13

3.5K 122 15
                                    

http://www.youtube.com/channel/UCXz_jPVZsMtLDEbT4tnNTrw?sub_confirmation=1

*Ku danna wannan shudin rubutun dake sama👆👆👆👆 domin samun wasu littafan dana rubuta, tare da magungunan karin ni'ima domin jin dadin zamantakewa*

*GIDAN KASHE AHU*

*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*

*Wattpad @maryam-obam*

*DEDICATED TO.....*
*AYSHA A BAGUDU*

*WARNING WARNING 'YAN MATA PLZ KARKU KARANTA MIN NOVEL, ONLY MATAN AURE NA YARDA SU KARANTA*

*PAGE 13*


Kai tsaye dakinsu ta nufa inda ta ajiye ledan hannunta a kusa da sauran kayan, ta fada Kan gadon dakin inda ta Fara risgan kukan da ita kanta Bata San dalilin yinshi ba..... Kuka take sosai inda taji maganan Aysha a kanta Wanda Bata ji sanda ta shigo ba, tana fadin Afrah maiya faru kike wannan kukan Kar dai kice wanine ya mutu???

Afrah tashi tayi inda ta zauna tana goge hawayen dake zuba daga idanunta, ta kalli Aysha da rinannun idanunta da suka Fara kad'awa sukai ja saboda kuka, tace Aysha Babu Wanda ya mutu Aysha dama akwai irin wannan soyayyar da zakaji baka ganin komai da kowa??

Aysha dariya tayi tare da fadin kaman ya? Ban fahimta ba? Wa kike so haka??

Afrah ta sauke wani irin ajiyan zuciya sannan tace Babu kowa, kin San David??

Aysha tace oh wannan arnen??

Afrah Saida taji wani iri jin tace wannan arnen Amma saita dake imma Bata dake dinba Babu yanda zatayi domin dai Aysha gaskiya ta fada ba musulmi bane Arne ne, inama ya musulinta dasai tafi kowa jin Dadi fiye da kowa duk da tasan bazata sameshi ba Koda kuwa Mai zai faru.....

Aysha ce ta katseta da fadin Ina jinki wani Abu ya samu David dinne

Afrah tace Babu abunda ya sameshi, Aysha na rasa wani irin soyayya yake mun, kwata kwata yaushe muka hadu dashi haka? Shuru tayi tana dafe kanta alaman Yana mata ciwo, sannan taci gaba da fadin Aysha yana kokarin nunamin zai iya komai a kaina.....

Aysha dariya ta Kuma saki tare da fadin saiya musulinta kawai, in Yana sonki dagaske sai kuyi aure, Amma Afrah kema tab wlh naji mamaki yanda har Kika yarda Kika bama Arne jikinki, aini wlh ban iyawa duk da Guy din ya hadu Amma bazan iyaba Arne fah baya tsarki, uhm Amma dai naji wannan akwai daukan kamshi wlh inba wannan cross dinba Dana gani a gidansa ba zan rantse musulmi ne, gashi da suffar musulmai Kai yayi tako ina wlh Ina mishi fatan ya gane hanyar gaskiya ya gane addinin musulunci shine dai dai ya musulinta Kinga da kin samu miji na nuna ma duniya uwa uba in yace zai auren inya musulunta wlh zan aureshi Kinga ke uwar gida ni Amarya ta karasa maganan da dariya

Afrah Bata ce komai ba Amma maganan Aysha tasan gaskiya ne, Babu Mai kushe David domin kuwa ya hadu iya haduwa, toh sai dai matsalan addini daya banbanta, sannan tasan zuri'arsu bazasu yarda ba ya aureta Koda ya musulinta domin tasan duk wani Abu da zata nuna tana so toh dangin mahaifinta Suna adawa dashi, ita har yau Tana son sanin wani Abu iyayenta suka aikata Wanda suka tsani aurensu, Mai iyayenta suka Yi Wanda dangin mahaifinta suka tsani mahaifiyarta? Sannan Mai mahaifinta yayi suka barshi cikin kunci da talauci Basu son taimaka mishi, duk kuwa da irin biyayyan da yake musu sannan tasan Suna da hanyar taimaka Masa ko sama mishi wani Abu domin ya samu ya iya rike kanshi da iyalanshi harma ya taimaki wasu, Amma sun barshi haka, wani hawaye ne ya zubo Mata Mai zafi tabbas tana son tayi karatu Mai tsawo domin ta taimaki iyayenta a matsayinta na yarsu ta farko da Allah ya Basu, tana burin zaman musu abun alfahari Wanda zata mantar dasu rashin d'a namiji da Basu dashi, ta nuna musu Allah ya Basu y'a mace Mai zuciya ta nuna ma dangin mahaifinta cewa itama fah zata zama gatan iyayenta....... Wani hawaye ne ya Fara kwaranyo mata a fuskar inda ta Fara fadin na cuci kaina na cuci iyayena, na Fara aikata Zina saboda son zuciya, duk abunda ya faru Dani Bai kamata in bada ticket din ci gaba da aikata babban laifi ba....

GIDAN KASHE AHUWhere stories live. Discover now