❤💛💔💛❤💛
❤💛❤
✨✨✨*RIKICIN MASOYA*
*(Masoyan gaskiya)*❤💛💔💛❤💛
❤💛❤
✨✨✨*WRITTEN BY: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL(UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR:*
*SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI**AND NOW*
*RIKICIN MASOYA**DEDICATED TO:ATK PLACE GROUP*
*SPECIAL GIFT TO:YAN BIYU KYAUTAR ALLAH HASSAN ATK & HUSSAIN 80K BANI DA BAKIN MAKU GODIYA SAI DAI NA CE Allah ya bar zumunci ya had'aku da mata na gari.
________________________________
*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*✨✨ page 5⃣
Wani irin tsananin farin ciki ta ke ji marar misaltuwa, ta na jin nishad'i sosai a ranta, a haka barci b'arawo ya yi awon gaba da ita cike da mafarkinsa.
****************** Asim kuwa bin wayar ya yi da kallo baki a sake da yaga ta katse kiran "Meyasa ta katsen waya? Ko dai bata amince mun bane?" Yayi tambayar acikin ransa.Ras! Ras!! K'irjinsa ya buga da ƙarfi, haka kawai ya ji hankalinsa ya k'i kwanciya, hakan yasa ya kuma kira sai dai har sau biyu yana kira bata daga ba.
Cike da fargaba ya kashe wayar gaba ɗaya ya Haye Kan gadonsa ya kwanta,amma ya kasa barci baya jin zai iya kuma yin barci ba tare da yasan matsayinsa a gunta ba, ganin ya kasa barci har ukun dare ya saka ya sauko daga bed d'in ya je ya d'oro Alwala ya fara jera nafilfili.
Bayan ya kamallah ya shiga jero addu'oi ya na roƙon mahaliccin bayi da ya azurta shi da samun Sabreen ya kuma sanya alkhairi acikin haɗin, ya dau tsawon lokaci ya na addu'oinsa kafin ya shafa ya tashi ya ninke sallayar tare da haye gado ya kwanta.
********************Washe gari Asim ya ji saussaucin damuwar dake ransa da safe ma ya kuma gwada wayar Sabreen amma har sau biyar bata d'aga ba, hakan ya sa hankalinsa ya tashi matuƙa ya kira Ashik cike da k'aryewar zuciya ya sanar masa abinda ke faruwa.
Lallashinsa Ashik ya shiga yi tare da ƙara masa gwarin gwuiwa akan ya cigaba da nemanta a waya kada ya sare insha'allah komai zai dai-daita.
Ya ji daɗin maganganun da Ashik ɗin ya gayamasa shiyasa ya ke matuƙar son Ashik kuma ba yada wani amini tamkarsa.
Saboda haka ya cire duk wata fargaba a ransa, ya ci gaba da renon soyayyarta a zuciyarsa.
*****************Bangaren Sabreen kuwa ta na kitchen su na shirya break fast ita da Nasreen amma tunaninsa ne cike a ƙwaƙwalwarta, aranta take addu'ar Allah ya sa ya kuma kira za ta ajiye jan aji ta karb'a masa buƙatarsa tun da ya yi dai-dai da nata ra'ayin.
"Kai ba zan iya jira har ya kuma kira ba ina kammala aikin nan zan je na kira shi,ai ko yanzu Alhamdulillah ya san shi ya fara kirana bazai zargi komai ba." Ta faɗa a ranta.
Bayan wani lokaci su ka kammala komai, Sabreen ta kalli Nasreen ta ce "K'anwata ki kwashi kayan abinci ki kai parlour ki haɗa komai da komai,zan shiga d'aki ina zuwa."
"To yaya." Nasreen ta faɗa.
Wucewa ta yi zuwa ɗakinsu cike da zumud'i don ba zata iya jira har su kammala shirya komai ba.
YOU ARE READING
RIKICIN MASOYA
Fantasíalabari ne na wasu masoya Masu matukar k'aunar junansu duk da yawan Rikici da rashin fahimtar juna da ke tsakanin su.