*ZAMANI*👩🏼🦱
*Written by*
*Sadnaf*💥💥*Two*
Sainting Gidan da kawayen Mubeena suke tayi ne yasa Mubeena yaye lullubinta itama ta hau kallon ko'ina Na Gidan,Ganin komai take kamar a Mafarki wani irin farinciki ne ya ringa ratsa ta da take kallon irin had'uwa da tsarin gidan Ba wani baban gida bane gini da tsarin gidan ne kawai abin kallo ya had'u ba karya ta dade da Sanin Zeed d'inta is classic Dole Gidansa ya zama Abin kallo.
Mik'ewa tayi ta Ta nufi wajen Seeyah dake kallon shuke shuken da suka balain K'awata Gidan kamar Wajen shakatawa ta rungumota tana
"Seeyah pls am I Dreaming Yau Nice a gidan Zeed"?
Tureta Seeya tayi tana " Ke kukan dadi ma kike Allah ya taimakeki kin shiga daga ciki mu kin Barmu ki koma ki Zauna kar a zo aga Amarya Mara Kunya ki bari a watse sai na tayaki muyi Abubuwan da suka rage mana Mu Tafi tunda kince yace baya San ganinmu".
Da Sauri Mubeena ta koma gefen Gado ta Zauna da ta jiyo takun Tafiya.
Ahaka 'yan uwanta suka kara Mata Nasiha suka fara Watsewa ya Rage daga Mubeena sai Seeyah Safeena da Siyama.
Da Sauri Seeya ta bude jakarta ta fito da kullin magunguna ta ware wani ta Mik'awa Mubeena tana "yi sauri Ki shiga bandaki kiyi zuba a ruwa ki watsa wanan kuma inserting zakiyi kin Tuna dai yanda yace kiyi Amfani dashi Seeya tace tana mik'a mata wani dunkullen abu.
Da Sauri Mubeena ta cire kayanta daga ita sai Under wear data ja shi Saman kirjinta ta nufi Band'aki.
Tayi Amfani da magungunan Ta fito jikinta duk jirwayen Magani.
Safeena da Siyama kuwa suna daga gefe suna dan Hirarsu dan duk kanwar Ja ce ba Wanda Baya bin mallami akan bukatarsu ta duniya sai Hali yazo daya ake abota.
Seeyah coal din data kunna a kaskon turaren wuta ta matso Mata Dashi.
Mubeena tayi Sauri ta tsugunna akan kaskon Seeyah ta mik'a mata layya guda uku ta zuba akan kaskon dayan daya yi Saura ta mik'awa Mubeena ta Jefa a bakinta ta.Seeyah ta jawo Mayafin Mubeena ta rufeta dashi.
Dariya su Siyama suka kyalkyale dashi Suna " Yayi assistant Teacher dole ma matar Dr ta Sallameki ni kuyi Ku gama mu Tafi Alhaji Tahir yana can yana jirana akwai masu Kauri danake na k'arba a hannunsa"
"Ai yanzu nan zamu Tafi kema kinsan bana Aikin Banza Dole ta sallameni "
Seeyah tace tana kara gyarawa Mubeena lullubin Mayafin sai data kwashi mintoci Ahaka kafin ta yaye Mayafin.
Tana sharba Gumi gefen Gadon ta koma ta zauna.
Seeyah ta janyo turaren Wuta ta watsa akan Kaskon nan da nan d'akin ya Hau K'amshi.
"Toh na gama Aikina kinga shidda ta kusa zai iya shigowa kowane lokaci ga kaya nan ki saka ki kara Murza kwalliya sai munyi Waya goben kila Nazo idan Banyi Tafiya ba"
Kai Mubeena ta gyad'a Mata dan teacher yace mata in ta saka layyan a baki kar ta bude baki tayi magana da kowa har sai da Dr Yazeed za tayi Magana sanan ta cire Layyan.
Cikin mintina biyar suka mata Sallama suka Tafi.
Suna Tafiya Mubeena ta kara shiryawa cikin wasu kaya da suka Bayyana Surar jikinta ba abinda ke tashi a dakin sai kamshin Turare sai murmushi take tana juya layyar dake bakinta da harshe sai kallon K'ofa take finally lokacin da ta dade tana mafarkinsa yazo Yau gata a gidan Zeed d'inta.
YOU ARE READING
Zamani
General FictionLabar Mai Tafiya Da Zamani if u Are Ready let me See Ur hands up How many of u miss me