PAGE 1
ORIGINAL VERSION
**Married in school,single at home**
Labarin Nuzlah da Amir.
Amarya ce zaune me make-up ta gama aikin ta,halittan nan ta fito rass da ita sai dai mu ce masha Allah.
Hada-hadar biki ake ta kowane angle,murna da farin ciki kam ba'a magana.
Nuzlah ce zaune tasha ado na ban mamaki ga wani shegen leshi an mata d'inkin fitted gown ya zauna daram a jikin ta,amma da kaga fuskan ta babu walwala.
"Nuzlah wai kekam baki gajiya da kuka ne???ke kika ce kina son auren nan fa,da yardarki za'ayi shi,mene ne abin k'unci?idan har ba zaman munufurci dake ba to ya kamata yau dai ki fad'a min abin dake saki k'unci ko kuma wallahi na fad'awa Ummah".
Zaro ido Nuzlah tayi tana kallon k'awarta Hafsat ."Hafsat ina cikin damuwa ,Hafsat da zan iya fad'a da na fad'a miki komai wallahi,Hafsat ina da mummunan labari".
Na sani Nuzlah amma aure zaki yi baki da aminiyar data wuce ni,ya kamata ki fadi min komai ni abokiyar kukan ki ce da farin ciki,idan kin yarda ki bani hannunki muyi alk'awari sirrinki nawa ne.
Nuzlah ta juyo ta fuskanci hafsat gami da mik'a mata hannu "Hafcy taho muje boys quarters nan da hayaniya".
A tsanake suke tafiya kowa ya gansu sai sam barka dan sunyi kyau matuk'a.Nuzla na zama a bakin gado ta dubi Hafsat
"Hafcy zan baki labarin da ban ta'ba fad'a wa kowa ba amma dan Allah ki min alk'awarin sirri na naki ne sannan baza ki guje ni ba"."Na miki alk'awari Nuzlah"
Hmmm Nuzlah ta sauke ajiyar zuciya.
LABARINAH
Hafcy kar kiyi judging dina ki jira in baki labarina,kar kiga laifi na k'addara na kan kowa.........
Shiru Nuzlah tayi tana sauke siraran hawaye.
Bayan 'yan mintuna ta fara..........Ko kinsan shekaru hud'u da nayi a jami'a tare da saurayi na nayi su?
Ko kinsan gidan mu d'aya ni ce MATAR AURENSA?
Duk rayuwar MATAN AURE ita nake yi?
Hafcy ni MATAR AURE ce a makaranta kad'ai?
Hafcy ko kinsan na haihu a titi?Hawaye ne ke kokawar sauk'owa daga fuskar ta .
Hafcy ma data gama rud'ewa ita ma hawaye ta fara duk ta rikice,mamaki ne ya cika zuciyar ta.Wannan shine "married in school and single at home".
Pages na farko are kinda short-short pages,lokacin daya fara dad'i yawan ya k'aru.
Labarin da ilimintarwa musamman ga mata iyayenmu damu kanmu matasa.
Labarin da ban tausayi.
Labarin da al-ajabi.
Labarin da koyon rayuwa da darussa.
Ku biyo Lauratu Abubakar a MATAR AURENA .
![](https://img.wattpad.com/cover/208924220-288-k312090.jpg)