5-10

1.4K 64 2
                                    

  ABLA 💞

By Rasheedah Dalha

   Bayan sallar azahar ya fito tare da bayin sa, ya sake sauya wasu kayan cike da issa yake tafiya har ya kai part din sokoto,yana zuwa aka nema mishi izini
   daman ita da adam ne aciki wani bakin cikine yaka mata data tuna abinda yayi mata da safe amma yata iya haka tace ya shigo.

   Yana kaiwa kofar dakin ransa neh yasoma baci kawai ya juya a harzuke ya nufi motarsa. Hadaddiyar mota an rubuta murad 06 a plate number ko jiran drivern sa beyi ba ya shige ya taka wuta a fusace ya fita.
    Yana tuki yaji wayan sa na kara daga wa yayi ya kara a kunne, abokinsa ne Faruk yace man kwata2 baka leka mu yau ba lfy kuwa?
   Murad yace lafiya ta lau ganinan shigowa ma faruk yace amma fah daga jin muryan ka an tabo maza,
   Murad yace zaka fara surutun koh faruk yace toh shikenan na bari kawai sai ka iso.
  Ya sauke wayar tare da firzo da iska daga bakin sa.
   Bayan yan mintuna sai gashi a Al-Hussain Murad General Hospital parking yayi yana tafiyan sa daya saba feeling free without fadawan sa danshi ya tsani yana tafiya suna wani binshi.

     Jiddah na tsaye  da flask da bag abla dake magana da nurse ta dawo tace jiddah bani flask din mutafi wards dake ta entrance, can aka mai dasu, jiddarh tace toh muje.
  abla ta amshi flask din ta juya ta fara tafiya jiddah na biye da ita.

   _____Yana tafiya neh gaba daya hankalin shi ba'a kan hanyar yake bah kawai yaji ya tungude abu cike da masifa zai fara magana yaji saukan taliya mai zafi a jikin sa, ba karamin daurewa yayi gurin ganin bai saki kara ba
   A fusace ya shako hannu ta cikin fada da tsawa yana zare ido yace keh are you blind.
  Itama cikin jin haushin ya zubar mata da abinci ga hijabin ta duk ta baci tace mallam dallah sakeni, jibi fah asaran da kamin maimakon ka bani hakuri sai ka hauni da fada.
      tsawa ya daka mata keeehh!! Zaki ban hakuri koh saina tattakaki, sai a sannan ya kare ma fuskan ta kallo, farace sosai tana da ido manya2 ka kuma eyelashes dogaye bakinta karami pure pink abinshi,
   haushinta daya ke ji ta rufe mai idanu shi baiga hakan ba.
   Da duk karfinta ta Kwace kanta tace hallan kai makaho ne ko kuwa... baka ga asaran da kamin bane zaka ce in baka hakuri
   Kalamanta sun konamai rai hannu yasa yadan sosa giran shi tare da fuzar da iska mai zafi daga bakin shi... wai makaho... cikin bacin rai ya daga hannu zai kai mata mari yaga ashe mutane sun taru suna kallon su ransa neh ya kara baci wai ni murad neh nake fadin magana yarinyar nan na fada lallai sai na koya maki hankali zaki san ni kika tozarta gaban jama'a duk maganan zuci yake yi..

    Tureta yayi ta fadi ya wuce tare da bige kafafafun ta.
   Hakan ya matukar kona mata rai, jiddah dake tsaye kaman an dasata tunda suka fara kasa magana tayi don ya mata kwarjini ta matso tadaga ta tana mamakin karfin halinta.

    Bag din abla taja tayi gaba saboda yadda mutane ke kallon ta ga hijabin ta duk ta baci,
   daukar flask din jiddah tayi ta bi bayanta.
   Koda suka zo daki abba na bacci mama taje siyan magani umma da safna ne kadai.
  Batace masu komai ba ta ajiye jakanta ta wuce waje jiddah ko ta gaishe su umma ta dauki flask din ta wuce gida don yin wani girkin don tasan abla bazata kula taba yanzu.
   Umma dai magana ma kasayi tayi saboda jikin abba ne agaban ta tasan dai bai wuce abla tayi barin abincin a asibitin ba duba da yadda hijabin ta ya lalace
   Kasan wani bishiya ta samu ba kowa taci gaba da kukan bakin cikin data kunshe.
   Office din MD (medical director) naga ya wuce, ashe office din shi kenan,
   zama yayi akan kujera ransa na kuna da karfi yace NO, wallahi sai kin bani hakuri ,
   waya yayi yace a kawo mashi coffee yasha koh zai calm down ya fito gida ransa bace nan ma ansake bata masa.
    Bayan mintuna biyar kansa kife kan desk Dr faruk ya shigo yana fadin kaifa dan iska ne haka mukayi da kai kace zaka shigo office dina amma shiru badan naga motarka bafa. Murad banza ya mishi ko yasan yanayi..
   Faruk ya sake cewa ina maka magana kamin shiru kodae sarautan ne yatashi besides naji ana dan surutai a hospital din nan mai yafaru neh
    sai a nan murad ya dago kai yace magana kuma, furuk yace daman kana ji na ka kyaleni murad yace yarinyar nan ta gama dani wallahi amma ba komai wani malalacin murmushi ya saki wanda ba karamin kyau ta mishi ba yana fadin zata gane kuranta ne. furuk yace yarima kai kuma dawa yace some crazy girl.
    nan ya labarta ma faruk abinda ya faru, faruk yace kadai bi a sannu, murad yace wallahi saita ban hakuri na lura tana da girman kai da gani ita ba yar kowa bace aman sai shegen fisara faruk yace kace dai halin ku daya da sauri yace Allah ma ya sauwake, faruk yace zan so in ganta kuwa murad yace kai kasani nikam dolene ma musake haduwa dan sai ta bani hakuri wallahi.
   faruk ya tsuntsire da dariya yace is that all, anya ba zuciyar ka ta sace bah,wani mugun harara murad ya maka mishi yana cewa you know me too well mata basa gaba na kuma ma in rasa wanda zan so sai wannan tsiyar din.
     dariya faruk ya sakeyi yace kai yarima anya kuwa. murad ya kalle shi yace malam inkagaji don kanka zaka bari.
   Wata mata tashigo da coffee faruk ma yace a kawo mashi still bai bar tsokanan yarima ba.

ABLA 💞Where stories live. Discover now