🌀 *GIRMAN ƘAUYE...!* 🌀
_Mai fidda Farin tuwo...!_Na
*HAFSAT A GARKUWA*🤙🏻
_(Mummyn Seeyama)_*Wattpad* = _Hayfaluv_😉
🎆
*Al'Umma Writer's Asso...✍🏻*'''Alhamdulillah, Am Back Again'''
*SADAUKARWA*
_Farhat Mrs Muh'd_*BABI NA UKU*
'''Free Page'''
................"Da Sauri Saude ta wani Irin Yin ƙurawa tare da zubewa Ƙasa Haka mai Magani ya Ci gaba Amma Saude ko Motsi bata yi kuma Bai ga komai a Tattare da Ita ba. Babu yadda Aka iya haka aka barta da Kanta ta tashi ta zauna. Nam Falmata Tace Saude dan Allah Kiyi haƙuri ki sauƙar min da Hannuna bazan Ƙara shiga Sabgar ki ba. "Wani Irin Murmushi Saude Tayi Sai Hannu Falmata ya dawo Dai dai. Ba Iya Mai gari ba kowa dake Wajen Abun ya bashi Mamaki. Nam mai gari Yaja mata Kunne in ta ƙara wani abu sai Sun bar masa Garin sa Wani Kallo Saude ta masa na zan riƙeka. Nam mai Gari yasha Jinin Jikinsa. Dan shi har ga Allah Tsoro take bashi. Nam yayi Saurin Sallamar Kowa ya shige gida.
"Saude suna Kumawa ta Shige ɗaki tayi Kwanciyar ta. Hajjo Kaka Kuwa sam taƙi shiga ɗakin sai ɗakin Umma ta shiga ta Kwanta. Umma kuwa Abun Duniya ya isheta Lamarin Saude sai ita."Sai Yamma Saude ta tashi Babu Sallar Asuba bare ta La'asar. Babu kuma wanda ya damu da Rashin yinta. Nam taci Abinci. Yanayin ta ya Gama Dawowa. Taje ta Samu Hajjo kaka tace. Hajjo Ɗan bani Biyar Mana in sayi ɗan tamatsitsi. Hajjo Kaka ta Kunce Zaninta tare da cire Mata biyar ta miƙa mata. Da Gudu ta karɓa tayi Waje.
"Tana fita bata Zarce ko ina ba sai inda Wasu Yara sa'anninta Suke tare."Tana zuwa ta wuce Wajen Wata Mata dake saida ɗan ta Matsitsi. Ta miƙa Kuɗin tare da cewa Goggo Ki bani Ɗan ta matsitsi. Da Sauri Matar ta ɗauko tare da Miƙa mata. Nam ta isa kusa da Wata Ƙawarta Mairo tace. Mairo Zo ki Rakani Gidan su Rabi, Mairo ta taho tare da Altine Suka Kama hanna Suna tafiya suna Wasa. Nam Saude ta Hango Nayi Mai Ƙosai da Bazawarin ta suna Hira."Saude Tace Kunga kuzo Muje mu tsokani Nayi ga ta chan, nam ta raɗa musu abun da zasuyi tare da Nuna musu Inda take. Haka suka Raƙuɓe suka fara Tafi tare da Cewa. Nayi Lukute tiya Gatanam Lukutetiya. Kai Nayi Lukutetiya Gatanam tana Hira! Nayi tana Jinsu Amma ta daure ta kasa Magana.
"Shima Bazawarin Yana Jinsu chan dai yace Wai Nayi waɗan nam Yaran ba dake suke ba?. Nayi cikin Takaici Har tana Zubar da ƙwallah tace Dani Suke Wallahi. Na Rasa yadda zanyi da Wannam Aljanar Yarinyar ta Takuramin Gashi yanzu Kisa take. Ta ƙarasa Maganar tana Mai Fashewa da Kuka."Malam Lado Bazawarinta Ƙuƙarin Ƙunshe Dariyarsa yake. Dan tayi Matuƙar bashi Dariya. Nam ce ya Daure yace Kiyi Haƙuri Karma ki Shiga harkar ta. A bangaren Su Saude Kuwa Da suka ga Nayi ta Fara Kuka ne taja Ƙawayenta Suka tafi.
"Basu tsaya ko ina ba sai Gidan su Rabi da Sallama suka Shiga Suka Tarar da Goggon Rabi a tsakar Gida Gaida ta sukayi nam. Goggo Rabi tace Ke Saude Mai ya Kawoki Gidan nam?.
"Cikin fara'a tace Nazo Wajen Rabi ne. Goggo Tace to Wallahi Ki bar gidan nam Kuma karki Ƙara zuwa Gidan nam Mayyar Banza Kawai Dahalla Fita min daga Gida ta ƙarasa Maganar Cikin tsawa.
"Saude ta fita tana mai zubar da ƙwallah Ƙawayenta suka Mara mata baya. Tunda suka Fita suke Mata Magana Amma Sam taƙi kulawa su sai Hawaye da take.
"Gidan su Ta shiga Suma suka Bita tana Shiga ta Samu Umma da Hajjo Kaka a tsakar gida ko inda suke bata Kalla ba. Umma ta miƙe tace Na Shiga Uku ne Talatu Yaushe Rabon Saude da kuka?. Yau nikam Na shiga Uki.
"Hajjo Kaka tace Yau mun shiga Uku dai Wani Ɗan Uban ne ya daka min Ƴar Jika ta?. Yau akwai Bura Uba a Ƙauyen nam. Mairo ce ta Sanar dasu Komai nam Hajjo Kaka Tace Jar Uba Jikar tawa za a Ƙira da Mayya?. Tana faɗar haka tana saɓa Mayafi tayi Waje tana tafe tana Sababi hanyar Gidan su Rabi ta Nufa Su Mairo ko suna biye da ita.
"Ko Sallama Hajjo Kaka Batayi ba Cikin Masifa tace Ina Matsiyaciyar Matar Gidan nam?. Cikin Fusata Hajjo Kaka take Maganar. Goggo ta fito Tace Haba Hajjo ya zaki shigo gidan Mutane ba ko Sallama?. Anƙi ayi Sallaman, Nace Anƙi ayi Sallamar ki ɗauki Mataki dan Jakar Ubanki . Wai har ke zaki cewa Jikata Mayya? To Wallahi Zakici Ubanki. Hajjo Kaka ta faɗa tana mai Shan Ɗamara.
YOU ARE READING
GIRMAN ƘAUYE...!
FantasyLabari ne mai taɓa Zuciya. wanda Yarinya ce Tsabar Rashin Tarbiyar ta da kulawa tasa ta haɗu...