INA MAFITA?
02SHATUUU❤️
One love💞
Lodge road, Kano.
Cikin sauri Anie ta fito daga dakinta hannunta rike da links tayi wani bedroom dake can gefe da nata. Knocking tayi hadi da sallama kafin ta tura kofar ta shiga. Gaban gadon da wani dattijon wanda a kalla ya tasar ma 60years zuwa sama ke zaune ya tattara dukkan hankalinshi akan TVn dake aiki a tashar Channels. Tana shigowa ya dago ya kalleta sannan ya maida kanshi ya cigaba da abinda yake. Itama gefenshi taje ta zauna tare da kama hannunshi ta fara zura link din sannan tace
"Honorable lokaci na tafiya kada ka makara"
Mikewa yayi bawai dan yaso ba se dan abinda ta fada gaskiya ne yace
"Sure, se jibi inshaaa Allah"
Kanta ta gyada tareda gyara masa zaman babbar rigar shi tace
"Safe flight my dear"
Hannunta ya rike tareda pecking dinshi wanda yasa tayi blushing yace
"Allah yasa"
Daga haka suka fito bayan ta dakko masa back pack dinsa wadda yan kayayya yakin shi suke ciki. Suna dan magana har suka sakko downstairs. Gida ne wanda kana kallonshi kaga gidan multimillionaire, komai ka kalla se ka kara kallonshi saboda yadda yake numfashi on its own. Kallon wani staircase yayi dake gefe da wanda suka sakko sannan ya juyo ya dubi matar tashi yace
"Ya Ammar kuwa?"
Dan murmushi tayi tace
"He must be sleeping nasan, zance masa ka wuce idan ya sakko"
Kanshi ya gurgiza yace
"Bari na ganshi dai"
Tare suka nufi staircase din har suka isa dakinshi, dakin yayi sanyi karara saboda ACn da aka kure, yana kwance ya kudundune cikin duvet. A haka iyayenshi suka karasa kowanne ya zauna suka sashi a tsakiya, shikam baccinshi yake ba tareda yasan da wanzuwar su ba. Anie ta yaye fuskarshi banda glowing babu abinda take, Papa ya bashi peck a goshi sannan ya aje masa envelope akan bedside drawer kafin suka sauka zuciyoyinsu cikeda tsantsar soyayyar dansu.
Jakar shi ta mika masa ya karba sannan sukai sallama ya fice, ta dade a tsaye tana kallon part din Ammar kafin ta girgiza kanta ta wuce kitchen dan bata san dan lelen nata ya tashi baa hada masa breakfast ba. Tana shiga Zainab ta tsugunna ta gaida ta, babu wani sakin fuska ta amsa sannan tace
"Ina breakfast din Ammar?"
Towel ta janyo ta goge hannunta sannan ta matsa can kan kitchen island ta dakko shiryeyen tray da aka rufa masa wani farin cotton material akai, matsawa Anie tayi ta yaye shi bowl din farka pepper-soup din kayan ciki ne, se irish french fries da tea da kayan tea. Rufewa tayi tace
"Ina porridge din?"
Kanta ta dan sosa tace
"Ya kare ne ingredients din"
Ranta ya baci tace
"Se yanzun zaki fada min kice ya kare?"
Zainab dai batayi magana ba se da Anie ta gama banbaminta kamar ko da yaushe sannan Zainab da kanta yake a duke tace
"Kiyi hakuri dan Allah"
Tsaki tayi ta fice kai Zainab ta dafe tareda sauke ajiyar zuciya tace
"Kullum a haka ake"
Daga haka Ta cigaba da aikinta, halayen Anie babu wanda bata sani ba matsawar akan wancan watsetsen dan nata ne wanda ita kanta da matsayinta yake a cook dinshi tasan ta fishi future.
YOU ARE READING
INA MAFITA?
General FictionIna mafita? Labari ne fictional da zaiyi duba akan zamantakewar mu a gidan aure. Matsalolin da suke damun ma'aurata. Shatuuu