Page 1&2

1.1K 72 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_story/written by_
_jiddah S mapi_

_Follow me on wattpad_ jiddahpretty

Hi guys this is my first story hope I will have your maximum  co-op ration ❤️

*NOTE:* Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba, labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai.

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 1&2

"Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba,  kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba.

Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas,  sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa  "Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?" Yaƙare maganar cikin sanyin murya.

Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa.
"Addu'a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci."

"Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata,  rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai,
na wulaƙantata,  na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah?  Ina zanji labarinta?  tana raye ko Tana mace?" Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa.
"Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita,  idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!"  Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka.

Awannan lokacin har Habeeb ba'a barshi abaya ba,  duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi.
*** ***

"Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota."

"Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba."  Naji wata siririyar murya Tana fada.

"Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu." Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa.

"Okay nama dauka ae ganinan." Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta.

"Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?" Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take.

Nan naga Beentu na  sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa.  Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami,   ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta.

Cewa tayi "Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?"

"Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min" Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta.

"Okay to muje" Cewar Beentu.

A tare suka fito daga   falon suna sauri.

_see me next page_

✍️🏻 *Jidderh S Mapi*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 01, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A GIDANMU TAKE!!! Where stories live. Discover now