♦♠♦♠♦♠ *K'AR'SHEN KAUNA*
♦♠♦♠♦♠
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*Story* *&* *written*
*By*
*RASHBEEL*😍*PAGE* 16to20
~"Kuma har gobe Ina nan Babu gudu Babu ja da baya sai na auri Ibrah...........,~
~Bata k'arasa ba taji saukar marin'da kad'an yarage tayi baya ta fad'i ci'ke da mamakin Wanda ya ma'ta wannan Marin ta d'ago fuskar ta~.
Ummah tagani Tsa'ye agaban'ta Sai huci ta'ke yi.
Cikin tsananin 6acin Rai,
Ummah ta'ce "Ashe bakida mutunci Safiyya Har ki rik'a jifar Nasir da irin wayan'nan Munanan kalamai Haka".
"har yau'she Kika iya fitsara Haka, ban sa'ni ba to wlh muddin na koma Jin Haka Sai na mugun sa6a Miki."
"Kuma ko bana ra'ye ban ya'fe Miki ki auri wani ba idan ba Nasir ba kinji na Gaya Miki".
Sofiya na Jin Haka ta durk'ushe agurin tana wani irin kuka Mai ciyo, ta'reda cewa "na shiga ukku!" "ummah Dan Allah karki mana Haka wlh bazan iya rayuwa ba'tare da Ibrahim ba, mutuwa zanyi, ummah Dan Allah karki min Abinda bana so"
Kuka ne ya ci karfin ta.'Ummah kuwa cikin tsananin Jin haushin Sofiya ta'ce "wlh sai dai ki mutu Amma auren ki da Nasir kamar anyi angama ."
Ummah na Kai wa Nan tabar gurin afusa'ce.
Nasir kuwa Yana tsa'ye Yana kallon Sofiya cikin 6acin Rai da mamakin wai kamar shi har akwai macen da zata ce Bata son sa.
Tuna yayi daga U.K har Nigeria irin manyan matan da ke d'okin son shi Yana wulakanta su.
Amma yau shi ne ke son wannan Yar ta tsitsiyar yarinyar tana Mai Rai nin wayau.
Duk'awa yayi kusa da ita,
Da sauri taja baya,
Shi kuwa wani Dan murmushin ta Kai ci yayi kafin ya'ce
"Gudu na ma ki ke?" "wato Sofiya Ina so na sanar da'ke cewa Zaki So ni fi'ye da son da ki ke yiwa kanki,
Zaki So'ni fi'ye da son da kikewa uwarki da ubanki""Wlh wannan Alkawali na ne Kuma idan hakan bai faruba namiki Alkawalin bazan ta'6a Mu'amalar aure da ke ba! har abada' Kuma Zan sauwak'e Miki ki dawo gidan ku".
Yana Kai wa Nan ya tashi yanufi hanyar fita.
Tsa'ye ya samu ummah atsakar gida sai safa da marwa ta'ke zuciyar ta ci'ke da Jin haushin Sofiya.
"Toh Aunty ni Zan tafi sai najiki idan Dadyn nata ya dawo"
"Amma fa bana buk'atar bikin Nan ya wu'ce nan da 2weeks"
washe baki ummah tayi tareda cewa, "haba Nasir karkaji komai wlh biki kamar anyi shi Allah ya kai mu lokacin kawai"
Dubu d'ari ya ciro ya bata tareda cewa "ga wannan kisa Kati idan ya dawo ki sanar Dani".
Godiya ta Masa sosai.
ficewa yayi daga gidan ya shiga motar'sa ya nufi gida.
Ummah kuwa gurin Sofiya ta nufa
Wacce har yanzu tana durk'ushe agurin tana kuka,