MAI HAKURI (shi ke da riba)
D'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba ta k'ara shiga tsananin tashin hankali, idonta kamar zasu yo k'asa ta d...