page two

27 1 0
                                    

UMMU AIMAAN ALIYU shine ainihin sunanta mahaifinta mlm Aliyu ya kasance dan garin Katsina a karamar hukumar kankia, su biyu kawai mahaifan sa suka haifi dashi da yar kwanwar shi Hafsah wacce yake matukar so bayan Allah ya yi wa iyayen su rasuwa ta hanyar accident gurin halartar taron bikin abokinsa a cikin garin Katsina yayinda Aliyu da Hafsah suke makarantar islamiyya, bayan sun dawo suka tadda mummunan labari haka sukayi ta kuku har suka godema Allah.

Basu da wurin zuwa sai wannan gidan da iyayensu suka bar musu alokacin Aliyu zai shiga ss1 a makarantar boko yayin da Hafsah zata shiga jss1 akan dole Aliyu ya hakura da makarantar ya shiga harkar kasuwanci domin taimakawa yar uwarsa ta samu ingantaccen ilimi, ahaka rayuwa ta dinga gangara wa har Hafsah ta gama secondary school allah ya haɗa ta da wani bawan Allah mai sonta tsakani da Allah ya aure ta, bayan auren ta da wata biyar ta matsama ƴaƴan nata daya daure yayi aure shima ya samu natsuwa.

Ana haka wata rana yaje kasuwa ya haɗu da wata kyakkyawar yar Fulani mai tallan nono atake ya kamu da sonta kuma yanuna yana son auren ta ba bata lokaci ya samu iyayenta dayake masu nagarta ne suka bashi ko ba komai ƙabilar su daya.

#vote
#comment
#share

UMMU AIMAANWhere stories live. Discover now