SALON TASU SOYAYYAR

106 2 0
                                    

Numan Gari ne da ubangiji ya ba su albarka kala-kala wadda ta haɗa da ƙasar noma da kuma gurin kiwo mai Yalwa .
Mazauna Garin fulani ne wadanda suke tashi duk shekara domin su je kiwon dabbobin su ya yin da ƙalilan daga cikinsu sune ke zama a gida .
Gari ne da ke dauke da rukuni ɓangare biyu wato ɓangaren musulmai da kirista wanda duk da Bambancin addinin bai saka su ƙyamatar yan uwansu ba kuma bai saka tashin hankali a tsakaninsu ba .
Hakan ya samu ne sakamakon samun adalin shugaba da suka yi wanda bai nuna wariya tsakanin Musulmai da kirista duk da kasancewarsa musulmi kuma Babban Malamin addinin Musulunci da ake ji da shi a Gaba daya ƙasar .
Sheikh Dr. Ƙasim Aglah Sa'ad Buba Yero .
Dattijon Malami ne mai tsananin kamala da cikar haiba wanda kana kallonsa zaka tabbatar da usulin ƙabilarsa ta Bafulatani duk da shekarunsa sun ja a duniya amma ba kowa zai shaida haka ɗin ba .
Yana da Matan Aure Guda Huɗu saboda kasancewarsa Malami kuma Masarauci .
Uwar Gidansa Hajiya Iyami tana da Yaya Takwas  Danta na farko Prof. Sagir Ƙasim Aglah Sa'ad Buba Yero wanda shine shugaban Kungiyar Jami'o'i na Ƙasa NUC sai sauran Masu Bi mashi , Dr. Fulani Ƙasim Aglah Sa'ad Buba Yero wadda take zaune a ƙasar America tare da Mijinta da Ƴaƴanta , Hon Umar Ƙasim Aglah Sa'ad Buba Yero Shine Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa kuma wanda ake tunanin maye gurbin Gwamnan da shi , Barr. Fatima Ƙasim Aglah Sa'ad Buba Yero ita kuma Barrister ce a High Court tana auren Accountant General na ƙasa .
Justice AnsarulDini Ƙasim Aglah Sa'ad Buba Yero shi ɗin Babban Alƙali ne a Kotun Daukaka Ƙara ta Adamawa .
sai na karshe Tagwayenta Hassan Da Hussaina wadanda suke Karatun Masters dinsu a kasar Lebanon .
Tabiyun kuma basu taɓa samun Haihuwa da shi ba sai ta ukun da suke da Yaya biyu Engrn Ƙamaruddini Ƙasim Aglah Sa'ad wanda yana da kamfanonin kwangila  da Mariya Ƙasim Aglah Sa'ad  Ita ke auren Senator din Adamawa North  .
Ta hudun kuma Ita ce Amaryarsa Ƴaƴanta Hudu
sune Miss Maryam Ƙasim  Aglah  Sa'ad Ita Ce Chief OF Staff ta Ma'aikatan Shugaban Kasa .
Sai Captain Fu'ad Ƙasim Aglah Sa'ad wanda shi matukin Jirgin Sama ne .
Da SP. Mahfouz  Ƙasim Aglah Sa'ad wanda shi Dansanda ne .

Autansu kuma wanda Gaba ɗaya Labarin akanshi yake shine
Sa'ad Ƙasim Aglah Sa'ad ( Yariman Numan ) Kuma Majidaɗin Lamiɗon Adamawa .

Sakamakon Lamiɗon Adamawa da Sheikh Dr Ƙasim Aglah Sa'ad wa da ƙani ne , Bayan rasuwar Aglah Sa'ad Buba Yero sai aka dora Babban dansa Gen.  Abubakar Aglah Sa'ad Buba Yero Sabon Lamiɗon Adamawa shi kuma Sheikh Ƙasim aka bashi Hakimcin Numan .
A duniya babu wanda suka ɗora wa so irin mai sunan Baffansu ba iya su ba har kafatanin ragowar yan uwan shi .

MS Kutama
07044122219

Zan Ci gaba ranar Monday.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 19, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAHAMAGEWhere stories live. Discover now