07

402 85 6
                                    

INA MAFITA?
07

Zaune ta sameshi shi da Najwa suna shan juice, Juwairiyya na shigowa Najwa ta fara tari saboda kwarewar da tayi, da sauri ta mike tareda barin gurin tana ta tari, ko kallonta Juwairiyya batayi ba se maitama ne ya mike shima yana fadin
"Careful! Are you ok?"
Kanta ta gyada tana ajiyar zuciya  bayan ta shanye ruwan da ta ciro daga fridge, ficewa tayi ba tareda tace komai ba. Shima bai bi ta kanta ba se ya maida hankalinsa kan Juwairiyya. Seda ta shafe mintina arba'in ana abu daya kafin ta samu suka tafi hankalinta a kwance Allah ya yarda ta kammalla da thesis dinnan se kuma a dauki wani abin.
Khauthar na tsaye jikin mota ta same ta, da tsananin murna ta nufe ta tare da rungume ta tace
"I'm done sis!"
Wani hug itama Khauthar ta bata tace
"I'm proud of you Adda, Allah ya taimaka"
Amin ta amsa sannan suka shiga cikin motar, wannan karan Juwairiyya ce ta karba driving din cikin murna. Har tayi mata key tana kokarin barin gurin wajen ta hango Najwa na tsayar da ita, sun riga da sun hada idanu if not bazata tsaya ba. Karasowa tayi ta tsaya jikin window tace
"Anty Barka da rana"
"Barka dai najwa ya karatu?"
"Alhamdulillah"
Ta bata amasa sannan tace
"Gida zakije ne?"
Kanta ta gyada mata daga haka ta mata sallama ta wuce ta a gurin. Suna tafe Khauthar tace
"Adda ina kika samo wannan kuma?"
Dan tsaki Juwairiyya tayi tace
"Anan na samo ta wajen Maitama, like inaga budurwar shi ce"
In exclamation tace
"This young girl! Maitama supervisor dinki? Wannan tsohon"
Yadda tayi maganar in one breath yasa dole Juwairiyya tayi dariya tace
"Ke meye naki wai? Kiji yadda kike magana kamar wata uwarta"
Kai Khauthar ta girgiza tace
"Bazaki gane ba amma dai Allah dai ya kyauta"
Sukai shiru se can kuma Khauthar tace
"Nikam Adda banga kina wani daukin bikin nan ba, tunda kukai maganar da Daddy ban kara jin kinyi maganar ba, ko kin daina son shi ne"
Kai ta girgiza tace
"Bazaki gane ba Khauthar, ina son shi mana do I've to even mention it. Kawia dai inaji wani weirdness a tare dani"
Kafin Khauthar tayi magana sega kiran Imran na shigowa hakan yasa Khauthar tayi saurin picking tareda karawa a kunnenta tace
"In-law"
Daga dayan bangaren Imran yace
"In-law sis, yakike? Kamar kuna hanya"
"Eh Adda taje submitting thesis dinta amma muna komawa gida, she's driving idan muakje she'll call"
Sallama yayi mata sannan ta dubi Juwairiyya da dukkan hankalinta yake kan titi, unlike da da zata ta balai akan anyi picking call din Imran amma yanzun batace komai ba as if bashi bane ya kira ba.
"Adda kunada issues keda inlaw dina ne?"
Kallonta tayi se kuma ta maida kallonta kan titi tace
"Amma Kinsan you're annoying? Yanzun muka gama maganar nan dake fa, it's nothing"
Da damuwa Khauthar tace
"Ba haka kike ba, da dane zakiyi ta doki idan ya kira amma yanzun ya kira ko sparing ma wayar second glance ba kiyi ba"
Juwairiyya batace mata komai ba suka cigaba da tafiya, itama Khauthar se ta bar zancen kawai. Suna isa gida sun ringa da sunsan Mamaa da Daddy basu nan sunje gombe so kawai se suka Zauna nan parlo dan yin lunch kasancewar har one ta gota. Anan aka musu serving abinci suka ci sannan suka haura sama. Khauthar ta zauna parlon ita kuma ta shige bedroom dinsu. Kayanta ta rage sannan ta tuna Imran ya kirata, da sauri ta janyo wayar ta Fara kiranshi amma har ta gama ringing baiyi picking ba, se kawai ta hakura tareda tunanin kilan yana wani abinne. Bata gama tunanin da take ba kuwan se gashi ya kira.
"Sahiba!"
Sai taji a hankali kamar anyi awakening zuciyarta da soul dinta akan sonshi, wannan sahibar means a lot a wajenta.
"Sahibi barka da rana!"
"Barkanki. Ya mutanen gidan?"
"Kowa yana lafiya, ya Ummiey?"
"Tana lafiya, she said na tambayeki favorites dinki zaa fara hada lefe"
Shiru Juwairiyya tayi ta rasa me zatace ma se kawai tace
"You please contact Khauthar about that"
Cokin gamsuwa ya amince da hakan, then se kuma aka fara hiran which was all about love.
"Baby, kinsan yadda nake jin kamar na janyo 3 months dinnan suzo na ganki kullum a gabana? Bakida idea how much you mean to me wallahi"
Idonta ta limshe babu shiri tayiwa kanta masauki akan gadon tareda kanke wayar a kunnenta sede duk yadda tayi kokarin ta furta wani abun she couldn't se kawai ta kasa kunnenta tana sauraren words dinta that are so enticing and loving. Sunfi awa suna hira kafin sukai sallama anan kwancen bacci yayi gaba da ita, laasar Khauthar ta shigo ta tashe ta sukai sallah.
Sallamar Luba yasa su kallon kofa tareda bata izinin shigowa. Shigowa tayi hannunta dauke da kaya neatly washed, ironed and folded. Straight dressing room dinsu ta wuce ta jerasu neatly sannan ta fito. Khauthar ta dube ta tace
"Luba kunyi kunun ayan?"
Kai ta gyada tace
"A kawo?"
"Eh"
Tace sanann ta maida hankalinta kan kallon da suke wanda ita daya kawai take ganewa amma mutuniyar dake gefenta bata gane komai illa kawai kallon take. Baa wani jima ba sega luba da hajara sun dawo dauke da tray kowanne da glass jug da tumbler daya. Daya yayi sanyi karara yayinda dayan kuma babu sanyi sosae saffa saffa. Me sanyin Khauthar ta karba ita kuma Juwairiyya ta karba dayan, no matter zafin da ake bata shan abu me sanyi shiyasa komai ana gamawa kafin ayi refrigerating dinshi zaa kawo mata, ko ice cream bata sha.
Se wajen tara su Mamaa suka dawo, dama su Khauthar tunda sukai ishai suka sakko dan tarbarsu. Suna dawowa kuwan suka raka su part dinsu sukai sallama suka wice part dinsu.

