KhadeejaCandy

KhadeejaCandy

ummusalmabdulkaadir

@KhadeejaCandy aslm anty Khadija ya gida ya abubuwa,Dan Allah anty Khadija Ina son na fara rubuta novels toh Amma bani da followers wlh shine nace ko akwai wani group haka na writers haka wanda Zaki Saka ni Nima na karu,saboda in babu followers bazan samu karfi gwiwar rubutu ba wlhi,Allah ya Kara basira ya Kuma bamu sa'a gabadaya
Reply

mammyAfreen

@KhadeejaCandy Masha Allah, Allah ya Sa kin fara a sa'a Allah Kuma ya caki iKon gamawa lafiya, don Allah na kudi ne ko free ne?
Reply

Seemahwrites

@KhadeejaCandy jaxakillah khairan ❤️
            Allah yasa kin fara a Sa'a 
Reply

KhadeejaCandy

https://www.arewabooks.com/chapter?id=65564bada707abe6f0c80cc3
          
          
          HURRIYA 
          
          BY KHADEEJA CANDY
          
           Available on Arewabooks. 
            PLEASE SHARE... 
          
          
          Gammm ta ji an rufe mota sai dai ba zata iya fadar motar da aka rufe ba, ta Salim ce dake neman saƙo kamar yadda ya fada mata ko kuma ta wanda za a bawa saƙon ne? Ganin Hasken dake hasketa ya dauke yasa ta janye hannunta daga idonta sai ta yi arba da mutum tsaye a gabanta nesa kadan da gurin da Salim ya tsaya a dazun, kasansa ta fara kallo har ta daga kanta sama ta kalli fuskarsa, akwai hasken wutar gidan dake haska ko'ina ta bawa kowa damar ganin abun da yake wakana a harabar, sai dai hasken be kai ya tantance mata fuskar waye tsaye a gabanta ba, saboda lafiyar idonta, amman tabbas zata iya shaidar wani abu da ba zata kira da shi tsoro ba, kuma ba fargaba ba ce, wani abu ne da ya cika idonta ya aikawa zuciyarta da saƙo ta fara bugawa da ƙarfi. A rashin zato da tsammani ta samu kanta a tsaye gabansa numfashinta na ƙoƙarin sarƙewa. 
          
          “Me kike yi a nan?”
          
          Muryara ta daki dodon kunnenta, a nan ta gane duk wani abu da ta ji gabanin fitar sautin muryarsa shimfida ce.
          
          
          *Idan kina bukatar karanta wannan labarin biya #500 to 2451879008 Zenith Bank Hadiza Abubakar sai ki turo shaidar biyan ta wannan number 08036126660 za a saka ki a group*
          
          *Ko kuma ki ziyarci shafin arewabooks domin karantawa a can*

Muazzamaliyu

@KhadeejaCandy I like the Content of the Story… sim like lbr yazo da Sabon Salo, Saidai ba Free bane. ♥️
Reply