♦♠♦♠♦♠
*K'AR'SHEN KAUNA*
♦♠♦♠♦♠Storry And written by *Momyn Muh'd*
Page 11to15
~Da mamaki Yusuf ya'ce ko Lafiya Amma Bari naje gurin nagani~
wani mutum ne ya biyo ta kofar gidan su Sofiya ya na tafiya Yana surutu Yana cewa yanzu NI Ina Zan samu wannan uban kudin har dubu ukku. NI da Naira Ashirin ma sai na "kwashe sa'ti ban samuba
Idanun'sa ne suka sauka akan wayar Ibrahim da ke akatsa hannu yasa ya dauka ba wani tunani
Tsayawa yayi agurin Yana duba wayar washe baki yayi tareda cewa wani hanin ga Allah baiwa yanzu wannan wayar ko dubu daya na saida'ta Zan Dan rage zafi
Bai Gama wannan tunanin ba Yusuf yayi parking din mashin Dinsa kusa dashi dasauri mutumin ya 6oye wayar abayan sa tareda
Kallon Yusuf cikin alamun rashin gaskiya ya'ce ma Yusuf
Sannu da zuwa
Yauwa Yusuf ya amsa atakaice
Da sauri Yusuf ya ciro wayarsa ya K'ara Kiran number Ibrahim shi kuwa mutumin har ya juya zai tafi sai ji yayi waya ta Fara k'ara
Juyowa yayi ya kalli Yusuf
Yaga Shima Yusuf din shi ya ke kallo da alamar tambayaAnan ta'ke ya fahimci wannan mutumin bayada gaskiya
Cikin zafin nama Yusuf ya shako wuyan rigar mutumin tareda cewa me wayar abokina keyi ahannun'ka
cikin rawar murya mutumin ya'ce Dan Allah bawan Allah kayi hakuri wlh yanzun Nan na tsinceta anan Dan Allah kamin afuwa kaji
Wani mugun Mari Yusuf ya sauke Masa tareda cewa Ina abokina ya ke Ina ka kai'min abokina wlh ko kafito dashi ko hukuma ta rabamu da Kai
Mutumin najin Haka yafara kuka tareda duk'awa har k'asa Yana rantsuwar bai San komai ba akan Abinda Yusuf ke magana
Nan ta'ke Yusuf ya daga waya yakira wani abokinsa police Yana dagawa ya'ce Dan Allah Saif ka turo min mota guda yanzun na
abokina ne bangani ba Kuma naga wayarsa ahannun wani mutum
Ban'garen Saif cewa yayi ba damuwa kana Ina ne katuromin address din gurin gasunan zuwa
Nan ta'ke ya turamai address din gurin
Baifi 20 minutes ba suka isoMutumin Nan abin tausayi yachi kuka har Muryarsa Bata fita idonsa sunyi jawur sun kunbura
Sofiya da mama da kannan ta har rigengen su'ke gurin fitowa suga Abinda ke faruwa Jin motar police akofar gidan su
Abinda suka gani ne ya Basu mamaki
Sofiya kuwa ganin Yusuf yasa'ta k'arasowa Dan Jin Abinda ke faruwa
Yusuf bai 6oye Mata komai ba ya bayyana Mata duk Abinda yasani
Da kyar ta iya cewa babyn nawa??
Meya faru dashi
Da sauri ta je cikin motar ta shak'o wuyan mutumin tana kuka tana cewa wallahi sai ka fitomin da masoyina Ina ka kai min Ibrahim Dina wlh bazan yarda'ba
Da kyar umman. Ta tazo ta kwace ta
"motar na wucewa Yusuf ya hau mashin yabi bayan su
Sofiya kuwa ummah ta'jata suna k'okarin shiga gida umman ta ta'ce Allah yasa ma kashesa sukayi shegen yaro sai bakin na'ci