25

504 12 0
                                    

SANADIN.......BOKO

-Lamido ya yi sanyi, ya ce to zai gana da
'ya'yanshi, in ya so za'a bincika aji asalinta.
Amma fa sai dai in ya yarda ya hada mata biyu,
domin ba za'a fasa Fadi ba.
Liman ya ce, "Wannan ba laifi ba ne." Lamido ya
kuma tara 'ya'yansa ya gaya musu cewa,
sakamakon zuwan da Liman ya yi yayi masa
bayanai da dama akan wannan lamari, dan haka
ya nada Baffa sa'adu da su binciko masa 'yar
wane ne? Sannan ya ce da Abba in yaje gida ya
turo masa Abubakar.
Ko da Abba ya dawo gida bai samu Abubakar ba,
sannan duk wayoyinsa a kashe suke, ya kira
Hashim yake gaya masa in ya ga Abubakar ya
fada masa Lamido yana neman sa. Tare suka je
gurin Lamido ya ce, "Hakika kana da sa'a, zan
amince da auren in naji cewa Iyayenta masu
mutunci ne, itama 'yar mutunci ce. Sannan kuma
in ka yarda ka hadasu 2 ka auri Fadi itama.
Sannan ita yarinyar tunda bakuwa ce anan gida na
zaka kawota mu zauna da ita muga irin nata
dabi'un." Har zai ce wani abu sai Hashim ya
zungure shi, sannan ya ce ya amince. Lamido ya
ce, "Shi bashi da baki ne sai kai?" Sannan
Abubakar ya ce, "Na amince." Lamido ya ce, "To
sai kuje, in mun shawarta lokacin da za'a je zaka
ji."
Farin ciki gurin Abubakar baya misaltuwa, ya isa
gidansu da karfin gwiwa. Dada tana zaune suna
hirarsu da Rukayya, ya zube gabanta yana neman
gafararta, sun ji komai daga bakin Abba, sai dai ta
ce, "Shawara daya zan baka, kada ka yi rawar jiki
akan bakuwar da zaka kawo cikinmu, ka nuna
kamar kafi son 'yar uwarka a kanta, ka tashi mun
yafe maka. Ka samu Abba ka bashi hakuri, sannan
ka samu Hashim ku je gurin Fadi." Ya ce, "To."
Ummi cikin murna ta ce, "Ni kam in zaka Kano zan
bika muje na ga Hafsat." Ya ce, "To, Amma sai na
fara zuwa in na dawo sai muje tare."
Shi da Hashim suka nufi gidan Goggo Jami, sun
jero ita da Fadi zasu fita, hannun Fadi rike da
makullin mota, sai ga Abubakar. Suka tsaya Goggo
da fara'a ta ce su shiga. Fadi ta musu sannu da
zuwa, suka gaisa sannan Goggo ta koma ciki tasa
a kawo musu abin sha duk da cewa da safe ne.
Fadi ta gaishe su, Hashim ne ya ce, "To Fadima,
kin san dai dalilin zuwanmu tunda magana ta yi
nisa, yanzun ma yana kan hanyar tafiya ne muka
biyo. In ya dawo zamu zo zuwa na musamman."
Ta ce, "OH, zashi gurin KISHIYATA ko? In kaje ka
gaidata." Ta mike, "Nima zan je office ne." Suka
mike suma, Abubakar bai yi magana ba, Hashim ne
ma ya mata sallama. Suna hanya inda Hashim
zaya kai shi filin jirgi don zuwa Kano. Ya ce, "Kuna
ta fadin Fadi nada mutunci, dubi irin tarbar da tayi
mana." Hashim ya ce, "Kishi ne, taga kowa a
family ita daya ake aure, amma ita su 2, dole ta
damu." Abubakar ya ce, "Ummi fa dole ta tsani
auren Fadi, saboda ita bata da kirki, da ace ina da
yanda zan yi to ba zan auri Fadin ba." Hashim ya
ce, "Na kula ai da zaka yiwa Lamido musu ne,
shiya sa nayi saurin amsawa." Haka suka yita hira
har ya kaishi filin jirgi, yau dai da farin ciki ya nufi
Kano, kuma baya jin zai samu matsala da Hafsat

SANADIN BOKO Where stories live. Discover now