3

1K 6 1
                                    

*............_KAI MIN HALACCI!_*
      💕

_*NA_*

_*©NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO)_*

®_*HASKE WRITERS ASSO💡_*

       *_SHAFI NA ‘DAYA_*

_بسم الله الرحمن الرحيم_
_In the name of Allah, the Gracious, the Merciful...!_

_D’AN-D’ANO na ZAFAFA BIYAR,daga cikin_
              _*KAI MIN HALACCI!_*
                               💕

“Wai dan girman Allah karatun bokon nan shi za'a tambaye mu a kabarin mu? ahh nace na gama neman ilimin boko dole sai nayi ne? gaskiya ni babu wata *Dabo English academy* d'in da zanje bare na b'atawa kaina lokaci, idan naje guri ban iya turanci ba dan Allah a zageni ko ayi min dariya, ba dai abinda mutum yake ji dashi zai yi amfani ba? toh ayi min turanci sai nayi hausa dan shine yare na.”

“Ni kake yiwa rashin kunya Shamsu? Umma kinji yaron nan ina cewa yayi abu yana cewa ba zai yi ba dan raini, to idan kayi wa zaka yi mawa? Kar Allah yasa kayi kudina ma sun huta kaje kayi duk uban da zaka yi sakarai kawai shashasha.”

Tashi yayi yabar gurin yana k'unk'uni, kawai yaya Garzali yazo ya b'ata masa rai sabida wani buri nashi can, yace baya so ba sai a kyalesa ba ko dole ne, sai kace fita daga addini duk yabi sai yab'a masa magana yake yi harda cewa yayi masa rashin kunya dan sharri...

******

Cikin takun ta na cewa itama fa yanzu 'yan mata ce kuma budurwa, tazo wucewa ta gaban shagon sa, yana zaune akan kujera a k'ofar shagon nasa. Yayin da daga cikin shagon kuma wak'ar *alagidigo* ce take tashi ta cikin speakers hannunsa rike da game yana ta faman yi.

Muryarta kawai ya jiyo kamar yadda ta saba duk lokacin da ta hangoshi a guri ko cikin mutane abokansa ne sai tayi masa waka, tun lokacin da tsautsayi yasa shi furta mata kalmar SO.

Satar kallanta yayi yaga yauma ta cokaro d'aurin d'ankwalin nan nata wato ture kaga tsiya, mayafin nan a kafad'arta ta tsaya dai-dai shagon, kusa da wata mai suyar awara ta rike kugu tana karkad'a jiki bakin nan yasha kanta kile, cunoshi take tana waka.

_''Allah ya tsine wa saurayin kusa da gida, shekaran jiya yazo.., jiya ma yazo..yauma kuma zaizo...!''_

Kamar yayi shiru ya kyaleta kamar kullum idan tayi, amman yau zuciyarsa tana son ramawa dan bai ga dalilin da zai sa k'aramar yarinya dan yace yana sonta ta dinga gasa masa magana a fakaice ba, dan haka shima yana danna game d'in ba tare da ya kalleta ba yace.

_''Allah ya sakawa saurayin kusa da gida, shekaran jiya yakai an k'arb'e.., jiya ma yakai ta karb'e.., yauma kuma zai kai, indai da gaske ne ba'a son 'yar kullum idan ya kai yau kar a karb'a...!''_

Da sauri ta kallesa domin ba tayi tsammanin martani ba daga bakinsa, murgud'a baki tayi tare da bugun cinya da hannunta ta kallesa, shima dai-dai sannan ya d'ago suka had'a ido ta dank'ara masa harara, yayin da shi kuma ya mayar mata da lafiyayyan murmushi, mai awarar ta kalla tana cewa.

“Aikin banza, Sa'ade soya ki bani ta hamsin.” Sa'ade dake zuba awara cikin mai tace,

“Toh.” Shi kuma da yake gefe yana jinsu yace.

“Sa'ade dad'a mata ta wata hamsin d'in, ta d'ari kenan zan biya ki”

Tab'e baki tayi maimakon tayi masa, godiya amman cikin ranta fess domin ko sisi daman babu a gurinta, saboda tasan zai iya biya, shi yasa tace a bata ta hamsin dan ta kare yawa a gabansa, da mamaki ya bita lokacin da aka gama soyawa aka mik'a mata ta karb'e ta juya zata tafi tace.

“A duniya dai akwai wahalallu, Sa'ade Allah ya sa a rage kud'in waken suya(soy beans), kinga kuma kun huta masu saidawa kuma sun kwaso asara.”

“Kai Aliyah Shamsu mafa yana sai dawa kuma a gurinsa nake auna, so kike shima asarar ta same shi bayan kuma gashi ya siya miki awara har ta naira d'ari”

Dariya Aliya tayi tana kuma sauyawa ledar awararta hannu, saboda zafin da d'ayan yayi, sai da ta kalli inda Shamsu yake zaune sannan tace.

“Oho ke wacce kike so a amsa miki a cikin addu'ar tawa? A kara kud'in waken suyar, ko kuma a rage kuma dole ku siya a haka wanne kika fi cewa amin?” Da sauri Sa'ade tace.

'”A'a nafi son a rage amman ai su Shamsu ne zasu yi mugun asara fa Aliya.”Cikin saurin baki Aliya tace.

“Haka nake so ai Sa'ade kinsan wasu a wahale suke duk abinda zaki musu toh ba ganewa zasu yi ba, ni na wuce sai anjima.”

Murmushi Shamsu yayi yana girgiza kai, sosai Aliya take bashi mamaki, gashi yayi-yayi soyayyar da yake yi mata ta fita daga ransa, amman abin ya faskara yarinyar duk tabi ta raina shi, yakan jure duk wani wulak'anci da zata yi masa, sannan yana lodar kayan ‘kwalam da makulashe ya bayar akai mata bata tab'a dawo masa dashi ba, amman duk lokacin da yaje tad'i gurinta bata fitowa haka kuma baya fasa komawa gobe.

****
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_

ZAFAFA BIYAR (DANDANO)Where stories live. Discover now