💞💞WAZAN AURA PART 1💞💞

57 4 4
                                    

Part one free

💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞

(THE BEGINNING)


fictional😩

traditional 🏚

politicians 🇳🇬

love💖
story

WRITTEN BY

ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

DEDICATED BY

RALEEYAT YA'U (UOM KHADY)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR :GIDAN GADO

AND  NOW

WAZAN AURA



INA TAWASSALI DA SUNAYENKA KYAWAWA YA ALLAH KA BANI IKON RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANI AL'UMAR MUSULMI BAKI DAYA KA HANENI DA RUBUTA BA DAI DAI BA, IN DA NA FARA WANNAN NOVEL LAFIYA YA BANI IKON GAMAWA LAFIYA,

Aunty na kanmu Allah ya Kara lpy da Nisan kwana ya Albarkaci Zuri'a (Aunty Hauwa)

Na sadaukar da wannan page ga duk wani ko wata mai fama da laluran SICKLE  CELL ANEMIA (sikila😭😭😭)
Allah ya yayemuku wanga lalura,

Kira ga yan mata da Samari please Taya Allah kiwo yafi Allah na nan ki tabbatar kunyi gwajin genotype before kuyi Aure, Allah ya bamu Zuri'a nagari Ameen 👏👏




Wannan lbr kirkirarrene Kuma basirata ne duk wanda yayi dai dai da rayuwanshi to akasi ne, Inna gyarane sai ya gyara,  kuma ban yarda wani ko wata ya juyamun lbr ba,

💘💘PAGE 1 TO 2💘💘

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

"Wayyo Allah  na Ummu ki daukota muje Asibiti karta mutu, "Uhmmn yanzu Sumayya ina muka ga kudin da zamu kaita asibiti kin san in munje ba kudi ba wanda zai kallemu,  "wai Mutanen   duniya yanzu Ummu basa taimako ne, wlh nima in na zama wani Abu nan gaba bazan taimaki kowa ba"Kull kar in Kara jin kin fadi haka Sumayya, wani Kakari da ihu da Wanda ke kwance tayi, duk sukayo kanta kakkafewa idonta yayi, Da gudu tayi Hanyar Kofar gidan  ta fitowa taci karo da wani makocin su yana dan gungoro mashin dinshi dayayi faci, da gudu ta karasa gareshi "don Allah Mudi ka taimakemu Yar uwata ce bata da lpy ka taimaka mu kaita asibiti, "subhanallahi badai Sikilan nata bane ya tashi, "eh shine wlh suna karasawa suka ga Ummu tana rungume da ita tana kuka da sunbatu, "don Allah Maryama ki tashi karki tafi ki barmu a duniyar nan, "Kamata Ummu Sumayya mu kaita asibiti, "Mudi bamu da kudi fa, "kamata haka mu tafi Allah zai rufa Asiri, Sumayya yi Maza kitaro abun hawa kan hanya, da gudu Sumayya ta fita, su kuma suka kamo Maryama suka fito da ita tamkar da matacciya, sai a lokacin na karema ta kallo kyakyawa ce na ajin karshe sai dai daka kalleta zaka gane bata cika koshin lpya budurwa ce yar kimanin shekara Ashirin Amma sbda lalurar dake tare da ita zaki dauka yar sha hudu ce,
Suna fitowa suka tarar har Sumayya tazo da me Nafef din, haka suka samu suka sata ciki yaja su, Sai Asibitin Aminu kano teaching hospital, Suna isa aka shige da ita,

