💫⭐ *SHINING STARS WRITER’S ASSOCIATION*💫⭐
{'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our reader’s'''✍🏻}
🧕 *DARAJAR MAHAIFIYAR SA*🧕
*NA*
*FIRDAUSI FAROoQ HYDAER*
_Bismillhir Rahmanir rahim_
~More comments~
~More typing~🅿5⃣➡6⃣
Ba zaki zuba min abincin bane? Yace cikin wata kalar muryar da tunda nake dashi bai ta6a mun magana da irin ta ba...
Har da zance da ni ke zuba maka? Sai kuma wata zuciyar ta gargade ni da kinyin hakan,mik'ewa nayi na nufesa zuciyata cike da tsoronsa dan maganar gsky ina matukar tsoron yaya Mujaheed...
Hannuna na rawa na zuba masa jallop din shinkafa da wake wanda yaji ishasshen ganyen albasa da kuma ganyen alaiyyahu...ina gamá zuba masa na mik'e zan tafi,ga mamakina sai ji kawai nayi yace, “ina kuma zaki je?”
“D'aki..” na bashi amsa atakaice....hmmm yayi murmushi sannan ya ture plate din abinci yace, “Zauna za muyi magana..” banyi musu ba na zauna tare da tank'washe qafafuna “haba Maryam yanzu dan Allah haushiná kike ji? To idan haushi kikeji Allah ubangiji ya baki hak'uri kinji...” yace tare da dafa kafad'ana ya kuma d'ago fuskata sama yana kallo..
Murmushi nayi tare da cewa “ni baka mun Komai ba yaya..” na ce ahankali....
Dan agaskiya yanzu ina matukar kaunar yaya duk da cewa da kam bana sonshi,bana kuma kaunar shi amma yanzu kam ina masifar sonshi shiyasa kO me yake mun bana iya ganin laifinsa...
In takaice muku awannan lkcn muka shirya ni da mijina dama masu iya magana sunce mata da miji sae Allah dan hatta abinci ma tare muka ci dashi duk da cewa ba musa ba ci tare bá.......*ASALIN LABARI*
Kamar yanda kuka ji sunana Maryam Sulaiman Ibrahim,haifaffiyar garin Bauchi ce ni unguwar fadamar mada...
Iyayena sun rasu tun ina da shekaru uku wato atakaice dai tun ina k'arama agidan yayar Mahaifiyata na tashi sbd yan uwan mahaifina duk ba wasu masu karfi bane kuma sun k'i karb'ata,mahaifiyar kuwa bayan rasuwar mahaifina da sati uku itama Allah yayi mata cikawa sakamakon ciwon cikin da ya turnik'eta cikin dare....
Sunanan yayar mahaifiyata Maryam dan lkcn da aka haifeni wa ita mahaifina yayiwa takwara sbd halalcinta agareshi shi da mahaifiyarta...
Maryam{Umma} tana matukar sona sosai dan har tafi nuna min so akan 'ya'yanta tana da yara biyu yaya Mujaheeed da kuma Anty Khadija su biyu ta haifa itama mijinta ya rasu tun da jimawa babban d'anta ke d'aukan duk wani nauyi na mu yaya Mujaheeed kenan
Yaya Mujaheeed yayi karatun boko mai zurfi dan har bautan k'asa ma yaje yayi a garin Jos aiki ne kawai bai samu ba sakamakon yanayin k'asar tamu komai d'An alfarma ne sai ka ga mai catifiket din firamare na aiki amma mai kwalin digree da diploma kai har masters bai samu ba dan ba su da mai yi musu hanya {Allah ya kyauta} sbd haka yaya bai takurawa kansa ba tunda yajejje neman aikin bai samu ba sai kuma ya cigaba da yin sana'ar dinkin{tela] sosai yake samu ta wannan sana,ar tashi dan sosae ya iya cire dinkuna na gani na fad'a...
Anty Khadeeja kuwa tayi aurenta a garin kano yanzu haka yaranta uku Basma,da Bassam sai kuma Aslam
Daga makarantar sakandiri na tsaya da karatu dan ba ni da burin yin wani karatun boko mai tsanani nafison na addini duk da dae shi din ma nayi sauka sau biyu hadda da taktil na kuma haddace wasu littafai kar su Hadisi da sauransu had'a bak'i ma na iya shi sosai dan ni ce ma mai yi ma yaran mak'otar mu k'ari da kuma asignment idan an basu a schoolTun tasowata agidan Umma na tsani yaya Mujaheeed dan kwata² ba shi da sakin fuska ga shiga abinda bai shafe shi ba dan zan iya cewa shi ma hakan take agare shi sbd ina yawan lura dashi idan ina waje baya son zama awajen idan kuma Umma ta siya mun zani ta bashi ya d'inka mun sai ya k'i ko kuma ya je ya bai wa yaran shagonsa su d'inka dan acewarsa baya dinki wak'ana nun yara...
YOU ARE READING
DARAJAR MAHAIFIYAR SA
Short StoryLbrn wata yarinya mai suna maryam da mijinta kuma yayanta majaheed,sai kuma lbrn wasu maaurata masu rigima akan zuwa aiki shi yace tabar zuwa aiki ita kuma ta ki.... ku biyo Feeby zakuji komai...👌❤