https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
••••• _*JAMEEL*_•••••
_{Nafseen}_
_PAID BOOK_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
________________________________________________
_We Are Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers._
________________________________________________
_A cikin kashi Dari na wannan labarin, 70% kirkirarre ne Wanda 30% ko ya kasance na gaskiya.__*LABARI DA RUBUTAWA.*_✍️
_*Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)*_
*_FREE PAGE -3/4_*
_*Yayata😰 ke daya ce Yar uwa ta jini agareni, ina rokon Allah ya ba ki lafiya🙏 Allah yakareki daga sharin duk mai bin ki da sharri😰dan Allah yan uwa Ku sa min yayata a addu'ah, Allah ya ba ta lafiya, ya kareta da ma sauran musulmai da ba su da lafiya🙏🙏Dan Allah Ku sa mu addu'arku*_
__________________________________________________________"Ayya Yaya ga abincin ka nan fa ka zo kaci."
A fusace ya juya ya na, "Ni na ce mi ki ina jin yunwa ne? Ke kam wai mayyace ko ya ya? Dan Allah ki barni na fada miki ki barni."
Tsakinnan dai na fama ya yi, ya na huci ya shige daki, har ga Allah a zuciyarsa ba ya jin dadin yadda ya ke ma ta Amman bazai iya controlling tempern sa ba, Dan haka kawai wa ni lokacin ya zabi ma ta shiru ya kyaleta Amman har yanzu ta ka sa fahimtarsa.Hannunta kawai tasa ta dafa kan ta tana fadin, "Wayyo Allah na." Sannan ta shige dakinta, ta kullo kofar kawai.
Washe gari,,
Kamar kullum da sassafe JAMEEL ya ta shi da wannan azababban ciwon kan da ya ki rabuwa da shi, bayan ya idar da sallah ya sha magani, duk da kasancewar zafi da irin radadin da kan ke yi ma sa bai fasa karatun Al'qur'ani ba, shi daya ya ke yi Amman sai ya ke ganin kamar su biyune domin zakakkiyar muryan Little Jawansa ya ke ji.
Ya na kammala karatu ya yi addu'a tare da rufe Qur'anin wanda ya dinga shafa bayan ya na murmushi.
A zuciyarsa ya ke fadin, "Allah Sarki Jawana kamar yadda ki ke fadi min a kullum a duk San da na shiga cikin wani yanayi ba abin da zai min magani illa karatun littafi mai girma, da kan ki, ki ka fanso min wannan domin faranta min, ina matukar alfahari tare da son ki.
Sai da ya dibi wajen 30minit ya na tunani kan ya tashi ya yi wanka ya Sanya Kakinsa.
Karfe bakwai dai-dai ya fito cikin shigar sa yadda ya saba ban da tashin kamshi ba abin da ke fita, indai JAMEEL ya je waje, ko da ya bar wajen indai Wanda ya San sa ya zo to sai ya tabbatar da kamshin turarensa.
Kamshin Turarensa kawai Fatima da ke kitchen ta jiyo ai ko da sauri ta fito tare da karasowa garesa.
"Morning Yaya."
Cewar Fatima.Wa ni irin bakin ciki ya ji aransa ya na fadin, "Wai wannan wace irin mayyace?"
A zahiri kuwa ya kawar da kansa tare da fadin, "Morning."
Ya cigaba da tafiyarsa ta kasaita kamar ya na tsoron ta ka kasa.
Motarsa ya nufa da sauri mai gadi ya bude ma sa get domin yasan halin mai gidan na sa ba wasa.
driving ya ke Amman kamar dole ban da kira'a ba sautin da ke tashi acikin mota, bin karatun ya ke kawai, azuciyarsa ya na jin dadi Amman da ka gansa azahiri dai kam kamar kullum fuskar nan ba fara'a.
YOU ARE READING
JAMEEL (Nafseen)
ActionLabarin Soyayya mai cike da ban tausayi,sadaukarwa tare da nishadi.