KULSUM

787 27 15
                                    

Tana wannan tunanin mai matukar soya zuciya mutumin da suka tarar ya fito daga ofishin likita, Taufeeq ya wuce gaba ta bi shi a baya. A jikin kofar ofishin an rubuta (Consultant Ophthalmology), ta bi bayan Taufeeq cikin mutuwar jiki da ta zuciya suka shiga.
Sanyin Iya kwandishan ne ya fara bugun jikkunan su. Kulsum ta kai dubanta ga mamallakin ofishin wanda ke zaune cikin kujerar sa mai juyawa dama zuwa hagu, ya baiwa kofar shigowa baya, idon sa na kan file din ta. Sanye cikin grey-black Italian suit. Gabadaya ya juyo da kujerar sa ya fuskance su, amma idon sa na kan file din gaban sa. Ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane TURAKI ba, Turakin ta .... Her Ex-Turaki, kowanne irin canjin rayuwa ya samu kuwa, sai dai ya tara suma a kansa wadda a baya ba shi da ita, ta kwanta luf a kansa sai sheki ta ke ta fulanin Gaya.
A jikin dan karfen da ke kan teburin sa cikakken sunan sa ne cikin ruwan gold, DR. ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI GAYA..... ta wani irin zuki numfashi ta fesar. A hankali ta soma maida kafafunta baya don barin ofishin. Cikin tsananin taka-tsan-tsan na kada takunta ya bada sauti. Abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun ta.... Alaqar da ke tsakaninsu, wata irin alaqa ce ba mai kankaruwa daga zuciya ba!!!
Saura taku biyu ya rage mata ta fice ya dago kansa gaba-gadi don ganin masu shigowa… Bayyanannen canjin da ta samu cikin shekaru takwas da doriyar watanni bai hana shi gane ta farat daya ba, kamar yadda itama nashi canjin da nauyin shekarun da suka hau kansa, suka bashi suffar cikakken mutum wanda ke cikin ganiyar cin ilmin sa,  ya kuma san ciwon kansa a halin yanzu, bai hanata gane shi ba.
Ya kafe ta da idanunsa ta cikin farin gilashin da ke manne a idon sa,... idanun nan na Turaki da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu... A lokacin da ita kuma ta bude kofa ta fice da dan banzan sauri… har tana tuntube, saura kadan ta fadi!

Littafin KULSUM na tafe a watan January Insha Allah!

AUREN KWANGILA Onde histórias criam vida. Descubra agora