiru taki cewa dasu komai sai faman rike ciki take tana mulmula a simintin dakin ,yasa suka sake yowa kanta sosai suna kiran sunanta gbdy idanunta sun juye  wanda hatta bakin dake cikin kwayar idanunta sunyi sama da kyar take motsa labbanta ahankali tana kiran "wayyohhhly Allah cikina mutuwa zanyi kucewa innarmu ta yafe min zan mutu rayuwata tazo karshe tana kaiwa nan numfashinta yssoma kokarin barin gangar jikinta  .

cikin rawar jiki malika ta rike hannuta tana jijigata tare da kiran sunanta" "yaya hafsa   me ya sameki dan Allah karki mutu ki barmu baba ya tafi ya barmu ga innarmu kwance idan kika mutu zamu shiga kuncin rayuawa ,itama imtisan ta riko dayan hannuta tana kuka tana kiran sunanta kafin kace me tuni jini ya ballewa hafsa yashiga tsiyaya tmkr ruwa , aiko suna ganin hk suka fito  aguje zuwa kofar gida suna ihun da kururuwar  neman d'auki .

"Kallo daya zaka musu kagane suna cikin tsagwaron tashin hankali ihu kawai suke da iya kancin karfinsu suna sambatu .

mahaifiyarsu kuwa tana kwance a daki jikinta na rawa rawa gabanta ya dinga faduwa ,duk da batasan abinda ke faruwa acikin  gidan ba amman tana iya jiyo  sautin muryar malika da imtisan wanda hakan ya  tabbatar mata da akwai matsalar dake faruwa da yaranta daga kwance datake Tashiga karanto adduar da idan mutun ya tsinci kanshi cikin kunci  *allahuma la'a sahla illa maja'altahu sahla wa'anta taja'alul huzna iza shita sahla*
hawaye na gangarowa ta gefen idaunta .

a kofar gida kuwa malika da imtisan ihu suke suna kukan  ataimaka musu kar yayarsu ta mutu inda.

"Wayyohhly yaya hafsa dan Allah karki mutu karki mana haka bamuda kowa daga mahaifiyarmu  sai ke ,kece gatamu wayyohhly Dan Allah jama,ar unguwa ku taimaka kar yar'uwarmu ta mutu....

Suna cikin wannan kukan me cike da ban tausayi da ta'ba zuciya  da wani makocinsu me suna alhaji kamalu ya fito  daga cikin gidansa cikin 'bacin rai yana  yatsina fuska hade da daka musu wata razananniyar tsawa .

Alhaji kamilu mak'ocinsune kuma attajiri ne shahararran dan kasuwa babu kasar da bai zuwa domin kasuwancin siyar da siyarwa cike da bacin rai ya fara musu ihu da hargagi "wai ku mene haka ne saboda Allah?

" Kunbi kun addabi jama'a da iwace iwace kun hanamu hutawa da iskancin kukanku ,sai faman hayagaga kukewa mutane ,na dawo daga tafiya kenan ina bukatar hutawa amman hayaniyarku ta hanani hutawa .

Yadda suka yana bambamin fada yasa suka zube kasa bisa gwiwowinsu agabansa suna wani irin kuka me taba zuciya kamar ransu zai fita .

"Dan girman Allah alhaji ka taimaka mana ka kai yayarmu   asibiti wallahi idan baka taimakemu ba mutuwa zatayi ,"dan girman ka ceci rayuwar yaruwar kar mu rasata .

A matukar tswace yace "kuyi mutane shiru duk  kun bi kun cika wa mutane  kunne da shirmen banza da wofi  bakwa tinanin akwai mutane acikin gidajensu suna bukatar hutu.

muryar malika da imtisan na rawa suka sske hada baki gurin cewa "kayi hakuri yayarmu ce acikin gida bata numfashi gbdy mutuwa zatayi  dan allah ka taimakemu mukaita asibiti ...

wata uwar harara ya zabga musu tare da cewar "uwar asibiti zan kaita  ba asibiti wannan gatalalliyar datayi sanadin mutuwar ubanta zan kai asibiti ," ai gara ta mutu ma a rage iri a duniya dan kuwa da haihuwar irinsu Hafsa gara barinsu dan hk ku saita sautinku ina bukatar  hutu acikin gidana yana gama fadar hk ya juya zai koma cikin gida .

"dan girman allah karka ce haka Allah ka tsaya ka taimakamana kaima wata rana Allah zai taimakeka .

ya juyo a fusace "idan taimakon  allah a hannuki take idan aka  tashi taimakona ki hana ji'iran yara kawai wanda zaku.kashe kuke nema kun kashe ubanku kuna neman kashe mak'otanku  yana gama fadar hk yashige gidnsa ya meida get garamm ya rufe yana cigaba da zaginsu haka kawa za'a nemi takura rayuwar mutun.

Alhaji tahir wanda ke cikin gidansa yasoma kokarin fitowa zuwa kofar gidan  , alhaji tahir shima  shahararran dan kasuwa ne sai dai shi  ma nemin mata ne na bugawa ajarida dan shima babu kasar da baya zuwa bashida mata dan tun rasuwar matarsa bai sake yunkurin sake yin  aure ba yayi zamansa haka sai dai yana da yara biyu duk mata suna gurin kakarsu ta gurin uwa  .

duk unguwar babu wanda bai san halin alhaji tahir  gurin neman mata ba , hatta yara kanana baya  barinsu lafiya   matukar yaji yarinya karama ko matashiyar budurwa  ta biya masa rai, tofa yazama dole ya gusar da sha'awarsa akanta .

Yana gama fitowa daga cikin gidansa yakarasa zuwa inda su   malika suke tsaye suna risgar KUKA  ya kamo hannun malika wace ya Dade yana k'wad'ayinta  yajata cikin gidansa tare da cewa imtisan tajirasu magana kawai zasuyi yanzu zata fito .

Imtisan taja ta tsaya tacigaba da  KUKAnta tana goge hawayen dake tsiyaya bisa kuncinta , ita kuwa Malika zuciya daya ta  binsa abaya a tinaninta taimakonsu zaiyi shiyasa ya jawota ciki .

Atsakiyar parlour'n sa yaja ya tsaya tare da juyowa ya  fuskanci Malika sosai  ya tsura mata miyagun idanunsa yana kallonta tare da kai hannunsa saman kafadarta ya dafata yana sake jin wata muguwar sha'awarta na tun karosa dan har jikinsa ya fara kirrma.

muryarsa a kasalace "yace yi shiru malika zan taimaka muku tayi saurin durmusawa kasa tare da cewa "mun gode alhaji .

Ya numfasa sannan ya sake bude bakinsa "zan.taimaka muku sai dai fa da sharadi akan taimakon .

Muryar Malika na rawa sannan kuma cike da murna "tace wani sharadi ne ?

Batajira jin ma  me zaice ba tacigaba  "koma wani irin sharadine badamuwa ni dai kawai kataimaka mana ka kai mana yayarmu asibiti karta mutu .

Lashe lip's dinsa yayi tmkr tsohon maye yana wani  murmushi ya matsota sosai har suna iya jiyo numfashin juna jin dumin numfashinsa yasa taja baya da sauri tana rawar jiki .

Sake matsota yayi sosai sannan  "yace kanki zaki  mallaka min kawai idan na d'an 'dana gardinki zan miki komai ciki kuwa har da lafiyar yayarki da mahaifiyarki........

ILLAR MAZAN ZAMANIWhere stories live. Discover now