BABBAN GORO 3

36 5 0
                                    

          BANBAN GORO....

Sadaukarwa ga mahaifinah.
Allah yajikanka baba nah!!!!!

         Washegarin komawarsu gidan gwamnati, ya Ashiryawa gyatumar shi tafiya da Imam wani asibitin kashi a kasar Indian, garin Punjabi.
Bayan ya yi magana da hukumar asibitin ta yanar gizo (internet) suka tashi ranar asabar, inda Imam (Al'mustapha), ya soma karbar treatment daga kwararrun likitocin kashi.
    Shikin sati biyu ya warke ragas suka dawo gida Najeriya, kowa na murna da samun lafiyar Imam, kasancewarsa yaro mai Shiga rai, babu wanda xaikali Al'mustapha bai ce yana son sa ba.
         Bayan kyau tsurar sa, da Allah Ya halicce shi dashi. Wani irin haxikin yaro ne mai kwarjini da kuxari hade da nutsuwa ta banmamaki. Haj. Zainab ta dauki kaunar duniya ta daura akan marayun nan da maigidanta ya damka mata amanarsu. Bata taba haihuwa ba, a tsayin shekarunsu ashirin da aure. In har suna da masala  a rayuwarsu toh wannan ce.
  Anyi jelen asibitin, anyi na gargajiyar shuru har yau. Don haka suka dauki komai suka mikawa Allah. Wanda ba'a sa shi, kuma ba'a hanashi. Shine mai bayarwa da hanawa ga wanda ya so. Don likitoci sun tabbatar musu kowannensu lafiyarshi lau, lokaci ne Allah bai kawo ba.
   Akwai aminci na hakika tsakanin Haj. Zainab da marigayiya Haj. Kaltume. Basu san wata kalma wai ita 'faccalanci' ba da matan hausawa ke yi, musamman idan mijin wannan yafi na waccan, duk da ratar arziki mai yawa take sakanin Zubairu da Aliko a lokacin da suka aure su.
   Don haka su Imam tuni sun saba da Haj. Zainab da kawunsu Alh. Aliko, don a kan kawosu hutu wajensu lokacin da iyayensu na raye.
Don haka ne da Imam da shahida suka saba da Uncle dinsu da Haj. Zainab, sai basu damu sosai ba. Sai dai jefi-jefi Imam da yafi wayo kan tanbayi Haj. Zainab Mummy da Daddy.
  Ta kan ce sun je kano sai hutu ya kare za so zo su dauke su. Ita shahida da yake karama ce ko ambaton iyayen ba ta yi, wasanta kawai take da 'toys' da 'teddies' da aka cika mata godonta dasu ba abinda ya dameta.
   Alh. Aliko dauka gyatumarshi Haj. Mama daga unguwar Rimi (gidanta da Alh. Zubair ya gina mata) ya dawo da ita Government House, sassa guda aka ware mata, babu abinda babu na jin dadin rayuwar duniya, babu ce kurum babu. Kun san dai tsari irin na gidan Gwanmnati.

       Mukinshi mulki ne mai cike da takawa (wato tsoron Allah) tsatseni (da dukiyar al'ummah) da tausayin talakawa.
      A shekara daya kacal da ya yi yana mulkin jihar Kaduna da local governments dinta (kananan hukumomin) guda ashirin da uku, ya kawo sauye sauye na ci gaba da dama, musamman ta fuskar tsaro da kariyar lafiyar al'umma.
       Ya tsayawa malaman makaranta ta hanyar kara inganta albashin su, da basu rancen motoci adinga diba da kadan da kadan daga albashinsu.
     Haka ya tsayawa iyayenmu 'yan fansho (pension) tare da taimako ta hanyar bada kayan aiki ga makarantun firamare da sakandire na jihar Kaduna.
   Bai tsaya a nan ba, gwamnatinsa ta tsaya-tsayin daka kan wutar lantarki da ruwan sha, wadanda sune manyan matsalolin da jihar ke fuskanta. Haka ya taka muhimmiyar rawa a kan harkar ilimin manya ( adult education) a jihar bakidayanta, da karo karatun malamai na jami'a dana sakandire a kasashen ketare ta hanyar daukar nauyin karatun da 'accommodation' da baiwa mata sana'o'I da tirenin akan sana'ar, haka matasan da basu samu damar yin ilimin zamani ba.
       Kan ka ce meye wannan? Ya zamo zakaran gwajin dafi shikin gwomnonin Najeriya tsararrakinsa, sannan abin koyi, kuma abin so a zukatan al'ummar jihar, sai fata daga bakunan al'ummar jihar, sai fatan alheri ga gwamnatinsa.
       Wadanda suka san masalarshi ta cikin gida kuwa (wato  rashin haihuwa) sai addu'a suke masa Allah ya ba shi magajin kyawawan halayensa.
       A wurin shi kuwa, bai tsanantawa kansa kan rashin haihuwa ba. 'Ya'yan dan uwansa sun isheshi, har gaba da abada in akwai 'ya'ya ne a gareshi da yake so fiye da 'ya'yan da zasu kasanshe shi ya haifesu. Wato Imam da Shahidah. Fatansa Allah ya raya masa su cikin tarbiyyar Islam ameen.


#vote
#comment

@fauxeekhan

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 21, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BABBAN GORO Where stories live. Discover now