Page 1

573 58 17
                                    

GIMBIYA SAILUBA

Free page 1

Salamu alaikum My beloved Readers,da fatan kowa yana lafiya?Ya mukaji da wannan rashin zaman lafiya da kasar mu take ciki?Allah ubangiji ya kawo masa saukin sa ya bamu zaman lafiya ya kuma tsare mu da yan uwanmu Amin.

Kamar yarda nayi muku Alkawarin fara rubuta wani sabon labarin,nace ku zuba  acikin labarin zamani ko kuma na DA na tarihi.toh Alhamdulillah dayawan ku kunce nayi muku na tarihi.
  Gani nan nazo muku da Labarin Gimbiya Sailuba ina fatan zaku so shi duk da idai kunsan yarda al'amarin yake idan ance lbr Fiction ne kirkirar shi akeyi kawai dan nishadi da kuma ilimantarwa.

Page 1
**************************************

"Shekaru dari biyu da sha biyu da suka gabata a yankin arewacin nageriya ta gabas..

Gidane irin na Da din nan na gargajiya sosai yasha zane da tambari irin na arewa a jikin bangonsa,ga kuma doguwar katanga da ta ke're ainihin ginin gidan kai kace gidan wani basarake ne saboda girma da kuma tsari irin nasa.

Jama'a ne suka taru dayawa a gaban wannan gidan duk sun sha manyan kaya da tazarce da gani dai kamar daurin aure ne akeyi duba da irin farin cikin dake bayyane akan fuskokinsu.
  Da sauri na kutsa kai cikin  wadan nan mutanen nan dan kawai na samu kwaso wa masu karatu labari da dumi dumin sa..

"UBALE ya kalli mutumin dake gefen nasa ,dogo ne kyakkyawa dashi me cike da zati da kira irin ta karfafan maza yana sanye ne da babbar riga data sha aikin surfani mai tsadar gaske,fuskarsa na dauke da annuri marar misaltuwa..

Ubale ya nisa sosai yace da murya mai raunin gaske...
SULAIMANU kana ganin babu wani kuskure a cikin wannan al'amarin da muke shirin aikatawa kuwa?
Ka duba fa ka gani wadan nan yaran sunyi kankanta dayawa ace mun daura musu aure tun wannan lkcn..

Ya sake jan lumfashi  mai dumi yana gyara tsayuwar sa..yace....
Yarinyar nan duka duka shekarunta takwas da haihuwa fa,a watan gobe ne ma muke saka ran cikewar ta shekara tara..
shi kuwa wannan yaron na wajenka bazai wuce shekara goma sha biyu zuwa sha daya ba idan har banyi karya ba..
    SULAIMANU ya jinjinar dakan sa yana zubawa ubale wadan nan manyan idanuwan nasa masu ban tsoro da kuma nuna rashin tausayi da rashin ko in kula..
Kai ubale! Ya ka tse sa!..
Wai ba a gaban ka bane ba wannan mai Duba(malamin tsibbo)yake ce dani  idan har ban daurawa Da'na aure da diyarka ba a cikin kwanakin nan biyu ba toh lalle bazan samu MULKIN MASARAUTAR SHIMLA ba..
Kai shedane akan yarda nake mafarkin amshe mulkin nan daga wajen dan uwana Sarki Naziru akan kan mulki a yanzu.
Ya ja lumfashi yana dafa ubale cike da kasaita da kuma mulki..
Kai ma kanka ai wannan karuwa ce tazo maka ko?
Kuma  bawai nace lalle lalle bane se yarinyar nan da yaron nan sunyi zaman auren nasu a yanzu ba,ko ni ai na san sunyi kankantar tunda ba jahili nake ba!..
Zata dai  ci gaba da zama dakai ne har sai takai munzalin zama budurwa...
Kuma..ya daga kafada cike da jiji da kai da kuma tunkaho nasa...
Yace....
Ni SULAIMANU jikan marigayi sarki na shidda Zailani dan sambo nayi maka alkawarin dawo wa  nan da shekaru goma dan na sake shafa wata fatihar na dauki surukata mu tafi Masarautar Shimla.yana fadin hakan ya washe baki yana daga kafata,
   Ubale ya nisa sosai yana wani tunani a cikin zuciyarsa..
Tabbas Gskyr sulaimanu ne kam,sune zasu karu da wannan aure ba kowa ba..
tunda dai har suka samu diyarsu ta kasance mace ta farko da yaron SULAIMANU za ya aura,sannan kuma yarima mai jiran kujerar gado idan har ubansa yayi nasarar samun mulkin da yake kwadayi.
Tabbas dolene ya amince da wannan auren dan kuwa diyar sa watarana GIMBIYA zata zamo..
Ya wangale baki a take yayin da wannnan tunanin ya fado masa..
Sai wani  gyada kai yakeyi yana jin zuciyarsa cike da tsantsar gamsuwa da farin ciki sosai..
Bai sake wani tunanin ba kawai yace..
Naji kuma na amince..
SULAIMANU ya washe baki  shima yana rungume ubale cike da farin ciki marar misaltuwa,dan kuwa babban burin sa yana daf da cika...
Zauren gidan nasa ne suka karasa ciki a tare ko wannen su na dauke da fara'arsa..
Ubale ne ya sake lekowa  wajen yana cewa jama'ar dake waje su karaso ciki yanzun nan dan za'a daura auren...

Gimbiya sailuba Where stories live. Discover now