page_5

36 2 0
                                    

*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION* 

'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45&ref=bookmarks

*DARAJAR MAHAIFIYAR SA* 🌸🌸

*NA*

*FIRDAUSI FAROOQ HYDAER*

'''FOLLOW ME ON WATTPAD'''
*@FirdausiFarooq*

'''my facebook username'''
*Firdausi farooq hydaer*

*page~15to16*

Ta dauki lokaci sosai acikin toilet din, sannan tafito daure da towel akirji, harara ta balla masa sannan ta wuce jikin mirorr ta fara shafa mayuka ajikinta…….
Tsaki Ahmad yayi ahankali sannan ya fice daga cikin d'akin ransa amatukar 6ace, itama tsakin tayi sannan tace "kayi, ka 6uge amma wlh bazan ajiye aikina akaron banza ba Allah, sai dai idan zamu rabu aikin banza aikin hofi mtsss…….. !

★★★★★★★★☆☆☆☆☆☆★★★★★☆
Washegari  kuwa da wuri Aisha ta mike tayi shirinta kamar kullum ta fita aiki abinta ko takan Ahmad ba ta bi ba tayi tafiyarta…….

*MARYAM*

a bangaren maryam kuwa kwana tayi da zazza6i.
Salatin da naji umma nayi ne yasanyani farkawa daga barcin da ya d'an daukeni…….
"Yanzu Shi Mujaheed d'in yana ina ne Auwal? Umma ta tambaya cikin rawan murya "ki kwantar da hankalinki umma muna tare dashi, kuma ba wani mummunan raunika ya jiba…. " ya auwal yace mata cikin sanyin murya dan yace mata hakane dan ya kwantar mata da hankali. "Shikenan amma ya kamata ka fad'a mun yanzu na zo? Ba yanda ya auwal ya iya haka ya sanar mata sunan asibitin da aka kwantar da Mujaheed d'in……..
Me yafaru umma? Na tambaya ina kallon umma dake faman share zufa da ha6an zaninta.. "Ki tashi ki karya, Mujaheed ne yayi accident yanzu haka yana asibitin T.H bari na shirya sai naje na ga yanayin jikin nasa…. "Ba ri na tashi muje umma dan bazan iya zama ba, zan ta tunanin shine… nace ahankali ke da baki da lfy kuma ? Ki zauna agida kawai ni zan fara zuwa na dubo sa… toh shikenan bari na yi sauri na yi wanka kan na fito sai kiyi ki shirya kinji ko? "Daga mata kai kawai nayi sannan na mike Ita kuma ta shige band'aki…......... .


Share pls

DARAJAR MAHAIFIYAR SAWhere stories live. Discover now