♦♠♦♠♦♠
*K'ARSHEN K'AUNA*
♠♦♠♦♠♦®☄
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION✍🏻*
{ _Gaskiya d'aya ce daga k'inta sai 6ata, burinmu mu fad'akar da Al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._}
🎐G. W.A🎐
*GASKIYA DOKIN K'ARFE.* 🏇🏻*Storry* *&*
*written by*
*Momyn Muh'd*
{ *RASHBEEL*}Page 1to10
"Amma wallahi babur d'in Nan idan baka ta Shiba ka cuce ni Haba ba ka ta'shi lallacewa ba Dan tsabar bakin ciki sai da zanje gurin masoyiya ta, haba wannan wa'ne irin bakin ciki ne, dogon tsuki Ibrahim yaja tareda nadawa mashin din duka.
Hannun'sa yasa cikin Aljihun wandon sa ya ciro wayarsa Nokia 1sim wacce ake Kira rakani Masai Sai ruri wayar keyi.
dauka yayi tareda Kai wayar akunnen'sa,
cikin Farinciki da sigar lallashi
"ya'ce Baby na kinji ni shiru har yanzu ko??"D'ayan 6angaren cikin zazzakar muryarta ta'ce. "eh Mana baby har yanzu baka zoba ta karashe maganar da Dan kukan shagwa6a"
"Aa kar
"kiyi kuka kinji ko gani nan tahowa yanzun Nan,Ummah ce ta Dan aike ni Amma na dawo yanzun nan Zaki ganni kinji ko "
"Lokaci daya ta Saki ranta tareda cewa ah ah to bakomai baby tunda Aiken lada ne ai ba'a wasa da aikin ummah"
"Yauwa baby na ai Nasan kina da hankali to yimin murmushin ki Mai tsadar Nan"
"Yar dariya tayi tare da cewa sai dai kazo .
Kiss din wayar yayi
kafin ya yanke Kiran shiga duba wata number yayi,Yusuf naga ya Kira
Yana dagawa ya ce "hello Yusuf Dan Allah Kana Ina Wallahi gurin Sofiya zanje kaga babur Dina yaki tashi Dan Allah kana Ina??,
Ka taimaka min kazo ka rakani ko ka aramin naka babur din naje Dan Allah"
Daga bangaren Yusuf kuwa cewa yayi wlh bana gida Ibrahim Kuma Ina nesa ne sosai,
"Amma Mai zai Hana ka hau mashin sai ka biyashi ya Kai ka"
"Haba Yusuf Kai kuwa idan inada kudin mashin din ai kasan bazan kiraka ba Allah ko nera Babu ahannu na Dan girman Allah ka taimakamin kazo ka ajeni pls."
Dan shiru Yusuf yayi na wani lokaci sai daga baya" ya'ce to ganinan zuwa Amma fa ajeka kawai zanyi indawo domin firarku bamai karewa ba''ce ."
Na amince aboki na Dan Allah kayi sauri kazo.
Jan mashin din Ibrahim yayi ya Mai da shi cikin gidan su Wanda gidan madai dai chi ne farkon shiga ga dakinsa Nan.
idan aka shiga ciki
Akwai rijiya sai baranda da Kuma Babban falonsu Wanda acikin sa dakuna ukku ne Dana umman sa sai na kannan sa Mata su ukku gefe daya kuwa Dakin mahaifinsa neBayan ya aje mashin din cikin barandar kofar dakinsa
Alokacin na Kare Masa kallo Yana da tsayi baki ne Amma ba baki sosai ba Yana da faffadan kirji Kuma ga manyan ido Yana da hanshi Mai tsayi gwargado Ibrahim bai da masoka Yana sanye cikin shadda blue Wadda ita ba tsohuwa ba ita ba sabuwa ba
Ya Kai minti latatin tsa'ye agurin
Fita yayi kofar gidan
Yana fitowa ba jimawa sai ga Yusuf ya iso da roba robansa Fari qal sanye ya'ke cikin kana'nan KayaIbrahim na ganin sa yasaki murmushi baijira komai ba ya hau mashin din suka Fara tafiya ahanya Yusuf keta faman tsokanar sa Yana cewa Kai Anna Sofiya anbuga dakai anbarka