1

2.1K 126 5
                                    

A hankali yake share hawayen idonsa, duk jarumta irin tasa yau ya kasa daurewa, duk wani taimako ya kasa bata a matsayin sa na babban likita, ba xai iya haqurin jure rashin Salma a tare da shi ba.

Itace rayuwarsa, komai Ma nata yana birgeshi yana so, yana tuna rayuwarsu na aure da Salma, tana matuqar so da qaunar sa kamar yanda yake mata tare da yaron su marwan mai shekaru bakwai kacal a duniya.

Sai safa da marwa yake tsakanin d'akin da take kwance xuwa corridor na asibitin yayin da likitoci ke kanta suna qoqarin ganin sun ceto rayuwar ta, shine babba acikin su amma bashi da wannan qarfin duba ta ko bata wani taimako saboda raunin xuciyar sa a yau.

Ya qara takawa xuwa d'akin yana kallon su a hankali dai dai lokacin da ta d'aga yatsan hannun ta da kyar tana nuna sa wanda ya saka sa nufar ta da sauri ya riqe hannun tare da xuba mata manyan idanun sa da suka sauya kala xuwa ja, da kyar ta motsa bakin ta tana magana baya jin abinda take fad'a ya sunkuya tare da kai kunnen sa dai dai bakin ta yana saurare.

Tace kayi aure ka manta dani, ka jure rashi na bakori, Allah bai nufa xamu... ya katseta ta hanyar d'ora hannunsa a bakin ta yana qara kallon ta da idanun sa da suka qeqance kamar ba nashi ba, ya sumbaci goshin ta Karo na farko tare da lumshe idanuwansa kafin ya bud'e yana kallon ta.

Xamu cigaba da rayuwa tare Salma har xuwa lokacin da numfashi xai bar jikina, baxan iya rayuwa da wata mace bayan ke ba, ki min wannan alqawari na kasancewa tare dani har abada..

Murmushi tayi bayan ta shafi fuskar sa, naji ajikina baxan tashi ba Saif, wallahi naji baxan tashi ba, ta soma hawaye sosai tana fad'in, ka kula min da marwan, kaso abinda marwan ke so, kaso ko menene yafi kusanci da marwan ko wacece idan yana samun kulawa daga gare ta, nasan xata iya kula da kai fiye da yanda nake kula da kai, ka min wannan alqawarin ba..... Numfashin ta na soma sarqewa, jini na fita ta ko ina a bakin ta da hancin ta.

Hankalin sa nayi matuqar tashi da sauri ya bada umarnin ayi emergency da ita amma kafin su qarasa tuni Allah ya karbi rayuwar Salma.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kuka yaci qarfin sa, duk jarumta irin tasa da qarfin halin sa ya kasa jurewa, ya fito yana xare safar hannun sa, ya dubi mahaifan sa dake tsaye duk suka qaraso gare sa cikin tambayar wane hali Salma d'in take ciki?

Daga yanayin sa suka gane babu Salma, sun rasa salma

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un suke ta nanatawa, Allah ya jiqan Salma amin.

ZARAH... Where stories live. Discover now