🌀 *GIRMAN ƘAUYE...!* 🌀
NA
*_HAFSAT A GARKUWA_*
~(Mummyn Seeyama)~*Wattpad* ='''Hayfaluv'''😉
🎆
*_Al'Umma Writer's Asso....✍🏻_**بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ*
_Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai._
*_Ya Allah ka bani ikon faɗar abinda zai amfanar da al'ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka tsare harshena da alƙalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.😭🙏🏻_*
🎊🎊🎊🎉🎊🎉🎉🎉🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎐🎐🎐🎐🎐
HAPPY SALLAH! HAPPY SALLAH!! HAPPY SALLAH!!!🎊🎊🎊🎊🎊
*_Ya ALLAH ka bamu laɗan wannam Azumi Allah Kasa muga Sallar Layya lafiya ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al'ummar musulmi da suka rigamu gidan gaskiya, 😭🙏🏻_**Ban yarda wani ko wata yayimin amfani da littafin nam ba ta kowacce siga. Komim ƙanƙantar, ta inko hakan ya kasance ban yafe ba duniya da lahira*
'''Na Sadaukar da wannam littafin dafa farkon sa har ƙarshe gareki Ƙawata, Aminiyata,'''
*Farhat Mrs Muh'd* '''Ina matuƙar Alfahari dake Kena Hafsat A Garkuwa taki ce'''👌🏻*1*
_Free Page_
*ƘAUYEN TAKAI*
................"Takai Wani Ƙauye ne Wanda ya Tara Albarka tun Gona sosai Hakan yasa Farin Ciki a cikin Wannam Ƙauye. Da Misalin Ƙare Biyar na Ranar Alhamis, Wata yarinya Na hango tsaye a Gaban Wani Mutun dake Sai da Agwaluma, Cikin Sauri na ƙarasa dan naga mai ke Wakana. Ina zuwa Naji yarinyar Tana cewa. Sallau Yayi Kwantai! Yaje Gida a dake sa, Sallau yayi Kwantai! Yaje gida a dake sa. Haka take ta faɗi tana Jijjiga jiki. Shiko Sallau ya jika fal kamar zai fashe Amma sam ya Kasa mata magana dan baƙin cikin da yake ji.
"Yana Jin haushi Mai sai da Agwaluma ba ga wannam Aljanar Yarinyar ta Sashi Gaba. Bai Ƙarasa ba yaji tace Yasin Sallau Gwara ka bani guda biyu Kaga na Rage maka Asara." Dan Ubanki bana bayar ba, Shegiyar yarinya Fitinanniya.
"Aiko Kwaranƙwasa sai ka Bani. To dan Jakar Ubanki sai In bakin In gani. Aiki Batai wata Wata ba ta Kwakusa tasa Gudu Shiko dan Takaici ko Iya binta Bai yiba sai Kallo Da ya bita da shi yana Kuma jin takaicin Iyayenta da suke Barinta ta fito tayi ta gantali.
"Bata tsaya ko ina ba sai wani Ƙofar gida da ta zauna a Dakali ta fara shan Agwalumar ta tana zuba Waƙa irin tasu ta Ƙauye tana cewa. Ahaiye! Jalla ku Jallah! Aiye Jallaku Jalla! Ƙofar gidan su Guda biyar ne Jalla ku jalla! In Babu nam da Akwai Garin mu Jalla ku Jalla! Haka tai ta zuba Waƙarta taɓa Tiƙar rawa har ta shanye Agwaluma Guda biyar data ɗibo.
"Bata bar wajen ba har saida aka ƙira Sallar Magriba sannam ta sakai Ta nufi Wani ɗan Matsakai cin Gida. A zauren gidan ta tsaya ta fara Leƙawa tace Salamu Alaikum tana Laɓe bata da Niyar shiga Cikin Ƙara tace Wai babu Mutane a gidan ne? Ta sake Leƙawa tace Umma na hego ko na Kuma?.
"Wata Mata dake zaune tace Dan Ubanki Karki shigo Mana. Nam ta sa wata Ja'irar dariya Sannam tasa kai ta shiga. Tazo Wuce wa ta Gaban Ummanta. Umma ta mata wani Damƙa tare da cewa Gidan Uban wa kika je kinsan ke kike Kai mana Markaɗen Ƙosai shine kika tafi Gantali sai yanzu kika shigo, Saude Wallahi Zaki ci Ubanki fa.
