11

1.1K 37 0
                                    

*illar Mazan zamani*

*3 writer's*

*Aysha bagudo*

*maimuna matar Abdullahi*

       *And*

*Yar mutan kagara*

Page 45

....Cikin kankanin lokaci ya iso asibiti  da nihal yana wani irin gunji kuka na tashin hankali , gadon marasa lfy aka turo aka daura nihal akai ,da gudu gudu sauri sauri aka shiga d!akin likita daita domin ceto rayuwarta ,sakamakon jinin dake tsiyaya ajikinta .

Likitoci suka rufa akanta suna kokarin bata taimakon gaugauwa, abun gwanar tausayi domin kasanta yayi kaca kaca gabadaya shugaban 'barayin nan yagama budeta .

Salman  Kam  ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zariya yake daga reception zuwa bakin d'akin da'aka shiga da nihal , Salman shi kad'ai yasan cikin tashin hankali daya tsinci Kanshi  ,duk sanda ya tuna sa'ida  da wulakanci data masa agaban yan ta'adda tashin hankalinsa  dad'duwa yake.

"Yarasa wace irin halita ce ita ,mara mutunci da kanmu kai ,da rashin sanin darajata ta uwa ,ya tabbatarwa kansa dakace sa'ida takasance  uwa ta gari ga nihal dabata aikata abinda tayi agaban yan ta'adda ba ,allah wadai yayisa sau ba adadi tare da matsanancin tsanar aurenta da yayi arayuwarsa .

"babban kuskurena  kenan dana aikata arayuwata ta  auren yar ta'adda bisa rashin sanin halinta na boye... kuka yake sosai tamkar karamin yaro "nayi danasani aurenki arayuwata  "naxalinci kaina da kaina dana aureki sa'ida har kikayi silar zama uwa ga nihar "meyasa na aureki?

"meyasa ban zabarwa yarinyata uwata gari ba?

"ai ko abinda bazai kasance da kai ba kenan, dole ka auri mata irin sa'ida tunda zina shine aikinka zuciyarsa tabashi amsa da hk wani sabon kuka ya 'barke dashi ,yana buga kansa da bango .."hakika na cutar da kai  "ashe ba amanar yaran mutane naci ba, amanar kaina naci.. "me yasa na cutar da kaina gashi zunubina ya shafi tilon diyata ..?haka ya dinga kuka yana cigaba da buga kansa da bangon gurin har sanda likita daya gama dinke nihal ya fito yana bashi umarnin yabiyoshi..

Satin nihar daya a asibitin oncontion's  sannan ta farfad'o cikin wani mayuwacin hali, sosai take jin rad'ad'in  pata pata da 'barawon yayi mata ,Dan sai da aka mata dinki babu adadi a gabanta , kallo daya zakawa yarinyar Tabaka mugun tausayi, tayi baki ta zabge gbdy ta rame sai idanuna,a wannan lokacin Salman bakaramin danasani yayi arayuwarsa ba ,yayi nadama tafi sau ba adadi, yayi kuka yayi kuka yayi dayasani arayuwarsa, alokacin neman hafsa yake ido bude saboda gabadaya matan da yayi ta'amali dasu abaya, babu yarinyar daya disviging sai hafsa ,kuma Yasan babu hakin daya tsaya masa kuma yake bibiyar rayuwarsa kamar na hafsa, saboda shi ne ya fara bud'eta, shine ya fara 'batata ya bud'e mata ido akan sanin dad'in nmj,shine ya nunansheta zandariya da dad'in dake tattare daita ,yayi mata ciki  ya koreta yace "baisan da zance ciki ba , har hakan yazama silar lalacewar rayuwata ta bige da bin maza , ido bude yake nemanta domin yaba ta hakuri abinda ya aikamata .

*************

Hafsat da malika tafe suke sanye cikin zubulelen hijabinsu  har kasa gwanin sha'awa,sun taho daga islamiyya ,suna Tafe a natse suna Hirarsu kasa kasa ,Kowanne rungume da alqurani.

sai ga wata dalliyar moto kiran g wago tasha gabansu, ahankali mamallakin motar yayi warning din glass din motar kasa kad'an "assalamu alaikum sukaji sautin daddiyar muryarsa me shiga jiki da tsintsike jijiyo jiki ta doki cikin dodon kunnensu .

hafsa da malaki sanin mahimmanci Sallma da sukayi, yasa suka had'a baki gurin amsa masa sallama"waalaikul Salam warahmatul Allah.
Sannan sukacigaba da tafiyarsu a natse bazakace su ne wad'an nan mutanen da sukayi yawon ta zubar ba .

ILLAR MAZAN ZAMANIWhere stories live. Discover now