Anie na zaune gefen Ammar da dawowarshi kenan daga yawo, jikinshi yayi sauki dama irin abinnan ne na baa saba ba.
"Ammar kasan illar alcoholism kuwa? Kasan menene matsalar shan giya?"
"Wai Anie wayace miki giya nasha ne, for goodness sake zargina kikeyi kuma?"
"Wanne zargi kuma Ammar? Ni fa na haifeka ta yaya zaka cemin wai baka shan giya bayan Dr Mansur yayi testifying da kanshi?"
Kwanciya yayi tareda juya mata baya, hakan da yayi ya tabbatar mata bazai kara cewa komai ba, se tayi shiru kawai gaba daya jikinta yayi sanyi. Can se ta mike ta sauka yana jin ta fita cikin sauri ya dakko kwalbar daya boye ya daga kanshi ya tuttila yana jin tamkar he don't exist a duniyar mu but in another planet.
Zainab ta gama shiryawa tsaf ta fito tareda tareda lekawa dakin masu aikin gidan da suka gama aiki suna hutawa, sallama tayi musu sunata mata Allah ya kiyaye sannan ta nifi bangaren Anie. A parlor ta taddata ta zabga tagumi, seda tayi sallama wajen sau uku kafin ta amsa mata. Shigowa tayi tace
"Anie Zan tafi se yamma zan dawo"
Kai Anie ta gyada tace
"Allah ya kiyaye hanya, ki gaida mutanen gidan"
Kai ta guada ta fice tana jin wani fresh air datake shigarata tabbas wanda yabar gida gida ya barshi. Kullum dare se taji kewar gida, dukda dakin da take ko a gidan aure bata tunanin zata samu kamarshi amma dukda haka tana jin babu kamar ya gidansu. Ba karamin kwaso ta akai da mahaifinta ba kafin ya amince ta taho gidan senator. Mahaifinta talaka ne amma zuciyar shi ta jajircece mutmum ce, su shida ne a gurin shi, itace ta uku kuma ita kadai tayi karatu a cikinsu dan sauran na saman nata duk aure sukai ko secondary basu gama ba, itace ta kammalla tayi diploma akan food and nutrition sannan tayi catering services dinta. Shi ne ta samu aka kaita gidan senator matsayin cook din Ammar.

Ayshatuuuu

INA MAFITA?  Where stories live. Discover now