Dasunan allah me rahma mejin kai,tsira da aminci sutabbata da fiyayyen halita annabi muhammad(swa) da ahlinsa da sahabban sa.
Wanan labarin nawa me suna RUDANI banyi shi dan wani ko wata ba, kirkiraren labari ne duk da wani abun yafaru dagaske dan haka saiku biyo ni danjin yadda labarin zai kasance domin yazo da ban tsoro da al'ajabi.
Taku harkullun
*********Ummu elham**********tafe take tana tsala gudu acikin kasurgumin bakin daji cike da tashin hankali, guduta ke iya karfinta amma ina kamar bata motsawa haka take gani gawasu muggan namomin daji biye da ita dawasu kalan mutane da jajayen kaya suna binta suna mata dariya dawasu irin zako zakon hakora da farce fukarsu dawani kalar farin abu gashi bakinsu sai zubar da jini yakeyi idansuko wani kalar kore sai futar da harshe suke aiko sai kokarin kamata suke tana tsala ihu tana kufcewa cansuka cafketa suka gurfanar da ita agaban wani yamusheshen tsoho dake zaune akan wata karagar mulki gefensa zagaye dawasu murtuka murtukan mutane maza da mata sanye da irin kayan matan nan dasuka kawosu da wani katan koko agabansu gefe kuma hutace keci ga wata yarinya da aka daureta agaban hutar sai kuka take , ako bangama mamaki ba sai gani nayi ankamo yarinyar nan ankwantar da ita akan wani dutse tana kalon sama antara koko akasan kanta wani gabjejen kato yazo yatsaya yana jiran umarni yacika aikinsa sai muzurai yakeyi.
Tsohon nan yataso dakyar yake dogara sandar shi yatsaya akanta yana wasu irin surkulle sai gani nayi wani irin jan kyalle yafada kan yarinya aiko fadowarshi keda wiya saiko katan mutumin nan yasa katuwar adda yasare kan yarinyar kankace me jini yacika kokon nan shikuma kan yabace bat sbd badu kan nashine domin yafison kwakwalwa da jini aiko saijin shewa da kururuwar kakeji yana tashi. Tsohon yadau jininyazuba akan wani dutse sannan yasha yaba ma mataimakiyarshi itama tasha haka suka tayi harsai da kowa yasha sannan akazo kan sarah itace takarshe aka bata tace bazata shaba aiko cikin fushi tsohon nan yanuna ta da sandarsa.
Take wata kacha tafuto tadaureta ajikin wata bishiya aiko me sauran zasuyi inbada shewa, yadaga hannu sai ji kayi wajen yayi tsit yace maganin me taurin kai kenan kuma inkika kara gwada tausayi acikin harkar nan tamu sai mun halakaki, ki gaggauta tuba wajen badu inbahaka ba zaki fukanci fushin kungiya kinci sa'ar munaji dake shiyasa bamu halakaki ba sbd kina bada gudum muwa sosai a kungiya inbahaka ba damun ba badu jininki.
Yajuya yakoma kan kujerar sa aka cigaba da kudanar da harkokin kungiya gefe kuma anata gasa naman yarinyar nan kayan cikin kuma akayi feffesun shi. Aka zuba ma kowa nashi sanan kungiya tawatse gabanin asuba da sharadin duk wanda yakara karya doka to fah ba sassauci kuma ba dagin kafa dan kawai kisane ita kuma sarah anja kunnan ta da sharadin kawo musu mutane goma sannan za akyaleta. Tace taji ta amince,
Kowa yakama gabanshi itako tana bacewa sai ganin ta nayi kwance akan gadon yan makaranta wato makarantar kwana.🤔🤔🤔
Kubiyo ni danjin yadda zata kasance.
Yawan comment nd vote yawan typn
Vote, comment, fallow nd share.
YOU ARE READING
FUSKA BIYU
VampireLabari ne na wata yarinya me ban tsoro da al ajabi. Gashi takasan ce malama da kowa ke koyi da ita a makarantar su, sai dai kashh ashe fuska biyu neda ita domin takasan ce matsafiya me shan jinin dalibe, Kubiyo ni dan jin yadda zata kasan ce