"Sai yanzu na Ƙarewa Saude Kallo Yarinya ce da baza ta wuce Shekara Goma sha ɗaya ba tana sanye da wata ya galalliyar Doguwar Riga Ƙafarta babu takalmi. Haka Kanta babu Ko hula ballantana Mayafi kan yaci Uba Datti tayi narai narai da idanu."Wata ƴar Dattijuwa ce ta fito daga Wani ɗan ɗaki Tana cewa. Kan Uban chan Mai Saudatu ta Miki kika Mata wannam Chakwamar. Wallahi Talatu Ki Fita a Idona na Rufe tana faɗar haka tana Ƙwace Saude a Hannun Ummanta. Umma cikin Takaici Tace Haba Hajja Kaka Kina ga fa Saude tun Ɗazu nake Jira takai mana Niƙa amma ta tafi Gantali sai ke kika kai mana fa.
"To Tunda Nakai Ba shikenam ba Wallahi Talatu Idon ki Ya bar kan Saudatu. Daga haka taja ta suka shiga Ɗakin da Ta fito. Umma Kuwa Ƙwafa tayi ta ci gaba da aikin da take.
"Suna Shiga suka Zauna, Hajja Kaka tace Saudatu na Ina kika je ne haka?. Wata Wawiyar gyatsa Saude tayi tare da Cewa Hajja Kaka wallahi Ina Wajen Sallau Mai Agwaluma Nam ta faɗa mata duk yadda sukayi. Ta Ƙara da cewa Shine Na Tsaya a Ƙofar gidansu Kandala Na Shanye Saboda nasan in nazo Sai kince na Tsanmiki.
"Nam Hajja Kaka ta ɓata Rai tace Dan Ubanki Dama danni kika tsaya kika shanye?. Aiko Nikam Ba Ubana ba Cewar Saude tana Murguɗawa Hajja Kaka Baki. Ita ko bata ce mata Komai ba suka ci gaba da Hirarsu. Saude tace Wallahi Hajja Kaka Ina jin daɗin yadda kike Hana Wacchar Matan Duka na."Yo to Ina zan Bari ta dake ki ƴar Jikalle na Wanda yake dukan kin Ba yanzu baya kusa kuma ko ya dawo yayi kaɗan ya daka minke. Saude tayi wani tsallen Murna tare da cewa Wallahi Wacchar Matar Muguwa ce. Ke dai ki bari kawai Ƴar Jikalle na Kamar ba ita ta Haife ki ba ma. Nam suka sa Dariya suka ci Gaba da Hirarsu. Rabin Hirar Saude Zagin Hajja Kaka take Amma Bata Nuna mata Rashin dacewar Hakan ba sai Lallaɓata da take.
'''(Iyaye Tun Anam zan ɗan fara Jan hankalinku Sufa Ƴaƴa Amana Allah ya baku, Ku kula da Lafiyarsu Ɗabi'arsu ku kuma Basu Tarbiya. Ya kamata kuna ƙwafan Ƴaƴanku da Zagin Manyan su Bawai Ku bar yara haka sakaka ba. Ya Kamata Mu tuna da Amanar Allah. Allah yasa mu dace)'''.
"Haka suka ta Hira Umma ta Kawo musu Abinci suka ci. Washe Gari Da Sassafe Saude ta tashi ta fice Babu Ko Alwalla bare Salla. Ta fita ta Nufi Wajen Nayi mai Ƙosai da zuwan ta ko yara kamanta da ɗan wada suka fita a tare a Wajen suna Jira. Tana zuwa ta Nufi Wata yarinya dake zaune Ta jakwameta. Tana wa Na kama ɗaɓ ƙwairon Ubanki. Yarinyar tace Saude Ni kuma mai na miki?. Saude tace Kam bala'i Wato kin manta abun da kika min to yau zakiji Kwal Ubanki. Daga haka ta kai msta mari. Nayi ne tace Ke Saude mai yasa kike da Masifa ne? Daga zuwanki zaki Fara faɗan da kika Saba Alhali ba saya Kike ba sai Neman Faɗa da kike zuwa min.
"Saude tace to Ina Ruwanki Nayi Lutiya ko nayi dake ne Munafuka mai bacci da Ido Ɗaya. Aiko Cikin Takaici nayi tayo Kan Saude. Nam Saude ta Arta a Na Kare Nayi ma ta Rufa mata baya gata da Jiki sosai tana gudu Tubur! Tubur! .Take Gudu Mai Karatu In kaga wanam Gudu na Nayi dole ya baka Dariya. Saude ta mata Nisa sosai ganin haka yasa Saude tsayawa tana cewa. kaga Nayi Lutiya Tana gudu Tubur tubur Nayi Lutiya Nayi Lutiya!. Nam nayi ta ƙara Hassala.