Sukuma suka tsaya a waiting room, Me napep ne ya biyosu "Hajiya baku bani kudina ba, "Nawa Zamu baka, "kudinku Dari biyar"Haba Mallam ga dai dari biyu nan, kayi hkr"gskya Hajiya Anmun son rai, wlh kuje ku da Allah, "Haba bawan Allah mare lpy fa muka dauko ba taimakone a duniya don Allah kayi hkr wlh shikenan mun badon haka ba dana cika ma, karkace ka barni da Allah, "Oho nima fa mai nake sawa a Napep din nan ba ruwa ba, ehe, wata matane dake zaune take jin duk abunda yake faruwa, ta ciro dari uku a jakanta kudin ma duk Yaji jiki Daga gani itama bashi gareta ba, ta mika mai bako kunya ba tausayi ya karba yayi gaba yana maganganu, "Baiwar Allah mun gode Allah ya saka da alheri, "ba komai Allah ya rufa mana Asiri, Sumayya ce keta kaiwa da dawowa, "Ummu ina Mudin?  Ai ya tafi tun dazu, nasha zai tsayane ya taimaka mana da wani abun, "yadai ce bari yaje ya dawo,

"Suwaye yan uwan wacce aka shiga da ita Emergency yanzu?  "Gamunan Ummu ne da Sumayyah suka hada baki gurin fadin haka, "likita na nemanku, "to muje, binta sukayi a baya suka shiga Office din hade da Sallama, wani Farin kyakyawa matashi ne zaune a Office din yasa kayan likitoci da, alama shine likitan ita kuma Maryama tana kwance kan gadon dake Office din, Amsa musu Sallaman su yayi ba tare daya dago ya kallesu ba, zama sukayi suna jiran jin me zai cemusu, sai da ya kai gurin minti goma suna zaune baice musu komai ba, har Sumayya ta fara tsaki sbda ita fa a ka idanta bata jure wulakanci, "oh Sorry kune  yan uwan Maryama Nuraddeen  wurno, "eh mune Doctor, "kun san tana da sikila koh? "Eh mun sani Doctor, "Ok to gskya ciwonta ne ya tashi kun san shi wannan ciwon ba wuyan ya shanye ma Mutum jini, in so samune ma a ce duk ending Month a dunga kwashe jininta Ana samata wani, yanzu dai kafin abata duk wani taimako tana bukatar Jini Leda uku, "wayyo Allah a debi nawa doctor a samata, ko Leda goma ne, "how old are you dazakice a debi jininki, ko ba haka bama ba,a diban jinin mace Sai ya zama dole, yanzu in zaku kawo wanda, za,a dibane zaku biya Dubu bakwai na diba da test din da za,a yimata, in kuma siya zakuyi zaku biya dubu sittin Leda uku, "don Allah doctor ka taimaka mana wlh bamu Da wannan kudin, bamu da Wanda zai taimakemu bamu da kowa, mu yan gudun Hijirane Daga garin Sokoto duk an kashe mana Ahali gaba daya dukiyoyin mu sun salwanta, "dakata baiwar Allah bashi na tanbayeki ba, zaku iya fita kuje can ku nemo, haka kuke ai kudunga karya kuna batama Hausawa suna, tashi yayi ya tafi har ya kusa fita ya juyo in har baku kawo kudi ba,  nan da Awa uku zaku iya rasata yana gama fadin haka yayi ficewanshi, dukewa Ummu tayi ta saka ihu, "shikenan nasan mun rasaki Maryama ina zamu samu wannan kudin, dagota taji anyi Sumayya ce ta dago Mahaifiyan nata ta fara magana cikin Dakiya, "Ummu bazamu taba rasata ba zanje duk inda zani sai na nemo kudi a yau dinnan Nayi miki alkawari, da sauri ta juya tayi hanyar fita Office din, da sauri Ummu ta biyota tana kwala mata kira, ina ai ko waiwayota batayi ba tai gaba,,,,,,,,,!!!!



Kudai cigaba da bin alkalamin yar mutan zazzau yanxu aka fara wasa farin girki, shin Sumayya ina zata samo kudi har dubu sittin don yima yar uwanta aiki, to nima dai ban sani ba kubi ni sannu a hankali✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️



Share

Vote

Comment

Follow me on whatpad
ZainabSalihu933

More Comment more typing ✍️✍️✍️✍️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 13, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Labarin wata yarinya ce Jaruma da bata da tsoro Sumayya Where stories live. Discover now