*ZAMANI*👩🏼🦱
*Labari Mai Tafiya da zamani labari Mai k'unshe da zamanin da muka tsinci kanmu a ciki Baga 'yan matan ba Baga Matan Auren Ba karku Bari a Baku labari*!!!!*Written by*
*Sadnaf*💥💥*3.am*
Ba abinda kake ji sai sheshek'an kukan Mubeena dake kuka sosai daga ita sai under wear tunda take a rayuwarta bata tab'a tsintar kanta a cikin tashin hankali irin wanan ba bata taba hararo Asirinta zai tonu ba lura da irin kokarin da tayi dan asirin nata ya rufu ji take dama duk abinda ke faruwa inama ace mafarki take kuka kawai take na rashin Mafita har yanzu tana mamakin yanda akayi Dr Yazeed ya gane halin da take ciki banda ma kwakwalwarta ya toshe ya za'ayi ta manta Gynecology ne Dr Yazeed duk halin da take ciki dole ya iya ganewa ita Duk ba Wanan ba yanzu bata San wane mataki zai d'auka akanta ba kuka ta kara rushewa dashi for the first time da ta fara nadamar Rayuwar da tayi a Baya.
Dr Yazeed kuwa kai kawo kawai yake a tsakiyar dakin duk da filtilar d'akin ba Mai Haske bane kana iya hango irin gumin da yake da wasu irin jijjiyo dake tattashe a goshinsa kallo d'aya zaka mishi kasan ransa a b'ace yake daga shi sai dogon wando hannunsa dafe dakansa dake barazanar tsagewa har wani k'yarma yake sabida tsananin b'acin Rai.
Kukan da Mubeena keyi kamar Kara mishi b'acin Rai yake da idonsa da suka kad'a sukayi jajjawur yake kallonta daga inda yake tsaye har yanzu ya Kasa gasgata abinda ke faruwa bai taba tunanin Daren Farkonsa daya dade yana tanadi a rayuwarsa zai zo masa a haka ba bai Tab'a tunanin Mubeena ta siyar da budurcinta a titi ba Yasan he is social he is romantic amma sabida tsananin kishinsa da k'yank'yami bai tab'a aikata zina ba a rayuwarsa Duk da irin Matan da suka sha kawo masa Hari wasu da kudinsu ma so suke yayi iskanci dasu bama da aure ba su dai su samu biyan Bukarsu bai tab'a ma kwatantawa dan shima bazai so ace matar da zai Aura wani ya fara saninta ba sabida shi namiji ne da Allah yayiwa tsananin kishi na fitar hankali shi yasa yake mamakin Mazan da suke shek'a Ayarsu da mata amma to his surprise sai gashi shine yau ya auro katuwar mazinaciya.
Runtse idonsa yayi da k'arfi ya daka mata tsawa dan kukanta da yake ji kamar kara masa b'acin rai yake.
"Shut up Mubeena Enough of your Drama kukan uban me kike min? after all the damage u have caused my life har yanzu ina mamakin yanda ma akayi idona ya rufe na aureki Mubeena Mubeena har yanzu ina mamakin yanda na kasa gane ke wacece Har na auroki na kawo cikin gidana Har yanzu ina mamakin yanda Har kika iya fooling dina"
"Have you forgotten who you are dealing with?
Am a gynecologist Mubeena! if you are raped dole na sani,wai Har Ni zaki linke Mubeena kije ayi miki dinki sabida kar na gane ke buduruwa ce how could you"?
Mubeena cikin tsananin tashin hankali tace "Wlh dgsk nake Dr I was rapped ka yarda dani bansan ta yanda zan gaya maka ba kafin muyi auren shiyasa na zabi na b'oye maka I can't bear to loose you pls forgive me"
"You are still lying Mubeena abinda ke kara sakamin tsanarki right now that am standing you are still distancing your self from me kin cuceni wlh ba yanda zan zauna da mazinaciya cos ni ba mazinaci bane you can Neva be mother of my children Neva Mubeena you are going back to your parents house tomorrow Morning Alhamdulillah ban kai ga kusantarki ba balle na kwashi kazantar wani"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun U can do this to me ka rufamin asiri karka sakeni Yau aka kawoni gidanka fa idan naje mai zan fada musu pls ka rufamin asiri don't forget the love and the promises"
Mubeena tace a gigice tana zub'ewa agabansa tare da rik'e k'afafuwansa.
Fizge k'afarsa yayi tare da watsa mata wani mugun kallon tsana yana " To Hell with the love and the promises you are leaving my house first thing tomorrow morning I so much hate you with passion I don't care what people would say am not sure if am in my right senses na Aureki wlh karki bari gobe na dawo side dinan na tarar dake Na sakeki saki daya"
YOU ARE READING
Zamani
General FictionLabar Mai Tafiya Da Zamani if u Are Ready let me See Ur hands up How many of u miss me