"Ta ƙara ƙaimi Wajen Gudunta Abun ban Dariya.Gudu take sosai Amm ina ta kasa Cin Mata. Nam Yara suka Taru suna. Lah Ga Nayi Lutiya tana gudu! Nam suka Fara Waƙa da Tafi. Nayi Lutiya! Tunbur tunbur! Nayi Lutiya Tunbur tunbur Ganin Yara sai Binsa suke yasa Nayi ta tsaya tana sauke Numfashi. Sai da ta ɗan Huta sannam ta Kama hanyar kumawa Wajen Tuyarta. Tana Rantsuwar In ta kama Saude sai ta Karya ta. Ko da Taje ta samu babu Kowa Kuma ba Ƙosai. Takaici ya haɗu yay mata yawa ta ƙara ƙudirta Idonta Idon Saude sai ta Karya ta."Saude ko Tana cikin Gudu Ta Haɗu da Ƙawarta Rabi zata tafi Rafi ɗibo Ruwa. Suka ɗauki Hanya zata Raka ta. Suna tafiya suna Hira har suka isa Rafi. Suna zuwa suka Samu su Harira a Wajen. Saude ta karɓi Tulun Rabi ta Kusa zata Ɗibo Mata. Harira tace Ke Malama Baki ga Mun Riga ku bane zaki wani Shegewa.
"Saude tace yo da kuka rigamu sai Wace Uwar. Harira tace Kam bala'i Ni kike zagi?. Eh an zageki ki ɗauki Mataki. Nam Harira tayi Kan Saude. Nam Idanun Saude ya fara Rinewa Yayi Jajazir. Harira tana Zuwa Kusa da ita Saude ta Wurgata cikin Rafi. Yaran Wajen Sunyi Matuƙar tsorata da Ganin Yadda Launin Saude ya Sauya Ta Chanja tashi ɗaya Kamar ba Ita ba.
"Nam suka Fara Kukan a Taimaka musu Harira zata Nitse. Harira ko Tana Ta shan Ruwa tana ƙoƙarin Nitsewa. Falmata da ta cika da Haushin Saude tazo Fangam Fangam tace ke Saude dan Kan Uwarki mai Harira ta miki? ta ɗaga Hannu zata daki Saude Hannunta ya Maƙale a Sama. Ganin Haka Sauran Yaran dake Wajen suka sa Ihu suka fara Guduwa."Falmata Kuka take sosai Ganin Hannunta yaƙi ya miƙe. Saude Ruwan ta ɗibo tazo Miƙawa Rabi taga babu Kowa a wajen. Nam ta ɗauki Tulun ta bar Wajen Ta bar Falmata sai Kuka take. Harira ko Tuni ta Nutse a cikin Ruwa.
"Haka ta isa har gida Cikin Wannam yanayin Gidan su Rabi ta fara zuwa. Tana shiga ko Sallama babu ta Ajiye Ruwan ta fito Innan Rabi tana Saude mai ya haɗaku da Rabi ne?. Amma ko ta kanta bata biba. Tayi Gidan su ta shiga kai tsaye ɗakin Hajja Kaka ta Nufa taje tayi Zaman ta. Umma Ko da Ganin yadda Saude ta kuma Jikinta yayi sanyi. Hajja Kaka ne ta bita tana cewa Ƴar jikalle na Mai ya Sameki? Wa ya taɓa Min ke. Tana Shiga Wani Ƙara ta sake Ganin.......'''Salon na Musamman ne Nasan Zaku fara Nazarin Waye ce SAUDE. To karku Damu zakuji Ko mai Ku dai Kawai Ku biyoni Domin Na warware Muku komai.'''
_Amma ta Hanyar Nuna min Ƙauna da Soyayyarku wajen Siyan *GIRMAN ƘAUYE...!* Akan Naira 200 kachal👌🏻 ta wannam Account Number, 0134205910 HAFSAT AYUBA UNION BANK, sai ki turo shaidar biya ta wannam Number 08132761212 ko Katin waya na MTN, shima sai ki ɗauko hoton Katin a Turo kai tsaye ta wannam Number 08132761212 sai kunzo Masoyana._
_Kada fa ku manta Akwai Garaɓasa na mai son siyan Biyu *BAƘAR TUKUNYA...!* Shima Dai nawa ne a 300 ne Kachal👌🏻 Shima ta wannam Number Account ɗin da na bada da Number Wayan ta Sama ko Kuma kai Tsaye ku Tuntuɓe ni ta wannam Number domin ƙarin bayani._
08132761212*HAFSAT A GARKUWA CE*🤙🏻
YOU ARE READING
GIRMAN ƘAUYE...!
FantasyLabari ne mai taɓa Zuciya. wanda Yarinya ce Tsabar Rashin Tarbiyar ta da kulawa tasa ta haɗu...