PART 9

41 1 0
                                    

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_

        *🅿️9*

"Washegari yaso ya Fita zuwa office ammh Abida taki barinshi ya Fita daya matsamata zai Fita sai ta Kira Abba ta gayamai wai bashi da lafiya kuma yaki zama agida nan da nan Abba ya Kirashi yace ya zauna agida ya samu Hutu bashi da yadda zaiyi Hakanan ya kwanta agida Abida na Kula Dashi,wanka ma ita ta taimakamai yana ta bari ya samu Sauki ammh taki bari Tsausayi take Bashi ganin bata da Ishashiyar Lafiyan Jikinta Tunda ta samu  Cikin nan,ammh game da Abunda ya Shafeshi Abida bata wasa dashi ko Abinci a baki ta bashi tana lallabashi kallonta kawai yakeyi yana jin Wani Iri acikin Jikinsa na wani Abun daya kasa gane komene,ko ma mene Toh yana da Nasaba da Fargaba.

Washegari ma bai Fita ba sai yammah ya fita zuwa Gidan Lauyan Abba Barisster Sa"ed sukayi Mgana Daganan kuma ya Biya gidan Kawu maude ya gaishesu sunyi kwana biyu basu Hadu ba, yadan Jima Suna Hira da kawu mauden wanda yake gani a matsayin Mahaifiyarsa,domin Shi kadai ne ya sani daga Dangin Mahaifiyarsa Sai bayan mangariba yama Kawu maude da Anty Naja"atu sallama ya Fito bai koma gida ba sai da ya biya ya Siyoma Abida kaza da yoghourt ita da kaka,kafin ya Shiga Gida sai da ya tsaya yayi Sallar Isha"i kana ya Shiga Gida,Gari na wayewa kuwa yayi Shirin Zuwa Office Abida bata Hanashi ba ganin yaji Dadin Jikinsa Karfe 8am na Safe ya Fice bayan ya karya yana zuwa Office dinsa ko zama baiyi ba wayar Abba ta Shigomai yana Gayamai wai Samiha tace ya kamata suzo su Dubashi ido ya zaro gabansa na Faduwa cikin Rawan murya yake Fadama Abba Shi ya samu Lafiya ya Fito zuwa wajen aiki jin Haka yasa yace Shikenan Allah kara lafiya suka Rabu ahaka Ajiyar Zuciya Ahmed ya Sauke Acikin Ranshi yana Tunanin Tabbas Samiha na kulla wani Abu wanda baisani ba,yana Fatan Allah ya Tseratar dashi Daga kaidinta.

******

Yau din takama Monday ne Tushen aiki ko bature na Tsoranki,yau Ahned ya Makara bai Tashi da Wuri ba Shiyasa sai Wajen 8:30am na safe Abida ta Rakoshi Zuwa Dakin kaka wacce ke Zaune Bisa Cafet din Dake Dakin nata ta kurama Talabijin ido kamar tana jin me ake Fada Sallama sukayi batama jisu ba Dariya Ta kama Ahmed ya kalli Kaka yana Fadin"Kaka kina jin Abunda ake cewa ne kika wani kafe ma Tibi ido..'?

Sai alokacin Taji Shigowarsu Dagowa tayi lokaci Daya tana makamai Harara tana Fadin",Bansani ba..Allah Ahmadu in baka Fita Daga idona ba zakaji ba Dadi..Ina Ruwanka da ina Jin Abunda ake cewa ko bana ji..?Tafada tana wani Murgadamai baki,Mirmishi ya saki yana Fadin"Ah taya zan ko Fita daga Idonki kaka..,?ai ina ciki bazan Bita ba Ahmadu da kaka ai mutu ka Raba.."

Washe baki Kaka tayi tana Fadin"Wlh kuwa Ahmadu..Haba ai ni na sani Duk Duniya waya kaini Sonka Ahmadu..Kawai wani Lokacin baka da Mutumci ne.."Abida da Ahmed suka saka Dariya Ahmed na Fadin"Ni Kaka Nine Banda Mutumci kai Tsaye gaban Iyalina harda ya"ta ko Dana gashi. "yafada yana Shafa Cikin Abida Baki Kaka ta saki kafin ta fara Tafa hannu tana Fadin"Na Shiga goma ba Tara ba Ni Bara"atu Jikar Audi Basakkwace.Ahmadu Rashin kunyanka kara gaba kawai yake Mu lokacin mu ko haihuwa aka maka Boye kanka kake saboda kunyar Fari ammh kai kuwa baka data ido Ahmadu agabana Har kana Shafa cikin Saboda Tsabar tacewa irin naka na yaran zamani.."Baki ya Tabe yana Fadin"Allah ya kyauta Kaka boyewa kamar wani Cikin Shege..? Mutum baiji kunyar Shiga Daki da mace ba,sai kunyar Abunda suka aikata ya Fito.."yafada kai Tsaye Kaka baki Ta Rufe da Hannu ta juya baya Tana Salati Abida ma baki ta Rike tana Zakudan Jikin Ahmed Shiko ko Ajikinsa yar Dariya yayi kafin yace"Kaka ni zan Fita..Kina Bukatar wani abu ne..? Ko mgana Kaka batayi mai ba Banza tayi dashi Ta juya baya bai damu ba Illah Kafada daya zakuda yana Fadin"Sweetheart ki tsaya anan basai kin Rakani ba...Tanque.."

Ya juya yana Karban Jakar Briefcase dinsa Kaka ta waigo tana Fadin"Kai Ahmadu tsaya nan kaji ni dakyau.."Waigowa yayi yana Fadin"Na"am Kaka.."ido ta Kuramai Tana Fadin"Ahmadu ashe duk zaman da mukeyi Dakai Kar kake kallona Bansani ba..?"Tafada cikin Mamaki kamar zaiyi Dariya sai kuma ya matse yana Fadin"Sosai ma Kaka..Kinsan yanzu Lokaci ya chanza zamani yazomana da Komai Shiyasa.."Kada kai kawai Kaka keyi tana rike da Haba,bai Bata zarafin mgana ba ya juya Zai Fita cikin Alhini Kaka ke Fadin"Abida Ahmadu ya gama Lalacewa...uhmh...Ahmadu ya lalace yazama Dan iska.."Abida ta saki Dariya Shima yana Jinta Dariyan yayi Cikin Ranshi yana Fadin Kaka kenan.

SILAR HALLACI...!Where stories live. Discover now