🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰
🤰*KARATU KO TALLAH!??*🤰
🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰*_Gajeren labari me dauke da dogon darasi._*
Written by:
*Sadik Abubakar**Wattpad @sadikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_Wannan labari ƙirƙirar ne, banyi shi ba dan rayuwar wani kodan ɓatawa wani rai. Duk sunayen dake cikin labarin anyi amfani dasu ne domin isar da saƙon labarin kawai._*✍️✍️✍️
*Sadaukarwa ga daukacin yan 'yan talla da kuma 'yan makaranta.*
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Dukkan godiya da yabo marasa iyaka sun tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su kara jaddada ga Annabi _MUHAMMAD_ ((Sallallahu Alaihi Wasallama)).*
*Kashi Na Daya*
Hankalin ta na matuƙar tashi duk lokacin da ta fara akan irin gorace-gorace da habaice-habaicen 'yan gidan su kanyi mata daga ita har iyayen ta, wani lokacin har cewa suke wai tafi ƙarfin iyayen nata, duk saboda tace ba zata dauki talla ba. Wani lokacin ma tsangawamar har da mahaifiyar ta ake mata, duk akan ta zaɓi yin karatu a madadin talla. Wai yaya zanyi? Wayyo Allah na, na shiga uku, Allah ka kawo min mafita.
Raliya kenan wacce take zaune tare da mahaifinta a wani gidan haya mai ɗakuna ashirin da biyar (25), wato akwai magidanta mutum goma sha takwas ciki har da mahaifin Raliya. Mutane bakwai daga cikin magidantan ɗakuna bibiyu suke riƙe dasu, sakammakon suna da ƴa ƴa manya wanda ba zasu iya haɗa kwanciya dasu ba a ɗaki ɗaya. Malam Bala shine mahaifin Raliya, shima ɗakuna biyu yake riƙe dasu domin ƴa ƴansa shida ne, Raliya ita ce babba sai ƙannen ta mata uku da kuma maza guda biyu. Mahaifin Raliya sana'ar wanki da guga yake.
Aƙalla adadin yaran dake gidan su Raliya sun haura sittin (60) ƴan mata da samari da kuma ƙananan yara. Duk yaro ko yarinyar da ta tasa a wannan gida, babu abinda ke gabansu sai talla sawa'un yaron na so ko kuma baya so sakammakon iyayen su talakawa ne ainin. Wasu daga cikin iyaye maza a wannan gida basu da sana'a, iyaye matan sune ke riƙe da gidan, su da ƴa ƴan nasu kan haɗu suyi sana'a domin rufawa kai asiri, kai hatta kuɗin haya ma sune ke biya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
To tsarin Raliya da tunanin ta yasha banban da na sauran yaran gidan, domin ita kuwa ta ƙeƙasa - ƙasa, sam bata san wata aba ba wai ita talla, inaaa, wannan baya cikin tsarin ta. Bawai girman kai bane yasa ba zata ɗauki talla ba, a'a ko kaɗan, kawai dai tana da burin yin karatun zamani domin ta zama mai amfani ga al'umma ba mai amfanuwa da al'umma ba kaɗai, tana da burin ganin ta bada gudummawar ta wajen cigaba da inganta rayuwar al'umma, musamman mata da ƙananan yara saboda ta fuskanci wannan ɓangarori biyu na al'umma sunfi kowanne ɓangare shan wahala, kuma mafiya mutane sunyi watsi dasu, ba'a basu muhimmanci da kulawar da ta dace dasu.
Raliya da sauran yaran gidan su basu san wani karatun zamani ba (karatun boko), basu samu ƴancin yi ba, na addinin ma ba wata kula iyayen keyi a kai ba. Islmaiyya ce suke zuwa da daddare, wasu ma ba kullen suke samun damar zuwa ba saboda duk ranar da akayi rashin sa'a abinci ya yi kwantai, to akwai kasuwar ƴan kwantai in dare ya yi can zasu kai su sayarwa da ƴan-ga-ruwa da almajirai.
YOU ARE READING
KARATU KO TALLAH???
General FictionRaliya yarinya ce wacce ta kekasa kasa tace allan fur karatu xatayi, ita sam bata san me talla ba, duk da cewa iyayenta talakawa ne kuma suna wani gida da dukkan yaran gida talla ce sana'ar su.