NANNY..

1.9K 153 2
                                    

*NANNY...!*
      (Mai Reno..)

*Alƙaluman:*✍🏻

*AISHA ALTO💞*
*JAMILA UMAR (Janafty💕*

_Don't Forget to Follow us On Wattpad: Janafnancy13 or Aisha Alto Alto_

*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔*
*KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

      *BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

........Ya Daɗe Zaune a gefen Gado yana Dafe da kanshi yana Jimamin Abunda Baba Hakimi ya Sanar Dashi, Tausayin Mufeeda na Ƙara Cika masa Zuciya. Rashin Mahaifiya Akwai Ciwo balle Ita Daba Uwa ba uba..

Ya daɗe Zaune Baisan Iya Adadin Lokacin Daya Ɗiba yana Tunani da Kuma Tausayin Mufeeda ba, Kiran Sallah ya ƙara Jiyowa Daga Masallatan Dake Kusa Dasu Zabura yayi ya Miƙe Lokaci Ɗaya yana Duba agogon Wayarsa yaga 5:10am Da Sauri Ya Nufi Wardrope ɗinshi ya Buɗe ya Ɗauko Wata Jallabiya mai Ruwan Toka ya Zura Hula ya sanya kafin ya Ɗauki Carbin sa ya Fice Daga Ɗakin.

Ƙasa ya Sauko Zuwa Ɗakin Bassam Shi ya kuma Tashi Su Basma, Iya kuma Koda ya Leƙa Ɗakinta Ta tashi sai yace Ta tashi Mufeeda Lokacin Sallah yayi, Daga nan Suka Wuce Masallaci Shida Bassam sai Wajen Bakwai Saura Suka Dawo Suna Shigowa Falon Suka Iske Basma Tsaye da Uniform A jikinta Cikin Girmamawa Ta Duƙa ta gaishe da Tahir, Cikin kallonta yake amsawa yana Faɗin "Ku Saka kayan gida ne Basma Gaba ɗayanmu yau Ɗanbatta zamu.." Tare da Bassam Suka Kalleshi Cikin Murna Suka ce "Da gaske Daddy..?" Kai ya gyaɗa musu alaman Hakane Tsalle Suka Farayi alamar Murna Cikin Dakewa yace "Ku ɗiba kayanku koda Kala Uku uku ne sai bayan Kwana Uku zaku Dawo.." Jin Haka yasa Suka Zura da Gudu Zuwa Ɗakunansu da Kallo ya bisu Acikin Ranshi yana Faɗin Kurucci Dangin Hauka.

Yana Shirin Haurawa Sama Iya ta Fito Daga Kichen ganinshi yasa Ta saki Fuska Tana Faɗin "Ah...Alhaji Barka da Safiya.." Cikin Sanyi ya waigo yana Faɗin "Ina kwana Iya..?" Ta amsa da lafiya lau bai bata Zarafin magana ba yace "Ahm Iya Ki Shirya kayanki ki kuma Saka Mufeeda Ta Shirya Kayanta Ɗanbatta zamu yanzu da Safen nan." Iya ta Ji Zuciyarta ta Tsinke da Sauri Tace "Ɗanbatta kuma Alhaji..? Allah sa lafiya..?"

Shiru yayi kafin yace A hankali.. "Mahaifiyar Mufeeda ce Allah yama Rasuwa Jiya da Daddare yanzu Baba Hakimi ya Kirani yake Faɗa min.." Dafe Kirki Iya Tayi kafin tace "Innalillahi Wa'inna Alaihirraju'un..." Ciwo Tayi Alhaji..?"

Kai ya gyaɗa mata kafin yace "Eh har ta kwanta Asibiti ma, Ki Taimakama Mufeeda Don Allah Iya, Kuma karki Sanar da Ita Domin batasan Halin Da'ake Ciki ba.."Jinjina kai Iya Tayi Tana Faɗin "Allah Sarki Haƙiƙa Mufeeda Tayi Rashi babba..Allah Ya Jiƙan Inna Fulera, Insha Allahu Alhaji yanzu zamu Shirya.." Ta faɗa Cike da Tausayawa.

Gyaɗa mai kai yayi kafin ya Haura sama Ita kuma ta Koma Kichen Ta Cigaba da Soya Dankali, cikin Jimami da Tausayin Mufeeda sai da Ta kammalah Duka Abun karyawan Ta kwaso Zuwa Dininng kana Ta Shiga Ɗakin Mufeeda Ta Isketa Tayi Wanka Har ta shirya Cikin Uniform ɗinta Naila ma Ta mata Wanka Ta Shiryata Cikin Riga da Wando, Tana gefen Gadon Tana Riƙe da Hannun Naila wacce Ke Tata tan Tafiya, cike da Tausayin Mufeeda Iya ta Shigo Ɗakin Tana Faɗin "Mufeeda Ki Cire kayan Makarantar ki saka na gida kuma ki Haɗa kayanki Cikin Akwati Naki dana Naila yanzu Alhaji ke gayamin Ɗanbatta zamu Tafi Dukkanmu sai mun kwana Biyu A chan.."

Da Sauri Mufeeda Ta Ɗago Tana kallon Iya Cikin Fitar Magana tace "Ɗanbatta kuma iiya..? Na Shiga Uku ko Gida Daddy zai maidani..?" Ta faɗa Idanuwanta na Cikowa da Ƙwallah Saurin girgiza kai Iya Tayi Tana Faɗin "Ko Ɗaya inaga dai Hutu Alhaji ya samu yakeso muje chan Muyi Hutun.." Ta faɗa Tana Ƙara Jin Tausayin Mufeedan, jin Haka ya saka Mufeeda Ta Washe baki Tana Faɗin "Da gaske Iya..? Yau zan kwana A ƙirjin Innata.." Ta faɗa Cikin Farin ciki Lokaci Ɗaya Tana Ijiye Naila kan gado ta isa Wajen Akwatinta ta Ɗauko, Iya Fita tayi Tana Sharan Ƙwallar Tausayin Mufeeda.

NANNY(Mai Reno.)Where stories live. Discover now