Babban Goro....2

62 1 0
                                    

         Babban Goro......

Alh. Aliko ya tsame hannu daga abinci ya soma salati yana fadin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"
Itama Haj. Zainab salatin take yi. Suka mike a tare suka fito harabar gidan. Direba da masu tsaron lafiyarsa suka fito da mota suka Shiga, a daren suka dauki hanyar Zaria.
  Da suka iso basu sha wahalar samun kwamishinan 'yan sanda ba. Nan da nan yayi musu jagora zuwa dakin da suke. Ya dubi tilon dan uwansa ministan FCT zubairu Dan kasa, ko'ina a jikinsa jini ne, bandeji ne plasta ce, yana numfashi da taimakon abin janyo numfashi.
   Daga shi har matarsa Haj. Kaltume cikin yanayi daya suke. A gefe yaransu Al~mustapha da ake kira (imam) da kanwanshi shahidah ne suke ta kuka.
Al~mustapha da plasta a kansa da karaya a hannun dama, ita kuwa shahidah abin mamaki ko kwarzane batayiba, amma hakan bai hana ta kuka ba, musamman ganin iyayenta duk a kwance cikin wani hali duk da kankantar shekarun ta.
    Suna shiga Alhj. Aliko ya karasa ga dan'uwansa hawaye na zuba a idonsa, yayin da Hajiya zainab ta nufi su Al~mustapha tana rarrashin su. Ta kama shahidah ta rungume tare da shafa kan imam tana rarrashisa.
       Ko minti goma basu yi da shigowa ba Haj. Kaltume ta cika. Washegari da asuba shima Alh. Zubairu yace ga garinku nan.

   Tashin hankalin da mai girma gwamna Aliko Dan kasa ya samu kansa a ciki, ya mantar da shi farin cikin da yake ciki bakidaya.
Dan uwansa tilo da ya rage masa duk fadin duniya, yau ya tafi ya barshi. Abokin shawararsa kwaya daya rak, a duniya, su fadi tare, su tashi tare, yau babu shi. Kai shi da za'akwace mukin a dawo masa da yayan sa zubairu, da yafi farin ciki. Kuka yake wiwi da shi da mai dakinsa.
       Gari na wayewa aka shiga watsa mutuwar FCT minister zubairu dan kasa a kafafen yada labarai. Da motar asibiti aka dauko gawarwakin zuwa ainahin gidan mahaifinsu, inda mahaifiyarsu take zaune a unguwar Rimi.
          Jama'a suka shiga tittudowa domin halartar jana'izar maxan jiya, wadanda tarihin Najeriya bazai taba mantawa dasu ba, tun bayan rushewar mulkin soja (return to civil rule), wadanda suka taimakawa Najeriya ta kawo matsayin da take kai a yau: (from agrarian to industrial) irin su minister zubair Dan Kasa. Nan mai girma gwamna ya zauna karbar gaisuwa, yayin da Haj. Zainab ke tare da su Imam a asibiti.

      Haj. Maama, tsohuwa ba tukuf ba, wadda ta kasanshe mahaifiya ga Alhj. Aliko da Alhj. Zubair, wadda samu kulawar 'ya'ya nagari ya boye zahirin shekarun ta, ta sha kuka har ta gode Allah. Sai dai da yeke mace ce ma'abociyar imani da rikon addini, cikin kwanaki uku da rasuwar babban dan nata da mai dakinsa ta dawo cikin nutsuwarta. Tana amsa gaisuwar kowa. Saidai bata umh bata umh-umh, sai jan carbin dake hannun ta, sai kuma in an yi mata ta'aziyyah ta amsa.
      Da ganin mai girma gwamna Alh. Aliko Dan Kasa, ka san ya mutuwar ta bege shi yadda ba a zato. Ya rame yayi duhu, ya manta da wata baiwa da Allah yai mishi na ba shi shugabancin al'ummar jihar su ko ransar dasu ba a yiba.
       A ranar da akayi sadakar bakwai ya hattama komai na marigayan ya adana ababan bankin Iloyds TSB na kasar ingila. Sannan suka taho Kaduna, inda aka ransar da shi a washegari.
     Suka tattara shi da mai dakinsa da 'ya'yansu Al~mustapha da shahidah, suka koma government House Kaduna state. Mulki ya soma kankama.

*****************************
Share
Comment
Vote

Sai da comments dinku xan samu kwarin al'kalamin yin rubutu.

      #Fauxeekhan

BABBAN GORO Where stories live. Discover now