page23

17 0 0
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

💔💔💔💔💔💔

*MA HAUKACIN KISHI*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

    *MALLAKIN*👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU,AD)*

      *FREE BOOK*

   *(TRUE LIFE STORY*)

Wattpad , zaynerb Muhammad kabeer
Facebook ,zaynerb Muhammad kabeer
Email address zainab m kabeer 1122@gmail.com *____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
        *PAGE 23*
Alhaji sule ne yaje ya sami  mahaifiyar Sadik yashaida  mata cewa ,Sadik ya zo yafada mishi komai , cikeda mamaki Hajiya tace , oo toh karana ya kawo maka,
  Takara da cewa wallahi  Alhaji ba auran bane banaso , hada zuri, a da hajiya Amina shine banaso , kuma na fuskanci yaronan  na matukar san yarinyar.  amma wlhy bazan taba goyon baya Sadik ya aureta ba .
    Alhaji sule yayi shuru yana sauraron matar tashi yakalleta yace kingama ? Cikeda jin haushi da bacin rai tace ehh nagama magana bazai aureta in har na isa dashi , Alhaji sule  yayi saurin  cewa yauwa kikace kin isa dashi , cikeda gadara tace kwarai kuwa , yace " yauwa in har kin isa da shi toh nima na isa dake sabida haka a matsayina na mijinki ina me baki umarnin barin sadik ya auri wacce yaga tamai , cikin tashin hankali Hajiya tafara magana "" haba Alhaji yazaka goyi bayan wannan yaro  akan yaje ya auro mana 'yar dangin tsiya gaskiya banji dadi ba wallahi    , kafasan waye Hajiya Amina!!
  Alhaji yayi murmushi irin nasu na manya, yace hummm , Hajiya nikaina banason  aure tsakanin su , amma  toh ya za ayi , haka dai zamu hakura muyita tayashi da adu ,a  kinsan cewa ni mutum ne da bayason takurama yaro tunda dai har yanuna yana Santa mubar shi ya aureta , in kuma muka jaa  a maganar auran, kuma akazo akwai rabo tsakani , sai rabo ya kashe mu sabida haka muyita addu ,a kawai ,
 
Dakyar dakyar Alhaji ya shawo kan matar tashi ta yarda da batun auren , bayan bayan nasiha  da yaiyi mata.
Jiki A sanyaye tace " Dama fa ni ba komai ne yasa nece ba zai aureta ba ! Kawai dai ina tsoron irin halinsu ne , duk sauran 'yan uwansu  mata bakaga yanad suke juya mazajensu Dama ni abun da na guda kenan , amma tunda hakane Allah ya tabbatar mana da alkhairi ,cikeda jin dadi Alhaji ya amsa da Ameen!!
   Bayan Alhaji ya fitane , Hajiya tace salma kiramun Sadik , A waya,kice yazo yanzu yanzu  salma ta amsa da toh , tana kiranshi tace yaya , wai kazo Hajiya na nemanka  yanzunan Sadik ya katse wayar bayan ya amsa da toh,

  Sadik ne zaune a gaban mahaifiyarshi , Hajiya tace" Sadik wato 'karata ka kai gun Alhaji ko , Sadik ya sunkuyar da kai yace Aaa Hajiya  ba karanki na kai ba ,

   Hajiya tace "Sadik ba wai Rukkaiya yace banaso ta zama sirikata ba kawai ina gudunkar muyi abun da zamuzo muna danasani , amma dai tunda kaji kagani zakuma aka iya da duk irin halinta , nayarjemaka , Allah tabbatar da alkhairi, cikeda jin dadi Sadik ya amsa da Ameen!! Yakara da cewa inshallahu Hajiya bazamuyi da nasani ba ,
  Hajiya ta kada takai ta Tashi kaje  Allah ya bada sa ,a ya amsa da Ameen , yafita cikeda farin ciki.
  Bayan ya fita bai zarce ko inaba sai gidansu Rukkaiya, yanazuwa Rukkaiyya tafito , yake sanar da ita duk abun da yafaru tsakaninshi da mahaifiyashi , Akan cewa dakyar ya shawo kanta ta amince , yakara da cewa dan Allah my Ruki ki bata mamaki  kizama mai biyaiyya , kar hasashenta yazama gaskiya kinji!!!
  Rukkiyya tace hummm in Allah ya yarda . baza ta sameni da wani mugun hali ba inshallahu , zata sameni mai biyaiyya .
cikin Ranta kuwa in yaiyi dubu ya baci, dan harta gama shirya abun da zata mata dan kuwa, bakaramin bata mata rai tayi ba, dan kuwa yanda takeji bata ki yanzu ma A dauramata aure da Sadik ba , Sadik ya ce ,

Uhhmmm yanzu za ayi magana sai in turo magabata dan wallahi na matsu in ganki a dakina , cikeda zumudi , Rukkaiya tace uhmm ai nikam ma nafika san in mallakeka A matasayin miji , sadik yayi murmishi yace koh , ta ehh  , cikeda jin dadi da farin ciki suka dan taba hirar su ta masoya  ,gwanin ban sha,awa, daga bisani sukayi sallama , Rukkaiya ta shiga gida .

