*ZAFAFA UKU. A K A RUM-BIL-HAƘ*
Faɗakarwa, nishaɗantarwa, ilmantarwa haɗe da wata zazzafar soyayya mai matuƙar tsayawa a ƙahon zuciya duk a cikin ZAFAFA UKU na Rufaida Umar, Bingel Mita, Fareeda Abdallah.
Me kike jira ƴar uwa ana ta yi ba da ke ba? ki biya ƴan kuɗinki ƙalilan ta wannan acc ɗin ki karanta hankalinki a kwance ba tare da kin jira na Allah ya isa ba😂👌🏽👌🏽.
0452523875 Rufaida Umar, gt bank. Littafai uku 700, biyu 500, daya 300.*ƊANƊANI HAUKACI*
BILHAƘƘI
Ɗan miƙewa tayi daga kishingiɗar da tayi ta kalli Jakadiya da jajayen idanunta.
"Ya ake ciki Jakadiya? an dace?""Ƙwarai kuwa ranki ya daɗe. Ba dolenshi ya amsa kiran uwar kowa ba? Ai umarni ne. Ko da ranshi baya so dole ya amsa kira. Yanzu haka yana cikin ɗakina yana jiran umarninki."
Jakadiya ta ƙarasa maganar cikin ƙasa-ƙasa da murya."A shigo da shi cikin sirri"
Ta faɗa a hankali cikin ƙasaita.Minti goma tsakani Jakadiya ta shigo da wata mace mai girman jiki da suffar samudawa. Ta sa wasu tsofaffin kaya riga da zani da suka koɗe sosai alamun sun gama cin duniya, fuskarta kaca-kaca da kwalliyar ƴan ƙauye.
Ganin bata nan a falon yasa suka nufi cikin turakarta kai tsaye.
Suna shiga cikin ɗakin Jakadiya ta maida babbar ƙofar ta datse da makulli, ko da ta waigo sai taga wannan matar har ta tuɓe kayan matan da yake jikinta sai ga sangamemen gardi ya baiyana.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya baje kayan aikinsa a tsakar ɗakin, ya kalli Fulani da idanunsa masu barazanar tsorata ƙaramin yaro.
"Bani hannuwanki"
Ya faɗa cikin tsawa yana gwalalo mata idanu.A tsorace ta kalli Jakadiya ita kuma ta ɗaga mata kai alamar ƙarfafa gwiwa.
Jikinta na rawa ta miƙa mishi hannuwanta da suka sha zabban gwal da awarwarayen gwal shi kuma ya kama ya riƙe gam! Ya janyo ta da ƙarfi tayi taga-taga kamar zata faɗa masa jiki amma ta cije ta tsaya daf da shi.
"Rufe idanunki"
Ya sake faɗa cikin masifa.Tana runtsewa ya fara wasu irin surutai yana zagaye kayan tsafe-tsafensa da ita tana binshi a tsorace kamar raƙumi da akala idanunta a gimtse.
"Naga tsananin haske a tare da ke. Burikanki zasu cika. Mulki na duniya zaki same ta ke da zuri'arki. Amma kina da babban ƙalubale, na ga wata zazzafar tauraruwa mai wutsiya da za ta baiyana a cikin haskenki. Muddin kika bari ta baiyana za ta tarwatsaki, za ki wulaƙanta, asirinki zai tonu, duk mugayen abubuwan da kika daɗe kina aikatawa zasu baiyana, za ki yi mummunar ƙarshe a masarautar nan"
Yana gama faɗin haka ya angije ta baya kamar zata kifa da mugun sauri Jakadiya ta tallafe ta, ta haɗa zufa tayi sharkaf kamar wacce tayi gudun famfalaƙi.
"Ta ya zan gane tauraruwar?"
Ta tambaye shi a tsorace."Duk sadda ta baiyana zaki ji alamun ita ce a jikinki, amma shawarar da zan baki ki fara nemanta tun kafin ita ta shigo yankin da kike, muddin kika bari ta shigo sai kinyi da gaske sannan zaki ci ta da yaƙi."
Daga haka bai sake ce mata komai ba ya fara harhaɗa kayayyakin aikinsa a cikin jakar da ya ratayo a kafaɗa.Sulallan gwal masu yawan gaske ta sallame shi da su zuciyarta cike da matsanancin farinciki.
Ya maida kayan matan jikinsa suka fice shi da Jakadiya Babba ba tare da ya bata ko tsinke tayi amfani da shi a matsayin magani ba.
HAƘABIYYA (Tsiya da wasali)
Acan cikin wani ɗaki da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar wani baƙin daji dake yamma da wata kushewa. Wata ƙwarya ce da ke cike da wani baƙin jini ta fara girgiza tana darewa, jinin cikinta ya fara toroƙo yana zaɓalɓala tamkar yana bisa garwashi, kafin kuma ta tarwatse gabaɗaya jinin ya fallatsa a ilahirin farin mayanin da aka kewaye ɗakin da shi, a sannan ne Ragon ya bayyana yana kuka, sai kuma ya yi tsit! Yana tsurawa mutumin da ke zaune acan kursuwar ɗakin kan wata baƙar kujera ido, a hankali kuma ya durƙushe a gurin yana kafa ƙahonsa a ƙasa tamkar wanda ya yi tozali da manyan dawa.
