Cigaban labarin
Gosh! Dafe kanta tayi tama rasa ta ina zata fara kawai sai ta fita harabar asibitin ta tari mai napep ya kaita gida dan ta sanar da abbin ta domin ba waya a hannunta, cikin sauri tace mai napep dan Allah jira ni yanzu zan fito yace to Hajiya gudu-gudu ta shiga gidan tana Ammi kina ina, ina Abbi gwaggo na asibiti bata da lafiya ban fita da waya ba balle na fada miki salallami ta fara tace barin fada ma Abbin ku tayi maza da shiga dakin shi tana fada mai sakon.
Cikin sauri ya fito hula a hannu ya fita gidan aimaan da Ammi suka mara mashi baya Allah yasa ta tsayar da mai napep din da sauri suka shiga suna jiran Ammi ta rufe gidan su twins ma basu nan suna makarantar zaure inda areef yake zuwa.
Suna isa asibitin doctor na fitowa daga room din, yana ganin su yace kune yan uwan ta suka eh sai yace Abbi ya bishi office dinshi, doctor na zama ya ce ina mijin ta Abbi yace baya nan yayi tafiyar amma muna tsammanin yau zai dawo sai yace okay, sai doctor yace yar uwar ta samu heart attach sakamakon wani abu da taji ya daga mata hankali amma mun shawo kan matsalan in Sha Allah she's safe, ajiyar zuciya Abbi ya sauke yana furta allhamdulilah tare ma doctor godiya ya fita, yanayin fuskar Abbi ya tabbatar masu da cewa komai lafiya kuma an shawo matsalar bayan ya musu bayani yace yanzu ke Ammin aimaan kije gida ki dafa abinci ni kuma zani gidan Hafsah naga ko mijin ya dawo ko kuma areef mu masu bayani ta amsa da toh aimaan kuma ki zauna idan ana bukatar wani abu ki kira ni.
Tana zaune jigum sai ga areef nan ya shigo hankalin shi a tashe yana tambayar ina mahaifiyar sa, shin tana lfy, wani abu bai zame ta ba koh, haka ya jera ma aimaan tambayoyin nan ita ko kallan sa ta tsaya yi ta rasa wanne zata amsa masa, kawai sai tace ka tafi wurin doctor zai ma bayani.
#vote
#comment
#share