    Bayan Rukkaiyya ta shiga gida  cikin hanzari ta kwalla ma mamanta kira tace ,mama!! mama!!  Kizo akwai matsala , da sauri Hajiya Amina ta fito tace kee lafiya ,
Cikeda tashin Hankali Rukkaiyya ta ce ""mama wallahi  sai yanzu na tabbatar da nayi  shirme da ban yarda munje gun bokanan  ba , mama kiji wai Ashe dakyar munafukar uwarshi  tabari ya aureni ,

  Hajiya Amina tace ""hummm ai nasan za a rini , amma kika ki yarda , yanzu ai gashinann kinkusa ki ja mana , Rukkaiya tace "' hummm mama ai yanzu dai yace zai turo ,a cikin satinan , Hajiya Amina tayi farin ciki da haka tace " duk da haka zanje gun boka yayi mana aiki tun kafin ma kishiga gidan , dan tunda irin haka tafaraa faruwa toh tun wuri gara ma a yi ma tokar  hanci , Rukkaiyya tace ai kuwa ,mama mutafi gobe gobe, Hajiya Amina tace"" Allah yakaimu ta amsa da Ameen !!
 
  Washe gari  da wurwuri Hajiya Amina da Rukkaiya suka nufi gun boka , bayan sun jene , suke ,fada mishi abun dake tafe da Su , da kuma abun da sukeso ya masu , dan su mallaki Sadik
 
Bayan boka  yayi 'yan duba dubanshi , ya buga kasa , ya dago ya kallesu yace "" me kukace sunanshi"" ??dasauri Hajiya Amina tace uhmm Abubakar sadik sule mai turare , boka ya kara yan duba dubanshi ya dago kai yace kaiiiii , gaskiya wannan aikin da kamar wuya , ba aiki bane da za ayi shi cikin sauki ba ,

   Cikin fargaba da tashin hankali Hajiya Amina da  Rukkaiya " sukace boka kamar yaya ,da kamar wuya , Boka yadago jajayan idonshi yakallo su yace, gaskiya ba lallai aiki yayi tasiri  akan shiba  dan mahaifinsu ya kafesu  da Addu oin , sossai da wuya aikinmu ya kamashi , amma da akwai hanya daya ,
Dasuri sukace" menene hanyar boka ?
  Boka yace ""aiki bazai yuyuba har sai ta aureshi mugani , ko zamu iya !!
Sannan mufada mata duk abun da ya kamata tayi da ka idojinmu , in anyi auran
   Hajiya Amina tace " toh badamuwa,  zamusa auran  nan kusa , boka yace dayafi dan kuwa in ba auran shi tayi ba aiki ba zaiyuyuba ,
Hajiya tace"" toh boka zamu iya tafiya ? Yace eh kutashi kuje  ,
 
Suka tashi sumisumi  da jin haushin rashin samun nasara da basuyi ba akan Sadik .

    Da haka suka koma gida sunata kulle kullen yanda zasu bullowa Al amarin , Hajiya Amina ce ke fadama  Rukkaiya tadinga mishi dabara ta na nunar mishi anfani suyi aure da wuri , Rukkaiyya ta amsa  da toh ! Ai hakan zanyi zan ta Jan ra ayinshi da muyi aure cikin gaggawa,

  Hajiya Amina tace ai kuwa dayafi , dan ba a bori da sanyin jiki .

   Soyaiyya mai karfi tashi ga tsakani Rukkaiya da Sadik , dan har takai Rukkaiyya har gida take biyo Sadik , Har daki , suna hira ,

   Wsa wasa, har shaidan yaso yayi tasiri akansu , dan tun Sadik na kokarin ganin ya saita kanshi amma inaa , saidan yayi nasarar hura mishi wutar   sha ,war  Rukkaiya , Domin kuwa duk Inda mace da na miji suka kebe to fa na ukun su shaidanne ,

Duk da cewar bai Santa a matsayin mace ba , sai dai sunfarantama , junansu ta hanyar wasa , tsakan.

*MUJE ZUWA*😎

   *Jan hankalina gareku masu karantun littafin MAHAUKACIN KISHI* *kuyi kokari gani gun gina so a kan turbar da ta dace kar shaidan yayi nasarar dasa ma zuciyoyinku sh ,awar junanku kafin aure ,domin Kuwa bayan aure ana samun  matsala ,babba ,yana haifar da zargi da rashin yarda  , dan Allah mu kiyaye*

*BANGA COMMENTS SOSSAI AB SABIDA HAKA BAZANYI TYPING DA YAWA BA ,*

  *SANNAN  BAZAN KARA POSTONG A GROUP DIN DA NAGA BA SA COMMENTS BA  DAN KUWA BANGA AMFANIN TUROWA BA TUNDA BAKWA COMMENTS*

*MORE COMMETS*😎😎😎
*MORE TYPING*.....✍️✍️✍️

*PLSS SHARE*👏👏

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 30, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAHAUKACIN KISHIWhere stories live. Discover now