DANDANO DAGA 💜 *Aalimah* 💖

3K 60 37
                                    

DANDANO DAGA

                                   💜   *Aalimah* 💖

(C) *Sumayyah Abdulkadir Takori**

A yau suna zaune a karamin dining din su mai cin kananan kujeru biyu kacal, wanda ke cikin kitchen dinsu suna cin abincin rana. Wayarsa dake gefen su tayi kara, ya kalle ta da gefen ido, bai yi niyyar amsawa ba, don a kwanakin nan amsa waya wahala yake masa, tafi zama a kashe a yawancin lokuta kafin ya karasa cinye kwanakin hutun sa. Amma ganin mai kiran, da sauri ya mika hannu ya dauka.

Aalimah na ganin yadda ya tattara bakidayan hankalinsa da nutsuwarsa akan wayar, ya kuma mike tsaye. Hatta muryarsa canzawa tayi, magana yake _with utmost respect._

"Bansan ka shigo gari ba, da tuni na zo kwance jaka. A yimin izni na kawo Aalimah ta kwashi gaisuwa wajen babban Yaya. Bata taba ganin ka ba".

Bata ji amsar da Mu'azzam din ya bayar ba, ta dai ga Aboulkhair ya kara nutsuwa, yana rokon sa cikin lallausar murya kan ya bar su su zo, har yana fadin; ya fadi iyakar mintunan da zai iya basu da bakin sa, in suka haura gobe kada ya bar su su sake zuwa. Takaici ya kashe Aalimah daga zaune. Sarkin ina ne wannan? Dole ne zuwa wajen nasa? Me yake rabawa da sai an roke shi za'a je inda yake?

Bata gama wannan tunanin ba ta ga Aboulkhair ya cillar da wayar tasa gefe, ya rarumeta daga kujerarta  ya mikar tsaye cike da zumudi, yace.

"kiyi girki wanda yafi kowanne dadi mu kaiwa Mu'azzam.  Ki hanzarta please, mintuna talatin kawai ya bamu in mun je, yanada seminar gobe da (concophillips) yana shirin tafiya kada ki bata lokaci".

Aalimah ta rausayar da kai ta ce "me zan dafa? Bansan me yake so ba?"

Ya koma ya zauna ya hau lissafi.

                 "Girkin da yafi kowanne dadi _with aroma and maggi_ ".

Bata san sanda ta saki dariya ba, ta tabbata Aboulkhair yana matukar son Yayansa, bata taba ganin ya dauki lamarin wani, ko wani abu da muhimmanci irin haka ba.

"Kowanne girki ai dole asa masa aroma da maggi, _I mean_ irin abincin da yake so".

"Tashin hankali" Inji Aboulkhair.
"Ai wato *_menu_* ake bashi daga WALDORF ASTORIA  ( mafi shaharar restaurant a Las Vegas) ya zabi abinda ya ke so, ni kaina ban sani ba. Amma ke me kika ga ya dace?"

Aalimah kamar tayi kuka. A ranta tace "haka kawai ina zaman -zama na zaka taro min aradu da ka. Wannan ba-saraken naka ai sai kai".

A fili kuma ta ce,
"Burabusko da miyar taushe"..
Ya zaro ido sannan ya kankance su yana duban ta, ya ce "you are not serious. Gero zaki bashi ya shaqe shi? Tukunna ma kin fahimci wai wajen wa nake magana ne?"
"Ka ce Mu’azzam!"
Ya ce "baki san Yayan mu ba ne?"

Ganin kamar ya soma harzuka ta shiga nutsuwar ta sosai. Ita haka kawai ranta bai son Mu'azzam dinnan, tun daga lokacin da ta fahimci irin *life-style* dinsa. Da maganganun da kannensa su Basma da Khaleesat ke yi a kansa. Sannan shekaru dai-dai har biyar ta kwashe a gidan Ishaq Raazee, amma daidai da rana daya bata taba ganin sawun Mu'azzam din a gidan ba da sunan ya zo gaida iyayensa, saidai kullum taji Mummy a hanyar zuwa gidansa *what a life!* Sannan yanzu ta kara fahimtar wani abu; Aboulkhair baya hada lamarin Mu'azzam dana kowa! Ita kanta ba'a bakin komai take ba in dai akan Mu'azzam ne! _She has to be careful_ don tsira da mutuncin ta da soyayyar ta a idon  mijinta mai kaunarta.

Da kyakkyawan sauti tace.
"Ina ganin mu yi masa tuwo. Ka fahimce ni *Mon Amour,* ba abinda ya saba ci ya kamata mu kai masa ba, ba zamu burgeshi ba. _African cuisine_ shi ya kamata. Idan Mu'azzam ya kasa cin tuwo na; ka mare ni sau uku".

Bai san sanda yayi murmushi ba. Amma kwarai ta bata masa rai da farko. Zancen Mu'azzam fa ya ke mata amma ta wani maida shi kamar wani marainin wayon ta. Kodayake ya mata uzri; bata san shi ba, bata taba ganin shi ba, batasan wanene shi ba, wata alaqa bata taba hada su ba, bata san komi akan shi ba.

AUREN KWANGILA Donde viven las historias. Descúbrelo ahora