JINSI BIYU page 1

20 2 1
                                    

*JINSI BIYU*

By Sajna.


1

Gudu ta ke sosai da dukkan k'arfin ta, burinta ta samu tsira daga gare su amma ina, cikin gudun nata tayi karo da wani abu wanda batasan menene shi ba sanadiyyar duhun dake cikin dajin.

  Hasken walk'iya ne ya hasko tsakiyar dajin, anan ne ta samu damar kallon abunda tayi karo dashi d'in.

Kyakkyawan matashi ne wanda zai kai shekaru talatin a duniya, fari ne tas kamar balarabe, yana tsaye cak bai yi ko alamun motsawa ba, ganin cewar sun tinkarota yasa ta saurin shigewa jikinsa ta ruk'unk'umeshi, wani xafi ta ji a jikin nasa kamar an tsamo shi daga tafashasshen ruwa, da sauri ta sake shi ta rakub'e a bayansa.

Isowarsu ke da wuya suka ganta bayansa atake suka fara ja da baya har sukayi nesa dashi sannan suka b'ace.

  Shi kuma a fusace ya juyo ya kalleta tare da cewa "keeeee!"

  A take ta saki fitsari cikin skirt dinta sanadiyyar muryar dataji me tsananin k'arfi da amsa kuwwa, dan duka dajin sai da ya amsa muryarsa.

A razane ta ja baya tana k'ank'ame hannuwanta a jikin ta, zuciyarta na bugawa da k'arfi, ya tako a hankali har inda take ya kamo hannayen ta ya zaro wani siririn zobe a k'aramin yatsar sa ya saka mata, daga nan ya b'ace b'at ya barta a wajen, tsoro da firgici suka kamata, ta rasa me zatayi, ta ina zata fara neman hanyar fita daga dajin nan? tana cikin wannan tunanin ruwan sama ya sauk'o me k'arfin gaske, ga sanyin ruwa, ga iska, ga duhu, haka take tsaye tsakiyar dajin nan har ruwan ya tsaya, bayan tsayawar ruwan ta fara ganin haske ya fara bayyana a sararin samaniya, alammun alfijir ya kusa, hakan yasa tafara lalub'en inda zata rakub'e zuwa wayewar gari, tana tsaka da neman ne sai ga wani kyakkyawan matashin daban da na d'azu ya bayyana a gareta, bayyi wata wata ba ya fincikota ya fizge zoben da wancan matashin yasaka mata, ya jefar dashi acikin ciyawi, yafizgeta da k'arfi, daganan idanunta suka rufe sai ji tayi an jibge ta a kan gadon ta.

Tanajin sautin tafiyarsa amma idanunta sun kasa bud'uwa, ga jikinta duk ya d'au zafi sanadiyyar ruwan saman da ya jibgeta.

Bata san yadda akayi ba sai salatin mahaifiyarta taji, ta bud'e idanuwanta a hankali ta kalli mahaifiyarta ta, mahaifiyarta tace "Sultana, na shiga uku na, wai me yake faruwa dake ne a kwanakin nan?"

   Ta kalli mahaifiyar ta ta hawaye na kwaranya daga idanunta tace "mami nah ban sani ba, bansan me ke shirin afkuwa dani ba, ni kaina kullum al'amarina k'ara rikita ni yake" ta k'arisa maganar cikin kuka.

Mami ta kalli 'yar ta cike da damuwa tace "ki bar kuka Sultaana, komai yayi zafi maganin sa Allah, ki tashi kiyi sallar asubahi kar lokaci ya wuce, kiyi gaggawan canza kayan nan kafun sanyi ya shiga jikin ki, bari in je kar a ta da sallah"

Sultaana ta mik'e da k'yar ta isa gaban wadrobe d'inta ta fito da wata doguwar riga jallabiya, tasaka tashiga toilet ta d'auro alwala ta nufi masallacin gidan.

Ana idar da sallar asubahi aka fara watsewa, yayin da ita da mahaifiyar ta ne suka saura a masallacin matan, a hankali ta tako zuwa inda mahaifiyarta take ta zauna a jikinta sukayi azkar d'insu tare, tadubi mahaifiyarta tace "Mami nah zazzab'i nake ji".

Mamin ta tab'a wuyanta taji zafi, tace "kai sannu, muje kisha magani ki kwanta muga zuwa safiya ko zai sauk'a"

  Suka wuce cikin gida Mami ta ba ta magunguna ta sha sannan ta kwanta.


Wannan somin tab'i ne daga cikin labarin, ina jiran comments d'inku, in naga dayawa xan cigaba tomorrow insha'allah.

08116952683
SAJNA CE

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 18, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JINSI BIYUWhere stories live. Discover now