Mutumin da yake dattijo baƙi, mummuna na haƙiƙa ya miƙe tsaye hannunsa dafe da wata baƙar sanda da aka sassaƙa mariƙinta da siffar kan mujiya. Ya taka a hankali zuwa gaban ragon ya ja ya tsaya idanuwansa a rufe. Ya buɗe baki ya fara furta wasu irin kalmomi yana kiran wani suna, ba daɗewa wanda yake kiran ya bayyana a gabansa ta cikin wani duhu, a sannan ne ya yi shiru ya buɗe idanuwansa yana kallonsa.
"Abinda muke aikinsa sama da shekaru ne ka turo mana Rago a madadinsa?"
"Ayi haƙuri kuskure ne..."
"Ba ma aiki da kuskure...!"
Ya furta da tsawa har sai da mutumin ya ja baya.
"...Da wannan kuskuren naka za ka rasa abinda ka fi so a duka rayuwarka, kar ka manta numfashinta tamkar kwan jimina yake a hannuna, a kowane lokacin da na tunzura zan iya sakinsa ya tarwatse a gaban idanuwanka. Na baka mako guda da ka kawo mini wannan yarinyar tunda har ta riga da ta taɓa wannan ƙyallen, idan ka kuskure hakan ka fi kowa sanin irin jinyar da zan iya saukar mata da sunanka!"
"Zan kawo ta ko gobe ka ce, amma a ɗan daɗa ba ni lokaci na ƙarshe, a kuma duba wannan alfarmar da na nema, a duba darajar addinina tunda an umarci na nemi wani 'yancin... Zan kawo ta cikin biyayya da dukkan abinda kake so."
Dattijon ya juya ba tare da ya ce masa uffan ba ya koma kujerarsa ya zauna ya rufe idanuwansa. Sai can ya ɗaga masa hannu alamun ya tafi ya gama magana da shi.RUMFAR KARA
Da wani irin murmushi take takowa zuwa falon, cover shoe dinta sai kwas-kwas yake yi saman tiles dake malale a falon. Tunda ta taho yake kallonta yana mai ci gaba da busa tabar Marlboro a hankali hayaƙin ke fita ta baki da hancinsa. Hannu ya miƙamata, ba musu ta ɗora hannunta saman nashi ya ja ta gefensa ta zauna. Hannu ta sanya itama ta karɓi tabar ta zuƙa gami da busarwa. Yana murmushi har lokacin yana dubanta gami da shafar gashinsa da ya sha style din Afro.
"Salma, ba kya tsufa. Kamar ba ke kika haifi Fu'ad ba."
Ta yi mai farr da idanu.
"Kaima ai ba tsufan kake ba, wa zai ce ka haifi waɗannan yaran."
Ya ɗan tsuke fuska.
"Kin ganki ko za ki ɓatamin annashuwa."
Dariya ta yi sosai.
Ya dan rungumota jikinsa.
"Ato, ai gaskiya ne, kinga hankalina a kwance yake yanzu, bana fargabar komai tunda muka ƙare da babin Matar can. Yanzu tunani ya tafi kan bude babban asibitin da zamu yi a Abuja tare da Alex, sati na sama zamu tashi zuwa Singapore don odar kayayyaki. Kinga ke da ɗanki za ku rigani tafiya."
Ta yi murmushi.
"Hakane, Allah dai Ya bamu nasara akan su."
"Ameen. Ina Fu'ad din?"
Kafin ta kai ga magana ya shigo, yaro ne dan shekaru goma sha biyu cif a duniya. Fari ne ƙal, yana da suma irin ta fulanin asali. Yana da ƙiba daidai misali. Wannan karon fuskarsa cike take da fara'a babu ko digon damuwa tattare da shi.
"Fu'ad." Juyowa ya yi ya dubi Mahaifiyartasa, da murmushi ya karasa bai ko kalli gefen da Hayat yake ba, nazarin yaron yake sosai da tunani iri-iri a ƙasan ransa.
"Mum, kinsan wani abu kuwa?"
Kai ta girgiza.
"No my son, sai ka faɗa." Kallon gefen da Hayat yake ya yi sai kuma ya ɗan yi kicin-kicin da fuska. Sarai sun fahimci manufarsa, wato dai ba zai fadi a gabansa ba. Ganin haka Hayat ya mike fuska a daure ya dubi Salma.
"Dole a ce da mijin iya Baba, komai daren dadewa kin sani, na sani, gaskiya za ta yi halinta." Ya yi maganar a fusace, bai ƙara cewa uffan ba ya kada kai ya fice daga gidan.
Salma wacce har zufa ta soma ta yi saurin kashe tabar cikin ashtray. Daidai sadda Fu'ad ya jefomata tambaya.
"Mum, me yake nufi? Wace gaskiya?"
Kai ta girgiza.
"Ba komai, gaskiya dama koyaushe a bayyane take. Ka rabu da zancensa."
Ya taɓe baki.
"I hate him, Mum meyasa kika aureshi?"
YOU ARE READING
BILHAƘƘI
HorrorWani dunƙulallen duhu ne ya tokare hasken da ya kamata ta gani a cikin rayuwarta, a taƙaice dai wani ɓoyayyen sirri ne. Duk abinda ta ce zai faru tabbas sai ya faru komai muninsa. Mutum ce ko aljana?