PART1/2

18 0 0
                                    

••••• _*JAMEEL*_•••••

         _{Nafseen}_

_PAID BOOK_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

________________________________________________

_We Are Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers._

________________________________________________
_A cikin kashi Dari na wannan labarin, 70% kirkirarre ne Wanda 30% ko ya kasance na gaskiya._

_*LABARI DA RUBUTAWA.*_✍️

_*Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)*_

*_FREE PAGE -1/2_*

_*Fejin Farko na ki ke Antyna Real-Shaxee,Fatan Allah ya saukeki lafiya 🙏😍*_
__________________________________________________________

_*BISMILLAHIR-RAMANIR-RAHIM*_

_Kamar yadda nafara lafiya Allah ka ba ni ikon gamawa Lafiya🙏ALLAH YA SA RUBUTUNA YA AMFANAR DA AL'UMMA SANNAN YA NISHADANTAR DA SU😍_


********
kwance yake ya na bacci da kaga yanayin  fuskarsa tare da kwanciyar da ya yi, za ka tabbatar da cewa ya na cikin nishadi tare da kwanciyar hankali, mafarki ya ke Wanda ke bayyanar da murmushin sa a zahiri, wata yarinyar ya hango ta na fadin, "Umm umm Yaya Jameel ka tashi Dan Allah nafadama ka tashi wai so ka ke nayi letti a zaneni ne? Ka tashi ka ji," cikin magagi ya ke fadin, "Ayya Janaf di ta barci  nakeji fa kije Driver ya kai ki."

Kuka ta fara tare Da dukansa tana, "Ni dai Wallahi driver ba zai kai ni ba."

Jin sautin kunkanta ya ke har cikin ransa hakan ya sa shi farkawa arazane ya na waige-waige.

"Subhannallah jawahir ina ki ke? Ki dawo Dan Allah zan kai ki Skul din kinji ko?" A bin da ke fitowa daga bakin JAMEEL kenan ya yin da ya ke zubda kwalla.

Dafa kai kawai ya yi da hannuwansa Dan wani irin radadin zafi da kan ya fara ma sa kamar kullum a yayin da ya fi kewar JAWAHIR.

Jan yo Box din maganinsa da ke kan bedside ya yi, ya sha sannan ya tashi ya yi wanka, A cikin kakinsa na Sojoji ya fito, Wanda da ka gan sa zakasan cewa wannan cikakken jami'in tsaro ne, ba karamin kyau shigar ta ma sa ba, dauko turarensa ya yi zai faisa sai kawai ya fara jin muryar JAWAHIR A kunnensa , "Yayana a duk lokacin da za ka yi wanka ka yi kwalliya to indai ba ka sa turare ba ina mai tabbatar da ce ma ka wankan ka bai kammala ba kuma ko da mun hadu kai ba Yayana ba ne indai ba ka kamshi, domin Kamshi ba ya taba barin jikin Yayana." Wani irin Murmushi ne ya bayyana afuskarsa Wanda zan iya cewa da bai kai zuci ba, fesa turaren kawai ya yi sannan ya dauki wayarsa ya na kallon Yarinyar da ke jikin screen din wayar,black beauty Sanye da doguwar Riga murmushi  ta ke Wanda ya kara baiyanar da kyan fuskarta tare dimple din ta mai dauke hankali mai kallo.

Zuba ma ta ido ya yi kawai ya na kallonta sai da ya kusa diban 30 minit kan ya kalli agogon wayarsa 8:30, Tsakin takaici ya yi kawai sannan fice daga dakin.

Da takun kasaita ya ke saukowa daga stairs din duk da ganin ya makara Amman ko ajikin sa, ya na saukowa Fatima ta karaso garesa da Murmushi ta na fadin, "Yaya ga abincin ka nan a kan daining ina ta jira ka fito Amman shiru."

Ko dagawo ya kallota bai yi ba, kawar da kan sa ya yi tare da fadin, "Nagode Amman dai kam na koshi ba na bukatan wa ni abinci a yanzu."

Bai bare ta ko kara magana ba ya cigaba da tafiyarsa.

Ita kuwa bin sa kawai ta ke da kallo, tana jin zafin abin da ya ke ma ta Amman tafijin tausayinsa fiye da komai domin duk Wanda yasan JAMEEL ya san cewa cikakken mutum ne Wanda ko wace mace ke burin samun sa, kyan hali ga kyan diri, ilimin addini da na boko.

JAMEEL (Nafseen)Where stories live. Discover now