02

674 16 1
                                    

SANADIN BOKO (P.2)
Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a
gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga
wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na
bata rai tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To
zabi wanda ki ke so."
Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne
da *yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da
kyar zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube
shi.
"Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi
muje". Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana".
Cikin daga sauti na ce, "To, to naji zan amsa,
amma ni na gane kamar zasu yimin kadan." Ya dan
sassauto "Muje gidanmu ki gwada." Da sauri nace,
"A'a zasu yi min."
Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka
shiga motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice
cream". Na ce, "A'a kai ni gida, Innarmu bata san
na fita ba, kuma nasan zata sa a leka ni, fada
kuma zata yi min". Ya ce, "To naji sarkin tsoro, ke
dai kawai kina tsoro ne kada na cinye ki."
Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a
dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga
Babana, ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki
wallahi. Shi yasa Dad din mu yake matukar burge
ni, baya takura mana, shi dai in dai zamuyi karatun
boko to duk abin da muka ga dama muyi. Kuma zai
kashe mana the last kudin shi don muyi karatu.
Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba,
amma ka fito ku gaisa.
Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na
nufi cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta
ce, "Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada
yaga lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um
asibiti muka je dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba
za ki fada ba? Kin san fadan Malam, don Allah ki
rufamin asiri kada ki ja min surutu sanadin bokon
nan."
Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu
yana shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo
muryarshi yana cewa.
"Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo
min manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar
gidan nan wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun
gama boko, to ban laminci wannan ba."
Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make
ni, ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko?
Inna ta ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya
zaburo tamkar zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji
wa? Wa ya fada miki?"
Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi
abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke,
duk ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai
ke?" Inna ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?"
Nace, "Kuyi hakuri, ba zan kara zuwa ba." Tayi
kwafa tare da ci gaba da yin aikinta. Baba ya ce
"To wallahi ba zan yarda da gantali ba, wai ku
*yan boko."
Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka.
Tunda ni na jajirce ki samu karatun boko." Na ce,
"Don Allah Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake
ba". Ta ce, "To me yasa ki ka min karya? Kin san
dai na tsani a min karya, duk abin da ya faru nafi
son gaskiya ko?" Na ce, "Na sani.
Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan
ta sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda
na bi saurayi wani guri.
Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai
Babane ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun
gidanmu na ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko
lafiya? Na jishi shiru. A bayan takardar ya rubuto
cewa Babana ya kore shi, don haka shi ya hakura
da ni. Na girgiza da jin wannan zancen, don ina
son shi kullum burina na aure shi. Shi kadai nake
jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi ko satar jiki zan
yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina cikin
damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce,
"Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira
goma a amsomin panadol."
Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya
*yar makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta
ce, "Kar ki zauna, maimakon kije tun ido na ganin
ido?" Na ce, "Ai dazun ciwon kai ke damuna." Ban
yi wata kwalliya ba, kada ta gane, sai kawai na dan
fesa turare. Na zari mayafi, gidan su Munnir da
dan tafiya tsakanin mu saboda mu muna Rigasa
ne Abuja Road ta kasa, su kuma suna Makarfi
Road.
Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga
motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara
sauri. Daidai ya bude motar zai shiga na ce,
"Munnir" Ya juyo da sauri, ya mai da motar ya
rufe. Abokin nasa yana ciki, ya ce, "Beby lafiya?"
Na jingina da motar, sannan na sauke ajiyar zuciya,
domin na gaji. Sai dai kuma lokacin ne naga rashin
hankalina.
Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko
nazo biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na
ce, "Ai ba ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce
"Dama nazo ne na maka godiya akan dawainiyar
da kayi da ni, don ko zamu rabu bai dace mu rabu
ba zumunci ba."
Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya
rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta
ni" Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka
motar yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki
kiji." Na ce, "A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan
gaddamar nan, ki daina kada muyi aure mu zo
muna samun matsala.
Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce,
"Ba za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya
tura Gate din gidan, muka shiga.
Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga
haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa
fita dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita.
Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin
gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau
kin zo gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki
kannena su Nana.
Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su
ganni cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da
nayi. Ya ce, "Shikenan.
Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa,
sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na
zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga
cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da
gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun
kujerar da nike.
Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya
mika min, na girgiza kai tare da cewa, "Na gode.
Ya ce, "Wasa ki ke yarinya, rike nan ko na dura
miki.
Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai
iya. Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na
kwace tare da mikewa.
"Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, "Dama ni banyi
fushi ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya
kashemin idonshi daya, nayi saurin kauda idona
saboda yarr din da tsigar jikina tayi.
Na ce, "Yaushe zaka zo? Ya ce, "Zauna to mu
tsara in da zamu dinga haduwa, don Babanku ya
ce in manyana ba su zo ba kada ya sake ganina.
Na ce, "Fada min daidai ina ne zamu dinga
tsayawa? Ya dan yi shiru, "To ni bansan yaya
zamu yi ba, na ce zan hada miki phone kin ce a
gida ba za a barki ba, wai ke ba ki da irin *yar
dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a silent.
Na ce, "Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na
marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na
lura yana son su. Mu bar maganar party din nan,
wallahi ba Babana ba har Innarmu in ta sani zan
bani, ka ji.
Ya tsare ni da manyan idanunsa.
"Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba "Ban san
me yasa gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena
su Nana da Suhaila Mom din mu da Dad din mu
sune suka shirya musu party din su last week.
Amma ku sai ana hana ku. Wannan duhun kai ne,
yanzu fa an waye.
Na ce "Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da
yake son ya yi ma *ya*yanshi. Ya ce "Shikenan
dai, mu bar maganar, naji nayi asarar kudina, kuma
ba wani gida ke ce dai ba ki ga dama ba.
Wani friend dina yarinyarshi itama *yar Geto ce,
amma ta jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo
muka yi shagali, amma ke kin kasa.
Na ce, "Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido,
sai kin yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki
hanyar fita, sai kawai naji ya rungume ni ta baya,
jikina ya dauki rawa.
Cikin rawar murya na ce, "Munnir la..la....lafiyarka?
Don Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi
sun canza, da sassarfa na fito na dau hanya. Ya
biyo ni da mota shi da abokinshi, wai na shiga su
kaini gida, na ce, "A'a don na tsorata, dole suka
bar ni.
Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya
min, dama an ce mace da namiji in suka kebe na
ukun shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir
ba, da tuni na bar shi.
Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake
tsayawa. Na fada ma Innarmu ta ce saboda me?
Na ce, Baba ya hana shi zuwa nan.
Inna ta ce, "Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da
Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace
wani abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama
kanki.
Na ce, "To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da
Munir ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba.
Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba
bai sani ba, Munir ne ya sai min form, sai dai
tsorona daya randa Baba zai sani.
Na zama cikin sa'a kamar ko yaushe, Munir ya
tsaya tsayin daka har na samu gurbin karatu a
(B.U.K) Kano, sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na
ce ma Innarmu, ta ce yau na yanke shawarar sanar
da shi komai, tunda gobe za ku je yin rijista.
Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar
Innarmu nake ji tar daga dakin Baba, domin
bangonsu daya. Tana sanar da Babanmu komai.
Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, "To bokon
nan ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na
hakura tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take
so ko duniya?
Inna ta ce, "Duka. Ya ce, "Karya ne, duniya ku ke
nema, kuma ga ku gata nan. Jami'ar da aka ce
*ya*ya suna lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki
sama da shekaru amma baki damu ba. To magana
ta ni uku ce, bata kai hudu ba.
Na farko duk abin da ya faru da ita sanadin boko
ba ruwana, zai shafe ki ne da ita.
Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba,
matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin
da Allah Ya dora min.
Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi
mijinki, duk ranar da wata ashsha ta samu sanadin
boko.
Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba
kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo
kusa dani ta zauna.
Tasa hannu ta dan dake ni, "Tashi Hafsatu.
Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce "Nasan
kin ji duk zancen da Malam yake yi ko?
Na ce, "Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce,
"Insha Allahu Malam karatun Hafsa zai zama
alkhairi garemu da kai gaba daya.
Ya ce "Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake
magana. Babah ta ce, " Hafsatu ki bar Babanki yayi
iko da ke, ki ce ma Innarku kin fasa karatu.
Kalamanshi ba baki yayi miki ba, amma ina ji miki
tsoron alhakinshi kada ya kama ki.
Na ce, "Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba
yanzu zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su
yarda ya auri mara ilimi ba.
Babah ta ce, "Sai shi? Akwai masu sonki da yawa,
kuma sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina
nazari, nasan Babah gaskiya ta fada min, amma ya
zan yi da son Munnir?
Na dube ta, "Babah ki duba irin hidimar da Munnir
yake yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba
zan jirashi ba. Ta ce, "To yanda ki ka gani, amma
karatun nan tunda ba na Muhammadiyya ba ne,
banga dalilin naci ba.
Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki
yake yi. Anya auranki zai yi? Na ce, "Allah Babah
aurena zai yi, ki dubi dadewar mu da hidimar da
yake min.
Ta ce, "Ba ta a nan, amma fa shawara ce." Na
koma na kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin
dakinta.
Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya
da ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni
ba. Nayi guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta
dawainiya da ni ba zai aure ni ba?
Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata
Mahaifana biyu ma haka ne, duk sanadin boko. Da
safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi
na kasa sha, Innarmu ma sukuku take.
Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan
alalarta manja, na ce "Inna ko dai zamu hakura da
batun bokon nan ne?
Ta dube ni, "Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce,
"Naji duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru,
can ta ce, "Abu daya zuwa biyu nike so ki min.
Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da
mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu
kiyi abin da ya kai ki makaranta, wato karatunki
wanda nike fata ya zama sanadin alkhairi.
Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da
ya yi wa boko, har kannanki suma su samu dama
suyi cikin kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu
damar ci gaba ba yana jin haushi.
Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na
hada ki da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu
ya cika ni, na ce, "Insha Allahu zan kula sosai,
kuma zan fidda ki kunya, sanadin bokon nan kowa
zai huta, Baba zai yi alfahari da ni.
Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a
jami'ar Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi
Innarmu bata daina rokona in rufa mata asiri in
lura da kaina ba.
Nan na tafi na barta da surutun *yan gidanmu, da
*yan unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri
mai kudi, shi yasa muka nace boko, wasu su ce
dan kyan nawa bai fi cikin cokali ba, amma mun
kuke sai nayi boko.
Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta
toshe kunne watan kwaram daya ne. Baba har
fushi yayi da ita, sun jima kafin ya soma amsa
gaisuwarta.
Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon
su bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba
shi hakuri suka ce wai karatun yana da amfani.
Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a'a tayi shi
can gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta,
sai suka ce ya yi hakuri *yan kwanaki ne zata
gama, don haka sai ya dawo ya zura mana ido.
Ehemmmm anya kuwa?????? Ni dai ba ruwana ehe,
ku in fada?

SANADIN BOKO Where stories live. Discover now